Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Matar Da Ta Yi Tsarin Iyali, Idan Aka Saketa, Dole Ta Jira Jini Uku

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Tambayoyi Da Amsoshi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum Malam macen da ba ta haila saboda planning na wasu watanni, yaya za ta yi idan aka saketa? Allah ya Kara Ikhlasi

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam. Za ta jira har ta ga jini uku, ko da kuwa za ta yi shekaru (10) Kamar yadda aya ta (228) a suratul Bakara ta Yi bayanin iddar matar da aka saka, Kuma ba ta daina jini ba.

Ina yiwa mata nasiha su nisanci yawancin magunguna da alluran tsarin iyali saboda suna sabbba Matsaloli na rikecewar al'ada.

Duk da cewa tsarin iyali na wucin gadi ya halatta, sai dai imani da cewa: kowanne abin haihuwa da arzikinsa yake zuwa yana da muhimmanci, saboda hakan zai sa kowa ya samu nutsuwa, ya daina tsorata da yawan yaran da zai haifa.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments