Da Yammacin Jiya ne a Unguwar Kofar Nassarawa dake Cikin birnin Kano, Wata Mata ta Kira Wani Mai Gyaran takalma Wato Shoe Shiner don ya dinka Mata takalmin ta da ya tsinke.
Da mai gyaran takalmin yazo ta bashi takalmin da nufin ya ci gaba da aiki, Sai ita Kuma ta Koma cikin gida ta ci gaba da aikace-aikacen ta, ta bar Mai gyaran takalman a kofar Gida.
Shi Kuwa Mai Gyaran takalmin nan ko da Ya ga ta shiga gida, ya Leka gabas da yamma bai ga Kowa ba, ya dai tabbatar babu Mai ganin Shi, Kawai Sai ya fitar da wani abu daga cikin dan akwatin sa ya sanya Wa takalmin ya dinke da Shi.
Inda Allah ya rufa Wa matar nan asiri shine, ashe wani mutum Yana Saman Bene Yana Kallon duk abinda Mai Gyaran takalmin Ke aikatawa.
Bayan Mai gyaran takalmin ya gama dinke takalmin, Sai Ya Kira Matar da ta zo ta gwada ta gani idan yayi, matar Nan ta dauki Kafar ta zata sa takalmin Nan Kenan Sai Mutumin dake Saman benen Ya 'Daga Murya Yace " Hajiya Kar ki sa takalmin Nan" Matar Nan Sai ta tsaya cak cikin Mamaki har mutumin ya sauko daga Saman Benen Yace Wa Mai Gyaran takalmin ya fara sa wa tukunna.
Nan aka yi aka yi yasa takalmin nan amma ya yi Kememe ya ce ba zai sa ba, Nan Fah Mutane suka taru makil aka tilasta mishi Sai ya sa.
Allahu Akbar, Idan dai baka da hakkin Mutum toh Allah Mai Kare Ka ne, Allah dai Ya sa Matar Nan ba ta da rabon wahala, kuma dai Allah yasa ranar nan ce dubun Mai Gyaran takalmin zai cika.
Bayan ya Sanya takalmin Nan, Kun San Me ya faru?
Ai Ko da ya sa takalmin, Nan take Kawai sai takalmin ya sake tsinkewa, ashe Abin da Mutumin nan ya ganshi yana sawa takalmin zare ne mara kwari, ba lilo bane Kamar Yadda Masu Gyaran Takalma Suka Saba Amfani da shi.
Karshe dai aka tilasta shi dole ya sa zare me kyau mai qwari ya sake dinke takalmin.
Don haka 'Yan Uwa a yi hattara, Maha'inta sun yi yawa. 🚶🚶🚶
Sannu da karanta Gulma😂
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.