Ticker

6/recent/ticker-posts

Karanta Alƙur'ani Tare Da Kallo!

Daga Abdullahi Ɗan Mas'ud (RA) Ya ce; Manzon ALLAH () Ya ce “Duk wanda yake son ya so ALLAH da Manzonsa to ya karanta Alƙur'ani yana mai kallon mus'hafi (Shafukan Alƙur'ani).” [Silsilatus sahiha: 2342]

Wannan hadisi ya bayyana mana cewar wanda yake karanta Alƙur'ani tare da kallonsa zai kasance cikin waɗanda ALLAH da Manzonsa suke so, akwai fa'idah sosai acikin karanta Alƙur'anin tare da kallon shafukansa domin yana raya jikin ɗan'adam ta hanyar samun cikakkiyar lafiya da kuma nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah (Rahimahullah) Ya ce “Ni banga wani abu wanda yake ciyar da hankali da ruhi, yake  kiyaye jiki, yake kuma tattare da dacewa a Duniya da Lahira ba, sama da yawaita dawwamar da  kallon Littafin ALLAH.” [Majmu’ul fatawa: 7/493]

Hakanan Ibnu Mas'ud (RA) Ya ce: “ku yawaita kallon mus'hafi (shafukan Alƙur'ani). [Almusannaf Li Ibn Abi-shaibah: 2/499]

Haƙiƙa shi Alƙur'ani albarka ne, albarkarsa yana kewaye wanda yake karanta shi da wajen da ake karanta shi, kallon shi lada ne, sauraron shi lada ne, tadubburin sa lada ne. Ko wanne harafi nashi yana ɗauke da lada goma.

Imam An-nawawy (Rahimahullah) Ya ce: “Karatun Alkur'ani da kallo shi ya fi falala akan karanta shi da ka (a haddace), domin kallon mus'hafi (shafi) ɗin shima ibada ne da ake son mutum ya aikata, don haka karantawa da kallo zai zama ibada ne guda biyu a haɗe (ibadar kallo da ibadar karatun).” [Attibyaan Fi Aadabu Hamalatil Qur'an: 55]

Telegram

https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook

http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube

https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

Post a Comment

0 Comments