Ticker

6/recent/ticker-posts
Yanda za ka yi kasuwancin DATA cikin sauƙi -SAHABDATA


Idan kana karanta wannan post ɗin to tabbas ka hau yanar gizo. Duk wanda ya hau yanar gizo kuwa to tabbas ya yi amfani da abun da muka fi sani da DATA. Babu shakka datar da ake ƙonawa a shafukan yanar gizo a kowanne rana yana da matuƙar yawa. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasuwancin sayar da data ya zama ɗaya daga cikin kasuwanci na zamani da suke kawo kuɗi sosai.


Akwai hanyoyi da yawa da ake bi wajen sayan data. Wassu suna saya kai taye daga layinsu, wassu kuma suna saya daga banki, wassu kuma suna saya daga wajen 'yan kasuwa da sauransu. Cigaban da aka samu a yanzu shi ne 'yan kasuwa (resellers) sukan sayi data mai yawa a farashi mai sauƙi sannan su sayar da shi a farashi mai sauƙi ga mai saya dan amfanin kai-da-kai ko kuma sayarwa. Suna amfani da shafukan yanar gizo wajen sayar da wannan data.


SAHABDATA ɗaya ne daga cikin waɗannan shafuka. A shafi na SAHABDATA za ka iya abubuwa kamar haka


  1. Sayan Data da katin waya(recharge card).

  2. Biyan kuɗin wutar lantarki.

  3. Biyan kuɗin TV Cable.

  4. Sayan PIN na jarrabawa, da sauransu.


yanda za ka saka kuɗi a wallet na SAHABDATA


Akwai hanyoyi biyu na saka kuɗi cikin sahabdata.


1. ACCOUNT: Wannan ita ce hanya ta kai tsaye da za ka saka kuɗi cikin wallet. Sahabdata ta samar da account number na bankuna daban-daban har guda huɗu ga kowanne customer. Duk wanda ka ɗauka ka tura kudi ciki zai shiga sahabdata wallet ɗin ka.

2.MANUAL: Wannan kuma za ka tura kuɗin ne zuwa account ɗin jami'in sahabdata. Bayan ya tabbatar da cewa kuɗin da ka tura ya shiga account ɗin sa zai saka maka su a cikin sahabdata ɗin ka.
yanda za ka sayi data


Bi waɗannan matakai daki-daki domin sayan data.

1. Shiga shafin sayan data.2. Cika waɗannan bayanai daidai sai ka taɓa buy data.
3. Za a tambaye ka shin ka tabbatar kana so ka tura data a wannan number? Idan ka tabbatar sai ka taɓa yes.
4. Daga nan za a tambaye ka PIN ɗin ka. Sai ka rubuta sannan ka taɓa continue.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba data za ta je inda aka tura ta.Ga masu neman ƙarin bayani. Kalli wannan video inda muka yi bayani daki-daki.
Post a Comment

0 Comments