Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsintsiya A Watse

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Da Arewa muna da hange,
Ko manya masu kishi,
Za mu so junanmu sosai. 

Tsintsiya ɗaya ne mutane,
Na Arewa a da dukkanmu,
Amma yau ga mu nan dai.

Mun rarraba kanmu nan can,
Nan Kirista can Musulmi,
Mun zare wukar ƙiyayya.

Tinubu Obi Atiku,
Ƙuri'un da suke gadara,
Mu ne muka ba su jingim.

Walƙiya dai gata an yi,
Kokwanto babu saura,
Mu ne da yawa a zaɓe.

Kaffara ba na yi ni,
Gwamnati in an kafa ta,
Masu mora masu kuka.

Da sannu da sannu sannu,
Za a bar mu a baya cancan,
Maƙiyanmu a ƙarfafe su.

Ko namu da munka zaɓa,
Haka ya yi muna ganinsa,
Wasu can ya gina idonmu.

A karo biyu babu kunya,
Kano haka nan ya bar ta,
Ba aiki ba kulawa.

Tashar jirgi na Baro,
Ajaokuta bai gina ba,
Haka Mambiya bai kula ba.

Shekararsa takwas a mulki,
Hanyar mota da babur,
A Katsina bai gama ba.

Takashin baya ne mu,
A komai yau Arewa,
Domin haka mun ka zaɓa.

Manyanmu suna ta sata,
Talakawa na ta maula,
Yara na shaye-shaye.

Ba babba guda Arewa,
Wai kowa babba ne shi,
Tsintsiya ne mu a watse.

Da Arewa muna da manya,
Masu kishi masu sonmu,
Za mu raya Arewa gaske.

Da Arewa muna da kishi,
Ba mu ƙin junanmu yanzu,
Za mu bar gilli ga juna.

Da Arewa muna da wayo,
Za mui tsari na gaske,
Na raya ƙasar Arewa.

Noma ƙira da saƙa,
Ilimu har kasuwanci,
Za su samu a nan Arewa.

Amma kas ga mu nan dai,
Ba kishi babu hange,
Na nesa muna ta shirme.

Tsintsiya in ba ta shara,
Yawan wofi gare ta,
Ba ta amfanawa kanta.

'Yan Arewa maza da mata,
Musulmi har Kirista,
Yara manya mu farka.

Gobenmu tana hanninmu,
Mu raya ko mu rusa,
Gaskiyata na faɗe ta.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

13/3/2023

Post a Comment

0 Comments