Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya saukar da littatafai, don bayi su san Allah, su san shi da Siffofinsa, su san hakkokinsa a kansu, da shari'ar da za ta inganta musu rayuwa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa, karatun Alkar'ani yana cikin manyan aiyukan
Ibada, Allah ya ce: {Lallai wadanda suke karanta littafin Allah, kuma suka
tsayar da Sallah, suka ciyar daga abin da muka arzurta su a boye da bayyane
suna fatan samun kasuwanci maras faduwa. Don Allah ya cika musu ladansu, ya
kuma kara musu daga falalarsa, lallai shi mai gafara ne kuma mai godiya}
[Fadir: 29 - 30].
Karatun Alkur'ani nau'i biyu ne:
Na farko: Karatu na hukunci, wanda ya kunshi gaskata
labaran da ke cikinsa, da aiki da hukunce – hukuncensa na umurni da hani.
Na biyu: Karanta lafazinsa, nassoshi masu yawa sun zo
suna bayanin falalarsa, imma karanta dukkan Alkur'anin ko kuma karanta wasu
Surori ko wasu Ayoyi daga cikinsa. Ya abbata daga Usman (ra), Annabi (saw) ya
ce: ((Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur'ani kuma ya koyar da shi)).
Bukhari (5027).
Kuma ya tabbata ya ce: ((Kwararre a karanta Alkur'ani
yana tare da Mala'iku SAFARA, KIRAMIN BARARA, amma wanda yake karanta
Alkur'anin amma yana i'inna a cikinsa, karatun yana wahalar da shi yana da lada
biyu)). Bukhari (4937), Muslim (798).
Ma'ana; lada daya na karatun, dayan kuma na wahalar da
ya sha a kan karatun.
Haka ya tabbata daga Abu Musa al-Ash'ariy, Annabi
(saw) ya ce: ((Misalin Muminin da yake karanta Alkur'ani kamar tanjirin ne,
kamshinsa dadi, dandanonsa ma dadi. Misalin Muminin da ba ya karanta Alkur'ani
kamar dabino ne, ba shi da kamshi dandanonsa kuma zaki)). Bukhari (5020),
Muslim (797).
Ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Ku karanta Alkur'ani,
don zai zo ya ceci ma'abotansa a Ranar Qiyama)). Muslim (804).
Haka ya tabbata daga Uqba bn Amir, Annabi (saw) ya ce:
((Da dayanku zai tafi Masallaci ya koyi karatu, ko ya karanta Ayoyi biyu na
littafin Allah hakan ya fi a ba shi rakuma biyu, ya karanci Aya uku ya fi masa
rakuma uku, ya karanci Aya hudu ya fi masa rakuma hudu, ya fi masa rakuma masu
yawa)). Muslim (803).
Haka kuma ya tabbata daga Abu Huraira (ra) Annabi
(saw) ya ce: ((Mutane ba za su hadu a daki daga cikin dakunan Allah ba, suna
karanta littafin Allah, suna yin darasinsa a tsakaninsu face nitsuwa ta sauka a
kansu, rahma ta lullube su, Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah ya ambace su a
cikin wadanda suke wajensa)). Muslim (2699).
Kuma ya ce: ((Ku lazimci karanta Alkur'ani, na rantse
da wanda raina ke hanunsa ya fi rakuma kubucewa daga igiyarta)). Bukhari
(5033), Muslim (791).
Ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya karanta
harafi daya na littafin Allah yana da kyakkyawan aiki daya, kuma za a ninka shi
gida goma. Ba ina nufi Alif, Lam, Meem harafi ne da ya ba, a'a,
"Alif" harafi ne, "Lam" harafi ne, "Meem" harafi
ne )). Tirmiziy (2910).
'Yan'uwa wadannan su ne falalolin karanta Alkur'ani,
kuma ga bayanin ladansa a wajen Allah, lada mai yawa a kan aiki mai sauki,
wanda ya yi sakaci ya yi hasaran lada mai yawa.
Haka wasu Hadisan sun zo da bayanin falalolin wasu
Surori, kamar Suratul Fatiha, Suratul Baqarah da Ali Imran, Suratul Ikhlas, da
Kula'uzai. Haka akwai Hadisai a kan falalolin wasu Ayoyi, kamar Ayatul Kursiyyi
da sauransu.
Don haka ya ku 'Yan'uwa, ku dage da yawaita karatun
Alkur'ani a cikin wannan wata mai girma, watan da a cikinsa aka saukar da
Alkur'ani. Kuma Mala'ika Jibril (as) ya kasance duk shekara a Ramadhan yakan zo
wajen Annabi (saw), Annabi yana bitan Alkur'ani a wajensa. Amma a shekarar
rasuwarsa sau biyu ya zo masa, kamar yadda ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya
ce:
((Annabi (saw) ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma
kyautansa ya fi yawa a Ramadhan, saboda Jibril ya kasance yana haduwa da shi a
kowane dare a watan Ramadhan har ya kare, Manzon Allah (saw) yana karanta masa
Alkur'ani, idan Jibril ya hadu da shi ya kasance mafi kyauta fiye da iska mai
kadawa)).
Bukhari (4997), Muslim (2308).
Wannan ya sa Magabata sukan yawaita karanta Alkur'ani
a cikin watan Ramadhan, al-Zuhriy idan Ramadhan ya shiga yake cewa: watan
karatun Alkur'ani da ciyar da abinci. Imam Malik ya kasance idan Ramadhan ya
shiga yakan dena karantar da Hadisi da majalisan ilimi, ya fisknaci karatun
Alkur'ani.
An ruwaito Qatada ya kasance yana sauke Alkur'ani a
dare bakwai, amma a Ramadhan a dare uku yake saukewa, a goman karshe kuma yana
saukewa a kowane dare. Ibrahim al-Nakha'iy kuma yana sauke Alkur'ani a Ramadhan
a kowane dare uku, a goman karshe kuma yana saukewa a kowane dare biyu. Haka
al-Aswad yana sauke Alkur'ani a kowane dare biyu a watan gaba daya.
Don haka 'yan'uwa ku yi koyi da wadannan Magabata na
kwarai, ku ribaci wannan wata ta hanyar yawaita karanta Alkur'ani dare da rana,
hakan zai kara muku kusaci ga Ubangijinku.
Allah ya taimake mu a kan aiyukan da'a, ya sa mu dace
da falalolin wadannan aiyukan Ibada, ya ba mu dukkan albarkatu da suke cikin
wannan wata.
'Yan'uwa kar mu manta da kasarmu Nigeria, mu yawaita rokon
Allah a kan ya ba mu zaman lafiya, ya kawar mana da fitinar ta'addanci da
garkuwa da mutane, ya ba mu arziki da shugabanni na gari masu tsoron Allah,
masu tausayin talakawa.
Daga
Dr. Aliyu
Muh'd Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.