This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
Musa Suleiman
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto,
Nigeria
musasuleiman424@gmail.com
Hauwa’u Salihu
Usman
Department of
Hausa, Shehu Shagari College of Education, Sokoto, Nigeria
Tsakure
Babbar manufar wannan bincike ita ce nazartar littafin
Gogan Naka domin fito da hikimomin da marubucin ya yi amfani da su wajen jan
hankalin mai karatu ko manazarci. An ɗora wannan bincike a kan ra’in hanyar nazari ta gargajiya ( Traditional
Approach). An keɓance binciken a kan littafin Gogan
Naka. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi shi ne rubuce-rubucen
masana da suka jiɓanci wannan bincike. Binciken ya
tabbatar da cewa marubuci na iya cusa hikimomi da fasahohinsa a lokacin da yake
ƙulla tunaninsa yayin rubuta littafinsa.
Bisa ga haka, takardar ta tabbatar da bankaɗo salailan da marubucin ya yi amfani da
su a cikin littafinsa tare da taurarin da ya cusa a cikin wannan littafi.
Fitattun Kalmomi: Gogan Naka,
Mahanga, Nazari
1.0
Gabatarwa
Nazarin ƙagaggun labaran zube fage ne na nazari
mai faɗi, wanda duk in da mai bincike ya kai
ga ƙwƙƙwafi sai dai ya yi iya ƙoƙarinsa. Wannan yana ɗaya daga cikin manyan ɓangarorin nazarin adabi, wanda ake nazartar littattafai
daban-daban a Harshen Hausa. A nan ne ake nazartar kayan cikin littafi. A
wannan aiki za a yi nazarin littafin “Gogan Naka”, tare da fito da irin
hikimomin da marubucin ya ƙunsa a cikin littafinsa, ta yadda zai ƙayatar da mai nazari. Kai tsaye
binciken ya mayar da hankali kan muhimman abubuwa da suka haɗa da:
a.
Gano jigogin wannan littafin.
b.
Fito da yadda marubucin ya tsara littafinsa.
c.
Zaƙulo taurarin da marubucin ya yi amfani
da su a cikin littafin nasa.
d.
Bankaɗo salailan da ke ƙunshe a cikin littafin.
1.2 Gabatar Da Littafi
Wannan littafi da za a yi nazari a kan shi sunansa “Gogan Naka” Na Malam Garba Funtuwa. An
buga wannan littafi a shekarar (1978), wanda Gaskiya Corporation suka buga shi.
Daga baya wannnan maɗaba’a aka sanya mata suna zuwa,
“Northern Nigerian Publishing Company”. Dalilin da ya sa marubucin rubuta wannan littafi shi ne sha’awa. Ya
rubuta wannan littafi ne ba tare da shiga wata gasa ba ko makamanci haka. Ba
kuma wani ya sa wannan gagarumin aiki ba dan ya biya
shi, kawai sha’awa ce ta ba shi wannan damar rubuta wannan littafi.
1.3 Tarihin Marubuci
Masu bincike sun yi iya ƙoƙarinsa dan mu samu tarihin wannan marubuci, amma abin ya gagara. Mun samu lambar ‘yarsa[1] amma ta faɗa mana cewa “Allah ya yi masa rasuwa
tun tana ƙarama. Haka kuma, ta yi ƙoƙarin haɗa mu da babban yayansu,[2] amma bai ba mu haɗin kai ba. Wannan yasa ba mu samu
wannan bayani game da mahaifinsu ba, wanda shi ne marubucin wannan littafi.
2.0 Jigo
Jigo dai shi ne saƙon da
marubuci yake ƙoƙarin isarwa
ga jama’a. Kuma shi ne manufar da ko me ke ɗamfare a
jikinta ( Ɗangambo, 1995: 372). Don haka, za
a fahimci cewa jigo shi ne ruhin duk wani abu da ake son aiwatarwa a rubuce ko
kuma a karance, domin shi ne maƙasudin wannan rubutun. Jigo shi
ne ginshiƙin duk wani abu da ya dogara da
kansa a cikin littafi ko kuma waƙa.
Ɗangambo
(1995) ya ƙara taƙaita ma’anar
jigo inda yake cewa: jigo shi ne ginshiƙin rubutu. Shi ne dalilin ko maƙasudin da ya
sa har marubuci ya ɗauki alƙalaminsa ya
yi niyyar rubuta abin da ya rubuta.
Jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama’a, kuma duk wani
salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai yi amfani da su, zai yi hakan ne
da nufin isar da saƙonsa ga jama’a (Sarɓi, 2007: 71).
Bisa ga abin da magabata suka bayyana kan ma’anar jigo, a
taƙaice za a iya cewa cewa:
Jigo shi ne dukkan wani saƙo ko manufa ko ginshiƙin abin da ya sa aka rubuta labari ko
dalilan da suke sa marubuci ya rubuta littafinsa. Don haka duk wani abu da za a
faɗa a cikin labari, ya kan danganci jigon
wannan labari.
2.1 Kashe-Kashen Jigo
Masana sun bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, wato babban
jigo da ƙaramin jigo. Bunza (2009) da Sarɓi (2007) da Ɗangambo (2007) duk sun tafi a haka. Don
haka, yanzu za mu dube su ɗaya-bayan-ɗaya don ganin yadda abin yake.
2.1.1 Babban Jigo
Babban jigo shi ne abin da mawaƙi ko marubuci ya sa gaba gadan-gadan
domin ya feɗe shi a gane shi sosai. (Bunza, 2009).
Babban jigon wannan littafi shi ne: “ Jarunta” da “ Buwaya”.
2.1.1.1. Jaruntaka
Jaruntaka na ɗaya daga cikin babban jigon wannan
littafi, musamman idan aka dubi shafi na 27 inda, Indo ya nuna jaruntakarsa
lokacin da suka yi artabu da Runbumbaushe mai garin Tatunas. Ga yadda
aramgamarsu ta kasance.
“ ...Sa’ad da Runbunbaushe ya iso, Indo
ya ga kawunansa sun kai wajen dubu. Daga nan sai ya ce, “ Kai ja’irin banza,
wannan ba ta yi maka da ma ka sake. Na gane dabonka. Tsafi gaskiyar mai yi, na
aure ta aure ni .” Da ya duba ƙasa ya ga Indo can kamar wani ɗan ƙwaro, sai ya ce “ Shin wannan ƙwaron kai ne Indo ko rigima ce! ” Indo ya ce “ To, bari ka ga rigima ta ” Ya sa ƙafa ya shure dokin Runbunbaushe suka faɗi ƙasa rica, dokin ya mutu shi kuma ya suma.”
2.1.1.2. Buwaya
Baiwa shi ne nuna wata buwaya
da Allah ya hore wa wani mutum, na aiwatar da wani abu na ban mamaki da mutane
ba su taɓa zaton hakan
za ta faru ba a wannan lokacin. Baiwa na ɗaya daga cikin ƙanannan jigogin wannan littafi. Dalili kuwa shi ne duk
abin da tauraro Indo ya ce wani abu ya faru, nan take za a gan shi kamar yankan
wuƙa. Dubi shafi na 36 inda, Indo ya
umurci Sarkin Jabulakaf da dukarunsa kan su yi ta ƙundumbala suna faɗuwa da ka, kamar yadda za a gani:
“...Ko da suka zo kusa da Indo, sai
suka zabura gare shi. Nan da nan Indo ya ce, “ Duk ku yi ta ƙundumbala kuna faɗuwa da ka”. To ka san fa Aljannu basa mutuwa, ko sun mutu
sa farfaɗo. Kafin ya rufe baki duk sai sukai ta ƙundumbala suna faɗuwa da ka...”
2.1.2 Ƙaramin Jigo
Ƙarami jigo ya saɓa wa babban jigo ta kowa ce fuska. Na
farko dai abin da ya kyautu a kula shi ne; ƙaramin jigo ɗa ne ga babban jigo, domin babban jigo ke haifar da shi.
Haka kuma, ba don ƙananan jigogi ba da babban jigo bai
fito fili ba sosai aka gan shi ba. Duk wani labari da aka gina kan wani babban
jigo ɗaya, za a samu wasu ƙananan da yawa da za su mara wa babban
jigon baya, domin ƙawata shi da ƙara fayyace shi sosai. (Bunza, 2009: 64).
Idan aka ce ƙananan jigogi dai, to ana nufin tubalan
da suka gina babban jigo, su waɗannan tubalan sun danganta daga waƙa zuwa waƙa, ma’ana dai kowace waƙa da irin nata tubalai da suka samar da
jigonta. Haka abin yake ga rubutun zube. Dan haka, littafin yana ɗauke da jigogi da suka haɗa ɗa:
2.1.2.1 Neman Magani
Neman magani shi ne fita wajen
wani ma’abocin sanin magunguna musamman na gargajiya ko ‘Yar-mai-ganye ko boka
ko wani malamin tsubbu da nufin neman maganin wata cuta da ke damun wani ko
wata domin a samu waraka. Neman magani yana ɗaya daga cikin ƙananan jigogin wannan littafi. Domin marubuci ya nuna
yadda Ramatu da Dangana suka yi ta fama wajen neman maganin haihuwa kamar yadda
za a gani daga alƙalamin marubucin a shafi na 2 na
littafin kamar haka:
“...Bai tsaya wata-wata ba sai ya kwashe
kuɗin ya kai wa Malam Muzayyanu, ya
habarta masa dukan abin da ke tafe da shi sarai. Malam Muzayyanu ya ce, “
Dangana maganar nan ta biɗar haihuwa tana da wuya kwarai da gaske....”.
Haka kuma, a shafi na 31 Sakin layi na biyu, Marubucin ya
nuna yadda ake ta faman neman magani Sarkin Susansa Fasaha, wanda ya kai wajen
wata uku a kwance. Sai an kwantar sai an tayar, kamar yadda za a ji daga bakin
marubucin, inda yake cewa:
“...An yi maganin har an gaji, amma ba
a sami gaikau ba. Ni ma da ka gan ni nan, zani neman mai magani ne”. Ko da Indo
ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce, “Allah ya sawaƙe. Tun da neman mai magani za ka, ka
huta, ni na isa...”.
2.1.2.2 Yaudara
Yaudara na nufin jan hankalin wani tare da lallaɓawa cikin ruwan sanyi domin a kauda tunaninsa zuwa ga
wani abu na daban, domin cimma wata buƙata ta musamman. Yaudara ta zama ɗaya daga cikin ƙananan jigogin wannan littafi. Domin marubucin ya bayyana
yaudara a matsayin ƙaramin jigonsa a shafi na tara 9 kamar
yadda za a gani.
... Da Nur ta ga lalle baccin ya yi
nisa, sai ta tashi saɗab-saɗab, ta buɗe Dangana ya fito. Ta ɗauko Babarbaren takobin nan tsafaffe ta ba shi. Dangana
ya yi kwance-kwance ya danƙara masa ƙas!, ya sake ƙarawa, sa’annan ya tsaya yana kallon ikon Allah.
Maridi ya farfaɗo daga giya ya ce. “In kana son ka
kashe ni ne to, sai ka ƙara sara na sa’annan in mutu. In ba ka ƙara sara ba, lalle yanzu ina miƙewa in kashe ku duka”. Nur ta ce da
Dangana, “Kul, kada ka ƙara”. Ta dubi Maridin nan, ga shi shirin a kwance, ta ce,
“Haba tsohon banza, tsohon kare, tsohon Maridi, maci amana. Ɗan La’ananne, ka makara. Daga gare ni ba zaka
sake yi wa wani makirci ba”. Da Maridi ya ji haka sai yace, “Anya Nur haka
tsakaninmu zai zama? Ke ce yau har da yaudara ta? Ki tuna fa duniyar nan
ba ki da wanda ya fini.
3.0 Zubi da Tsari
A nan za a yi bayani ne kan
yadda marubuci ya tsara littafin da yadda ya jera tunaninsa. Ya tsara
littafinsa babi-babi ne ko kashi-kashi ko kuma fitowa-fitowa. Sannan a nan ne
za a sakin layi nawa ya yi amfani da shi da adadin kalmomin da jimlolin da ya
yi amfani da su da yawan shafukan da ke cikin wannan littafi.
3.1 Tsarin Jimloli
A nan a na so a ga yadda
marubucin littafin ya shirya jimlolinsa. Dogaye ne jimlolin ko kuma gajeru ya
fi amfani da su a cikin littafisa. Marubucin littafin
ya yi amfani da tsarin jumloli iri biyu wato dogayen jimloli da kuma gajerun
jimloli.
Ta fuskar dogayen jimloli, marubucin ya yi amfani da su a
cikin littafinsa a shafi na 3 sakin layi na farko in da yake cewa:
“Ya kawo sandar
zinariya wadda darajarta ta kai jaka dubu ya ba Dangana .”
Ka kuma a shafi na biyu (2) ya ƙara kawo irin wannan doguwar jimlar:
“Ni a gani na ya fi
kyau mu haƙura in Allah ya nufe mu da ganin Kwammu.”
Ta fuskar gajeriyar jimlar kuwa, marubucin ya yi amfani
da gajeriyar jimla a shafi na tara (9) inda ya ke cewa:
“Ya yi ta bacci da masori.”
Ba a yi nan ba a shafi na sha-biyar (15). inda yake cewa:
“To, jeka na yarda.”
3.2 Tsarin Sakin Layi
Marubucin ya yi amfani da tsarin sakin layi guda uku (3)
a duk shafin littafi guda. Haka kuma, wannan littafi yana ɗauke da shafuka guda arba’in da uku (43). Wanda bisa
wannan ƙididdiga za a ga cewa; littafin yana ɗauke da sakin layi guda ɗari da ashirin da tara (129).
3.3 Tsarin Yawan Jimloli
Marubucin ya yi amfani da tsarin yawan jimloli guda biyu
(2) a duk layi ɗaya na shafi. Haka kuma, duk shafi guda
yana ɗauke da layuka guda talatin da huɗu (34), wanda jimillar jimlolinsu ya kama guda sittin da
takwas (68) a duk shafi. Bugu da ƙari, wannan littafi yana ɗauke da shafi arba’in da uku (43). Ke nan adadin jimlolin
da marubucin ya yi amfani da su sun kai dubu biyu da ɗari tara da ashirin da huɗu (2924), a duka littafin.
3.4 Tsarin Yawan Kalmomi
Marubucin ya tsara littafinsa, inda kowane layi yake ɗauke da kalmomi goma sha biyu (12). Sannan, kowane shafi
yana ɗauke da layi talatin da huɗu. Wanda idan aka lissafa, za a samu kalma ɗari huɗu da takwas (408) a duk shafi ɗaya na littafin. Duba da wannan sakamakon da aka samu, duk
shafi ɗaya na littafin na ɗauke da kalmomi ɗari huɗu da takwas (408). Haka kuma, littafin yana ɗauke da shafi arba’in da uku (43), wanda idan aka ninka
arba’in da uku (43) sau (x) ɗari huɗu da takwas. Bisa ga haka, adadin kalmomin da marubucin
ya yi amfani da su sun kai kalma dubu goma sha bakwai da ɗari biyar da arba’in da huɗu (17,544) a littafin gaba ɗayansa.
3.5 Waƙa a Cikin Labari
Akwai waƙa a cikin wannan littafin, marubucin ya
kawo waƙa a cikin shafi na 39, a lokacin da
Indo ya je dutsen Sangiri. A nan ne ya rera wannan waƙa lokacin da yake zagaya wannan dutse.
Ga bin da yake cewa:
“Wa’in kana min rabbi,
Wa’in
kana rabbahu.
Wa’in kana min maula,
Wa’innaka
maulahu.
Ba iya nan Marubuci ya saka waƙa a cikin labarin ba. A shafi na 41-43
Marubucin ya sake waƙa inda Maroƙa suke yi masa waƙa suna yabonsa lokacin da ya zama
Sarkin Masar. Ga waƙar kamar haka:
“Bismillahi Rabbana za ni waƙa,
Zan
tsara sabo da Sarki Indo.
Duk jama’a ku
tattaro na gare ni,
Kuji
waƙa ta shugaban namu Indo.
Ga goyo na
Ramatu na kira ka,
Ga
goga na Barkatu yaka Indo...”
3.6 Warwarar Jigo
Kamar yadda ya gabata, an bayyana cewa babban jigon
wannan littafi shi ne “ Jarunta” da “ Buwaya”. A shafi na 27 an ga yadda Indo
ya nuna jaruntakarsa, inda Indo ya yi artabu da Rumbunbaushe mai garin Tatanus.
Rumbunbaushe ya nuna wa Indo dabonsa iri-iri, amma duk a banza, bai ji wani
shakka ko tsoransa ba. Daga dai ƙarshe Indo ya sa ƙafarsa ya shure dokin Rumbunbaushe suka
faɗi a ƙasa rica, dokin ya mutu shi kuma
Rumbunbaushe ya suma. Haka abin yake wajen nuna buwaya. Tauraro Indo duk inda
ya ce wani abu ya faru, nan take za a ga abin ya faru kamar yankan wuƙa.
Baya ga wannan, akwai ƙananan jigogi irin su: “ Yaudara ” kamar yadda ya gabata. An ga
yadda marubucin a shafi na 9 ya nuna yadda Nur ta yaudari Maridi ta hanyar faɗawa Dangana yadda za a bi a kashe shi. Kuma Dangana ya bi
duk abin da Nur ta faɗa masa, har su kashe Maridi.
“ Neman magani ”. A shafi na biyu 2, an
ga yadda marubucin ya nuna yadda Ramatu da Dangana suke ta faman neman magani
haihuwa, domin su ga ƙwansu kafin mutuwarsu.
Haka kuma, marubucin ya yi amfani da “ Buwaya ” a matsayin ƙaramin jigonsa. Inda ya nuna yadda Indo
ke baiwa abokan faɗansa umurni wani abu, kuma nan take za su
ci gaba da yin wannan abin da ya umarce su. Kamar yadda ya zo a shafi na 36,
inda ya umurci dakarun Sarkin Jabalakaf da su yi ta ƙundumbala suna faɗowa da ka, kuma nan take suka bi umurnin Indo suka ci gaba
da yin ƙundumbala.
4.0 Taurari
Taurari su ne, irin mutanen da mawallafi ya kan sako a
cikin labarinsa. Idan suna da yawa, maza da mata da yaro da babba na labarin su
ne ake kira taurari. Idan kuma ɗaya ne shi ake kira tauraro. (Muktar, 2004:
8)
Wannan littafi ya ƙunshi taurari da suka haɗa da:
1.
Dangana (Abdul Bakara)
2.
Ramatu
3.
Malam Muzayyanu
4.
Nur
5.
Muridi
6.
Munir
7.
Hausatu
8.
Boko Shabbaki
9.
Ƙasim (Indo)
10.
Kalleri
11.
Sanda Na Sanda
12.
Kudasa
13.
Sarkin Ɓarayi
14.
Malam Dinar
15.
Rumbumbaushe
16.
Fanfaragi
17.
Gwangiran
18.
Hamburum haya
19.
Bodari
20.
Kunkumadi
21.
Tunkun Ɓauna
22.
Kunkuru
23.
Mubarakatu
24.
Samhani
25.
Kantafarga
26.
Kufuyatu
27.
Jauharatu
28.
Boka fanɗare
29.
Umar Sanda
30.
Dargaza
4.1 Babban Tauraro
Babban tauraro shi ne wanda aka gina labari a kansa wanda
kuma mawallafi yake ta faman tattalinsa, kuma ba a so wani abu ya same shi a
cikin labari.(Mukhtar, 2004: 68). A wannan labarin babban tauraro shi ne “ Ƙasim (Indo) ”.
4.1.1 Fitaccen Tauraro
Shi ne tauraro wana suke gudanar da komai tare da babban
tauraro. Fitaccen tauraro a wannan litafi shi ne ”Dangana (Abdul Bakara) “.
4.1.2 Sumammun Taurari
Sumammun taurari su ne waɗanda aka fara labari da su, sai suka ɓace, daga ƙarshe suka ƙara fitowa ko a tsakiya. Sumammun
taurari a wannan littafi su ne “ Ramatu da Nur da Mubarakatu.”
4.1.3 Tauraro Mai Tsawon Rai
Shi ne tauraron da aka fara labari da shi, kuma aka kai
har ƙarshen labarin da shi. Amma kuma bai
taka rawar gani ba kamar yadda babban tauraro ya taka ba. Tauraro mai tsawan
rai a wannan littafi shi ne “Abdul Bakara”.
4.1.4 Tauraro Mai Walkiya
Shi ne wanda yake fitowa kamar walkiya a cikin labari
kuma sai ya ɓace, can kuma sai ya ƙara fitowa a tsakiya ko kuma a ƙarshen labarin. A cikin wannan
littafin, an samu taurari masu walkiya da suka haɗa da:
I.
Malam Muzayyinu
II.
Malam Dinar
III.
Ummaru Sanda
4.1.4 Boyayyen Tauraro
Shi ne tauraron da aka bayyana shi da baki, amma bai
bayyana a zahiri cikin labari ba.[3] Don haka, wannan labari yana ɗauke da ɓoyayyun taurari da suka haɗa da:
I.
Katafare
II.
Kutemeshe
III.
Kwanta-Kwaran
IV.
Katanga
V.
Kushekara
VI.
Na-Kantu
VII.
Dargaza
5.0 Salo
Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu a kan
ma’anar salo ta hanyoyi daban-daban, duk da yake abu ɗaya suka fuskanta. Gusau (1993) ya bayyana salo da cewa:
“ Shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko rubutu.
Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayi harshensa da zaɓar abubuwa da suka dace game da abin da yake son
bayyanawa. Daga nan ne za a fahimci salon mai sauƙi ne ko mai kashe jiki maras karsashi
da sauransu.
Yahya (1999) ya ce “ Salo dabara ce ko hanya mai iya kwalliya
ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana.”
Dangambo (2007) ya ce: Masana da manazarta suna ganin
cewa salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu
sigogi nasa daangane da ma’anarsa. To amma muna iya cewa salo shi ne hanyoyin
isar da saƙo.
A bisa ra’ayin Dangambo yana cewa za a iya karkasa salo
kamar haka:
1.
Salo wani ƙari ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci.
2.
Salo wani ƙari ne na daraja a cikin karatu ko
furuci , wanda ba lalle ne a same shi cikin kowane rubutu ba.
3.
Salo ya shafi kauce wa wata daidaitaciyar ƙa’ida.
4.
Salo harsher wani mutum ne, wato yadda salon wani ya bambanta
da na wani.
Duba da waɗannan ma’anoni da masana da manazarta
suka bayar dangane da ma’anar salo. Za mu ga cewa marubucin wannan littafi ya
yi tsattsafin salailai da dama a cikin wannan labari kamar yadda za a gani.
5.1 Kirari
Kirari shi ne kwarzanta wani
abu tare da kambama shi fiye da ƙima ta yadda zai ji babu kamar
shi. Marubucin ya yi amfani da salon kirari a wurare daban-daban a cikin
littafinsa kamar yadda za a gani:
A shafi na 9 sakin laya na
farko yana cewa: “Dangana ya yi kamar zai ce wayyo saboda tsoro. Can sai ya ji
gogan tafe, yana kirari yana cewa:
“Ni ne Maridi
gogan Nur,
Ga mala’ikanku
fatake,
Tilas ku bi
ni ko don dole,
Ni ne maci
kasuwar sama,
Gogan Nur,
In kashe
mutum in ci namansa,
Wane wanda
bai sanni ba,
Ya zo ga ni,
Ni gogan Nur,
Ko da mai
musu, ya zo yanzu,
Ya je ƙiyama”.
A shafi na sha-takwas 18 sakin layi na ƙarshe, marubucin ya yi amfani da salon
kirari inda yake cewa:
”...Ko da Indo ya ji haka, sai yai kalmar shahada, ya yi
kirari ya ce:
“Sai ni Indo Ajanaku Mai Dawa ɗan Ramu,
Ni ne ɗan Ɓakara komai da ruwanka,
Ni ne Indo mai yaƙi da makangara,
Ƙaryarku ta sha ƙarya.”
Ba iya nan ya tsaya ba, idan aka dubi shafi na a shirin
da shida 26 sakin layi na ƙarshe nan ma ya yi kirari, inda yake
cewa:
“...Ko da Indo ya ji haka, sai ya ce, ku Arnan banza wane
ku, wane kashinku.
“Ni ne mutum guda tamkar da dubu,
Ni ne dan buzurwar
Akuya,
Arna maza bisa kanku,”
Haka kuma, ya ƙara wannan salo a shafi na 33 sakin layi na biyu. Inda
yake cewa:
“...Ar, Arnan banza, na ci na sha ba
dominku ba
“Ni ne mutum guda tangun da goma,
Na – Dangana mai abin mamaki,
Ni ne ɗan babban bajimi sankara babban wuya,
Ban yi ba sai da na shirya”.
5.2 Karin Magana
Marubucin ya yi amfani da karin magana a wurare daban –
daban a cikin littafinsa kamar yadda za a gani.
A shafi na 6 sakin layi na farko ya ce: “ Mai nema yana tare da samu. ”
A shafi na 10 sakin layi na ƙarshe, ya ce: “ Komai tsawon wuya dai kai shi ke sama .”
A shafi na 17 sakin layi na biyu (2) ya ce: “ Tun ran gini ran zane .”
A shafi na 21 sakin layi na ƙarshe ya ce: “ Mai
rabon kuwa ya ga baɗi ko ana ruwan kibau ai sai ya gani” Ya ƙara da cewa: “Ai mai rabon shan duka ba ya jin bari.”
A shafi na 22 sakin layi na ɗaya (1) ya ce: “ Ruwa
baya tsami banza.”
A sakin layi na biyu ya ce: “ Banza dai ba ta kai zomo kasuwa .” Ya ƙara da cewa: “Ai ko yaro na goye ya san kura.”
A shafi na 26 sakin layi na farko ya ce: “ Mai rabon shan duka ba ya jin bari”
A sakin layi na ƙarshe ya ce: “ yaro
ya san kura .”
A shafi na 36 sakin layi na farko ya ce: “ In ka ga makaho ya ce ai wasan jifa...”.
Ya ƙara da cewa: “ Inda
gwanin rawa zai faɗi .”
5.3 Dabbantarwa
Marubucin ya yi amfani da salon dabbantarwa a cikin
littafin kamar yadda za a gani. A shafi na 26 inda yake cewa: “ Ni ne ɗan buzurwar Akuya .”
5.4 Salon Tambaya
Marubucin ya yi amfani da salon tambaya a cikin
littafinsa a wurare daban-daban kamar yadda za a gani.
A shafi na 3 sakin layi na ƙarshe inda yake cewa: “ ...Da
zuwa ya ba Ɓauna ta ci ta ji abin ba kama hannun yaro, ta ce “Kai Bil
Adama, ina ka samo wannan abu mai ɗan karen daɗi haka? ”
A shafi na 5 sakin layi na biyu ya ce: “ ...Ramatu, kin ji kuma wata irin shiririta
wajen malamin nan. Shin ko ƙarya yake mana ne, yana dai so ne ya ci kuɗinmu a banza?”
A shafi na 6 sakin layi na farko ya ce: “...Kuma ai ka ji Allah ya ce tashi in taimake
ka. Me zai tsorata ka da wannan magana? ” Ya ƙara da cewa: “ Ya ya teku za ta gagare ka zuwa na Ramatu?”
A shafi na 7 sakin layi na biyu (2) inda yake cewa: “Dangana ya ce, ina ma ga rumuninsa?”
Ya ƙara da cewa: “Na ji. Amma ina so in sani in ce ko shi ne ya gaya miki wannan magana?”
A shafi na 9 sakin layi na ƙarshe inda yake cewa: “Da maridi ya ji haka, sai ya ce, “Anya Nur
haka tsakaninmu zai zama?”
A shafi na 12 sakin layi na huɗu (4) inda yake cewa: “Sarki ya faɗi sai ya ruɗe ya ce – Tana ina?”
A shafi na 18 sakin layi na uku (3) inda yake cewa: “Ko da Indo ya ji haka, sai ya ce ashe a
duniyar nan akwai garin da za ni har in rasa masauki?”
A shafi na 21 sakin layi na ƙarshe inda yake cewa: “Kai wannan samari ina zaka cikin daji ba
gida gaba ba gida baya?” Ya ƙara da cewa: “Ko baka san inda za ka ba ne?” Ya ƙara da cewa: “Ko kuwa taɗinta kake ji?”
A shafi na 24 sakin layi na ɗaya (1) ya ce: “Za ka
wuce Jabalakaf ne, ko kuwa za ka kwana biyu tukuna?”
A sakin layi na ƙarshe ya ƙara da cewa: “Buɗe mini ƙofa maza ” Sarkin ƙofa ya ce, kai wane ne?”
Ya ƙara da cewa” “Wo! Yaro wargi wuri garai. Wane kai da
Runbunbaushe me garin Tatunas?”
A shafi na 30 sakin layi na farko ya ce:
“Sarki ya tashi zaune tun, mutane suka yi
mamaki, don rabonsa da ganin Sarki a zaune tun yana da lafiya. Indo ya ce, kana
iya shan ƙazanta?”
A shafi na 34 sakin layi na farko ya ce: “ Kai bawan Allah kuwa me za ka yi a cikin
dajin nan?”
Ya kara da cewa: “ Ba
ka tsoron ‘yan fashi?”
A shafi na 36 sakin layi na farko ya ce; “To ran ka ya daɗe, me kake gani?”
5.5 Salon Al’ada
Marubucin ya yi amfani da salon al’ada cikin littafinsa
inda ya riƙa yin tsattsafin al’adu a wurare daban-daban
a cikin labarinsa.
A shafi na 12 sakin layi na uku (3) ya ce:
“ ...can kuma suka sami mutane mata da maza
ana jiransu, ga tambura, ga bushe-bushe da kaɗe-kaɗe iri-iri ba mai jin na wani.”
A shafi na 40 sakin layi na farko ya kawo al’adun sarauta
irin su:
I.
Sallama
II.
Kuyanga
III.
Gimbiya
IV.
Sarkin ƙofar
V.
Manzon Sarki
VI.
Dakarum Sarki
5.6 Salon Labari cikin Labari
Marubucin ya kawo salon labari cikin labari a shafi na 6
inda yake cewa:
“ ...Bayan ya natsa sai ya tambaye ta,
“ Menene dalilin zuwanki nan, kuma ga ki ke ɗiyata ce, amma ban sanki ba?” sai ta ce “Ai kakan ji
labarin wanka da yake nan birnin Bokhara ƙetaren Maliya yana sarauta. To, shi ne
ya haife ni. Ko ba kakan ji labarin Nur ba? Sai ya ce ai duk duniyar nan ba
inda sunanta bai je ba”. Ta ce, to ni ce .”
5.7 Salon Aron Harshe
Marubucin ya yi aron harshe a cikin littafin sa, inda ya aro
harshe Larabci ya yi amfani da shi kamar yadda za a gani:
A shafi na 23 inda yake cewa: “Marhaba-bika Indo Abdul Bakara. Ahalan wa sahlan.”
A cikin shafi na
39, a lokacin da Indo ya je dutsen Sangiri ya yi waƙa. A nan za a ga cewa ya rera wannan waƙa ne da harshen Larabci. Ga bin da yake
cewa:
Wa’in kana min rabbi,
Wa’in
kana rabbahu.
Wa’in kana min maula,
Wa’innaka
maulahu.
5.8 Wasiƙa Cikin Labari
Marubucin ya yi amfani da salon rubuta wasiƙa a cikin labarin. Inda ya rubuta wa
babban Mubarakatu, wato sarkin Masar wasiƙa kamar yadda za a gani.
A shafi na 29-30 ...Da
aka zo da Mubarakatu, Indo ya ce, “yau in Allah ya so za ki sadu da tsohonki Simhani.
Amma kafin ki tashi zan kashe Runbunbaushe a idonki.” Sa’annan ya juya ya murɗe wuyan Runbunbaushe ya mutu, kana ya rubuta takarda ya
ce:
Daga hannun Indo Ajanaku Mai Dawa,
Zuwa ga shugabana mai girma mai daraja,
Sarkin Masar Mohammad Simhan Ibn Ahmed Tahir.
Bayan gaisuwa ina shaida maka ga ɗiyarka Mubarakatu na tsamo ta daga halaka a hannun wani
maridi wai shi Runbunbaushe mai garin Tatunas. Bayan na kashe shi, na ribɗe gidajensa sai na sami wannan yarinya a can cikin wani ɗakin duhu. Da na tambaye ta, ta kwashe duk labarinta ta
faɗa mini. Kuma cikin rahamar Ubangiji na
sami wannan doki ya kawo ta gun ka. Amma in Allah ya yarda zan zo nan birnin
Masar wata rana. Asali na ni mutumin Bokhara ne, sanan ubana Abdul Bakara, mun
kuwa gaji sarautar Bokhara iyaye da kakanni gaba da baya. Kome daɗewa zan zo Masar. Wassalam,
Ni ne mai neman albarka gare ka,
Indo Ajanaku.
5.9 Nason Addinin Musulinci
Marubucin ya nuna tasirin addinin Mussulunci ga babban
tauraron wannan littafi. Domin kuwa duk abin da zai aiwatar sai ya danganta shi
da addinin Musulunci, kamar yadda za a gani:
A shafi na talatin 30 inda yake cewa: “...Kuma cikin rahamar Ubangiji na sami wannan
doki ya kawo ta gun ka, amma in Allah ya yarda zan zo nan birnin Masar wata
rana”.
A shafi na 31 inda Indo yake maganar ba da magani, yake
cewa: “...Ko da Indo ya ji haka, sai ya
yi murmushi ya ce, “Allah ya sauwaƙa”.
A shafi na 35 inda ya ke cewa: “...Ko da Indo ya ji haka, sai ya yi murmushi ya ta da kai sama ya yi
godiya ga Ubangiji talikai.”
5.10 Nason Maguzanci
Marubucin ya yi tsattsafin Maguzanci a cikin labarinsa
kamar yadda za a gani.
A shafi na 26 sakin layi na 2 inda yake cewa:
...Runbunbaushe
mai garin Tatunas ya shaida masa duk yadda aka yi. Ko da ya ji haka sai ya
husata ya zagi rana, da wata da taurari, da wuta. Ya shirya iya yaƙi kamar mutum ɗari ya ce maza su je su zo masa da kan Indo.
A shafi na 36 sakin layi na 2 ya ƙara nuna irin abin da ya gabata. Inda
ya ce:
...Ko da manzo ya
je ya faɗawa sarkin yaƙinsu, nan da nan ya husata mai tsanani
ya zagi rana, da wata, da taurari da wuta, ya hawo toron giwa jama’arsa na biye
da shi.
Haka abin yake, a shafi na 39 inda ya ƙara nuna Maguzanci tsantsa ta hannun
Boka Fanɗare, inda ya ce:
...Sarki ya sa
wani bawansa ya je maza ya kira Boka Fanɗare. Nan da nan ya tafi suka zo tare. Sai sarki ya kwashe
labari sarai ya gaya masa, sa’annan boka fanɗare ya ce “Ai sai in koma gida in zo da kayan dubana. Nan
da nan ya tafi ya ɗauko ya zo gaban sarki ya shiga aiki.
Ya watsa wuri, ya jefa ‘yan dambe, ya zuba alƙaluma ya buga ya share, sai ya ta da
kai ya dubi Indo ya ce “Indo Ajanaku Mai Dawa ɗan Ramu barka da zuwa.
5.10.1 Salon Aron Kalmomi
Marubucin ya yi amfani da aron kalmomi, musamman daga
harshen Larabci kamar yadda za a gani:
I.
Baitumali
II.
Allah
III.
Tawali’u
IV.
Hamdala
V.
Sahibul-Junau
VI.
Marhababika
VII.
Ahlan wasahalam
VIII.
Walaha
IX.
Rabbu
5.10.2 Salon Amfani da Sunaye na Musamman
Marubucin ya yi amfani da sunayen garuruwa da wurare da
gulabe da koguna da rafuka da dabbobi da tsuntsaye da kuma kwari. Bisa ga
wannan za a kawo su daki-daki.
5.10.3 Sunayen Garuruwa
1.
Kan’an
2.
Lumana
3.
Bilgarib
4.
Bolehara
5.
Sumaila-khan
6.
Birnin Rayyasa
7.
Kaironi
8.
Masar
9.
Samar Kandi
10.
Makoli
11.
Burham
12.
Kagatakowa
13.
Birnin siyasa
14.
Jabalakaf
15.
Karsasawa
16.
Kubura
17.
Tutunas
18.
Kartum
19.
Fasaha
20.
Birnin Somaliya
21.
Birnin Kaf
22.
Birnin Hariri
23.
Shariritun
5.10.4 Sunayen Dabbobi
1.
Zaki
2.
Zakara
3.
Doki
4.
Giwa
5.
Ɓauna
6.
Kura
5.10.5 Sunayen Koguna
da Gulabe da Koguna
1.
Tekun Harhalta
2.
Bahar Maliya
5.10.6 Sunayen
Dazuzzuka
1.
Dajin Rugu
2.
Dajin samagi
3.
Dajin Na-Kurururu
4.
Dajin Kwantai
5.
Dajin Farbaba
6.
Dajin Tsantseni
7.
Dajin Kanikayi
8.
Dajin Domana
5.10.7 Sunayen
Duwatsu
1.
Dutsen garuje
2.
Dutsen Da-na-sani
3.
Dutsen siraiɗane
5.10.8 Sunayen
Aljannu
1.
Maridi
2.
Sarkin Rafi
3.
Jan Ƙarago
4.
Wakadago
5.
Madagira
6.
Karamkaban
7.
Kwantagi
8.
Dodanni
9.
Gantagero
10.
Dandagazau
11.
Samangi
12.
Burguzan
5.10.8 Salon
Amfani da Tsofaffin Kalmomi
Salo ne da marubucin littafi ke yin amfani da tsofaffin
kalmomi a yayin da yake shimfiɗa labarinsa. A irin wannan yanayi wasu
kalmomin da marubucin ke yin amfani an daɗe ba a yin amfani da su, kasancewar
zamani da kuma tasirin baƙin al’umma da aka cuɗanya da su a ƙasar Hausa. Wannan ne ya sanya duk wasu kalmomin Hausa
suka ɓace wasu kuma suka salwance ba a cika
amfani da su ba a wannan lokacin. Marubucin ya yi amfani da tsofaffin kalmomi a
cikin littafinsa kamar yadda za a gani:
1.
Kalaci
2.
Niƙau
3.
Alfen
4.
Kiri
5.
Hita
6.
Kuyat
7.
Banju
8.
Batta
9.
Kwatashi
10.
Waga
11.
Tsariga
12.
Adila
13.
Habarto
14.
Boto
15.
Buka
5.10.9 Salon Farawa
Marubucin ya yi amfani da salon farawa na gargajiya wanda
yake nuna lokaci kamar yadda za a gani:
“A zamanin da”
7.0 Kamalawa
Wannan bincike kai tsaye ya mayar da hankali ne wajen
nazarin littafin Gogan Naka. Nazari irin wannan na taimakawa wajen zaƙulo fasahohin da ke tattare cikin
rubuce-rubucen adabi tare da kundace su. Daga cikin abubuwan da wannan bincike
ya fi mai da hankali kansu sun haɗa da; gano jigon wannan littafi, wanda
ya kasance jarunta da buwaya da babban tauraron wannan littafi ya nuna. Sannan,
akwai ƙananan jigogin littafin da suka haɗa da; neman magani da kuma yaudara. Haka kuma, marubucin
ya yi amfani da salailai da dama a cikin labarinsa. Daga cikin salailan da ya
kawo akwai kirari da karin magana da dabbantarwa da salon tambaya da salon
labari cikin labari da aron kalmomi da kuma al'ada. Daga ƙarshe maƙalar ta kallaci nason addinin Musulunci
da Maguzanci da kuma amfani da tsofaffin kalmomi a cikin labarin.
Manazarta
Abdullahi, A.A. (1987). Tasirin Adabin Baka kan ƙagaggun littattafan zube na Gasa Ta Farko,
1933. Kundin Digiri Na Ɗaya. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Abdullahi, I.S. (1990). Abubakar Imam’s Life, Works and Contribution
to Society. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na sashen Harsunan
Nigeriya da Africa. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Buhari, M. (1988). Nazarin jigogin wasu ƙagaggun labaran Hausa. Kundin Digiri Na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.
Funtua, M..G (1978) . Gogan Naka. Zaria: Northern Nigerian
Publishing Company Limited.
King, B (1971). Introduction to Nigerian Literature. Evans Brothers. Lagos
Malumfashi, I. (2007). Adabin Abubakar Imam. Sokoto: Gwarkuwa
Media Services Limited.
Mukhtar, I. (2004) . Jagoran Nazirin Ƙagaggun Labarai. Kano: Benchmark
Publisher Limited.
Yahya, A.B.
(1999). “Salo Asirin Waƙa”. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya, A.B.
(1997). “Jigon Nazarin Waƙa”. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya,A.B.(1988).“Hikima A Cikin Wakokin Hausa”Sakkwato:Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
[1] Wadda a yanzu haka take karatu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
[2] Wanda ma’aikaci a hukumar tsara Birane ta Jahar Katsina.
[3] Irin wannan tauraron baya fitowa a zahiri a gan shi sai dai kawai a yi
maganarsa a cikin labari.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.021
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.