Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyar Samun Rahma Cikin Sauƙi

 Abu Huraira (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

 Duk wanda yakiyaye faɗin:

 SUBHANALLAH 33.

ALHAMDULILLAH 33.

ALLAHU AKHBAR 33.

Ya cike na ɗarin da:

LA'ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LASHARI KALAH LAHUL-MULKU WA-LAHUL-HAMDU WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN ƘADIR.

Za a gafarta masa zunubansa ko da kuwa sunkai yawan kumfar Teku.

[Sahih Muslim].

 Wato wannan hadisi yana nuna mana nuni da falalar da ke cikin kiyaye azhkar na bayan sallolin farillah harma da nafila.

 Saboda yadda ALLAH TA'ALAH yake son bayanisa da rahnarsa sai ya ajiye wata hanya ta samun kankarar zunubai baki ɗayansu ta hanyar azhkar na bayan sallah.

 Shi ya sa shaiɗan baya barin wasu su zauna su yi wannan azhkar ɗin, da zarar an sallame sallah suke tashi su tafi izuwa harkokinsu na duniya, wanima zunubi zaitafi ya aikata.

 Sannan kuma anaso a rinƙa yin ambaton a cikin nutsuwa ba tare da gaggawa ba, domin shi wanda kake ambato ɗin shi ne ya halicceka, kuma baya gaggawa ba kuma yasan gaggawa ya kuma hanemu da gaggawa.

 Saboda haka duk wanda yake neman ALLAH ya kankare masa zunubansa komai yawansu, to ya kiyaye faɗin waɗannan kalmomi a bayan kowacce sallah tasa ta farillah da nafila.

 Amma fa ALLAH baya yafe zunubin da da ke tsakanin mutum da mutum, kamar:

Wani ya cuci wani a ciniki, ko miji ya tauye hakkin matarsa ko ita ta tauye nasa, ko sata, ko fitarwa da wani jini dadai sauransu.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments