Ticker

6/recent/ticker-posts

Kashles - Ta Malam Khalid Imam

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.


Allah Ke 'yanta kowa,

Nairarmu da da a baya,

Mu ke liƙi mu taka,

Muna ta rawa a kanta,

Allah Ya ba ta 'yanci,

Ba mai liƙata yanzu,

Ya taka rawa a kanta.


Allah Ya 'yanta Naira,

Nairar da mu da kanmu,

Mu kewa cin mutumci,

Mai man ja duk da man jan,

Bai goge hannuwansa,

Yake shakar wuyanta,

Haka ma mai saida ƙosai.


Da kwandasta na mota,

Da mai gyara na babur

Suna murɗe wuyanta,

Ba wanda ya damu da can,

Maza mata da yara,

Ya tsare haƙƙi mutunci,

Na Naira sai ƙalilan.


Kashiles ya zo ƙasarmu,

Naira yau tai mutunci,

Daraja ƙima a hannu,

Layi jama'a da kansu,

Su ke yi babu soja,

Ko ɗan sanda a banki,

Ko kaɗan Naira a ba su.


Kashiles ma na da rana,

Duk da ya matse mutane,

Yasa jama'a fahimtar,

Darajar Naira a hannu,

Masu liƙawa su taka,

Yau babu bare su liƙa,

Su taka rawa da homa.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

13/3/2023

Post a Comment

0 Comments