This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
Dr.
Musa Fadama Gummi
Email: gfmusa24@gmail.com
GSM: 07065635983
TSAKURE
Daular Zamfara tana ɗaya daga cikin daulolin
ƙasar Hausa da wasu masana suka ce tana
cikin ‘banza bakwai’. Daga wani sashe na tsuhuwar daula ne aka sami jihar
Zamfara. Jihar tana nan a yankin arewa maso yamma na arewacin Nijeriya. Zamfara
ƙasa ce ni’imtacciya ta ɓangaren noma da ma’adinai na ƙarƙashin ƙasa. Akwai koguna da ƙoramu da suka ratsa jihar. Wannan ne ya sanya ake samun fadamu jefi-jefi a
wasu sassa na jihar. Akasarin al’ummomin wannan jiha manoma ne da makiyaya.
Shekaru aru-aru da suka shuɗe, manoma da makiyaya na Zamfara suna
zaune lami lafiya tsakaninsu da junansu. A wannan zamani da muke ciki, zaman
lafiya da amince wa juna ya ƙaranta a tsakanin
manoma da akasarin su Hausawa ne da kuma makiyaya da mafi rinjayensu Fulani ne.
Tsaro ya yi matuƙar taɓarbarewa a jihar
sakamakon rashin jituwa tsakanin waɗannan al’ummomi. Wannan ya sa har ake samun
sace-sacen dabbobi da kashe-kashe a tsaninsu musamman ma mazauna karkara.
Wannan muƙala ta ƙuduri anniyar yin waiwaye na bin diddigin ayyukan magabata dangane da tsaro
a Bahaushiyar al’ada da kuma duba a kan yadda har yanzu ake amfani da su a wasu
wurare da nufin samun tsaro. Ra’in da za a gina muƙalar a kai shi ne Bahaushen ra’in da ke cewa, ‘Da Tsohuwar Zuma Ake
magani.’ Tunanin wannan muƙala shi ne cewa, watsi
tare da kauce wa bin matakan tsaro na gargajiya da aka saba da su kuma suka
biya buƙatun tsaro ya taimaka sosai wajen
haifar da wannan tayar da zaune tsaye da ake samu a jihar. Wannan ya sanya muƙalar yin waiwaye kan matakan tsaron na gargajiya da nufin
zaƙulo yadda za a yi amfani da su a
matsayin ‘tsohuwar zuma’ da za a iya amfani da ita wajen magance matsalar tsaro
a wannan zamani. Za a yi haka ne ta hanyar tattaunawa da waƙilan tsaro masu ruwa da tsaki kan lamarin tsaro da ma waɗanda shaidi
abubuwan da ke faruwa dangane da lamarin. Muƙalar ta gano cewa kasawar hukuma da kuma al’umma haɗe da daina bin
wasu matakan gargajiya ne suka haifar da taɓarɓarewar tsaro don
haka a sake maido tare da ƙara inganta
matakan tsaro na gargajiya domin inganta tsaro.
Fitattunn kalmomi: Matakan tsaro, Gargajiya, Matsala.
1.0 Gabatarwa
Zamfara wata daula
da ta wanzu a ƙasar Hausa. Ana kyautata zaton cewa
daular ta kafu a shekara goma na farkon ƙarni na goma sha shida (Ƙn.16)[1] Daular ta roshe ne a wajajen tsakiyar ƙarni na goma sha takwas (Ƙn. 18), sakamakon rosa babban birninta
da Gobirawa suka yi.[2] Ƙasar Zamfara tana da ƙasar noma ni’imtacciya, mai dausayi sakamakon
albarkar ruwa na koguna da ƙoramu, waɗanda suka ratsa ta cikinta. Daga ciki akwai kogin Gagare,
da kogin Bunsuru, da suka ratsa jihar ta ɓangaren gabas maso arewa, wajajen Zurmi
da Ƙauran Namoda da Shinkafi. Kogin
Sakkwato ya ratsa jihar ne ta ɓangaren tsakiya, wajajen Gusau da Bunguɗu da Maru har zuwa Maradun da Bakura. Daga yammaci kuwa,
kogin Zamfara da kuma kogin Ka suka ratsa jihar ta wajajen Anka da Bukkuyum da
Gummi. Wannan ne ya sanya akasarin al’ummar wannan jiha manoma ne da makiyaya.
Galibin manoma Hausawa ne, sha’anin kiwo kuwa akasari na Fulani ne, amma dai
ana samun Hausawa mazauna ƙauyuka, har da birane waɗanda ke gwama sana’ar da suke yi da kiwon ƙananan dabbobi, har da manya. Shekaru
aru-aru, al’ummomin suna zama na lumana har ta kai auratayya ta shiga
tsakaninsu. Kasancewar haka ba ya rasa nasaba da matakan tsaro da kiyaye
zamantakewa, waɗanda shugabannin al’umma a wancan
lokaci suka ɗauka, suka kuma ɗabbaƙa. Daga cikin matakan, akwai zagayewar
garuruwa da ginin ganuwa ko garu. Haka nan akasarin garuruwan Zamfara a wancan
lokaci kusan zagaye suke da itatuwa masu ƙaya[3] kamar gumbi. Ana yin haka ne kuwa domin shiga garuruwan
ta ɓarauniyar hanya ya yi wuya. Tare da haka
ga kafi da ake yi wa garuruwa da ƙauyuka domin samun kariya daga
hare-hare. Ana kuma saka ‘yan sintiri masu sa ido da kai kawo da dare domin kiyaye
tsaro da lafiyar al’umma. A can inda aka fito, waɗannan matakai na tsaro da makamantansu, sun yi tasiri
matuƙa wajen tabbatar da tsaro na birane da ƙauyuka a Zamfara.
2.0 Yanayin Tsaro A Zamfara
Ba nufin wannan muƙala ba ne ta yi dogon
sharhi a kan dalilan rashin tsaro a Zamfara. A fili yake cewa, jihar Zamfara, a
‘yan shekarun baya- bayan nan, tana fama da
matsalolin tsaro. Da ma can, jefi-jefi, lokaci-lokaci, ana samun rashin jituwa
tsakanin manoma da makiyaya a wannan jiha. Lamarin bai yawaita, ya wuce hankali
ba, sai a ‘yan shekarun nan. Abin ya ta’azzara, ya yi nauyi sosai ta yadda har
ya wuce tsakanin manoma da makiyaya, ya shafi kowa. Munanarsa ya fara ne da ɓarnata dawa a gonakin da aka kafa a cikin
dazuzukan da a da can, aka keɓe domin kiwo.[4] Daga nan sai aka shiga satar shanu, a shiga ƙauye, a kore shanun
talakawa. Ba a ƙare shan raɗaɗin
wannan ba, sai sabgar satar mutane da karɓar kuɗin fansa mai yawa daga danginsu ta ɓulla. Wannan ya sa lamari ya ƙara munana, sai mazauna
karkara, waɗanda akasarinsu manoma,
suka kafa ƙungiyoyin
tsaro na sa kai. An fara ne da ƙungiyoyin banga a kusan kowane gari da ƙauye. ‘Yan
banga kama mai laifi suke yi, su miƙa shi ga hannun hukuma. Zargin da talakawa
suke yi wa hukuma na rashin kamanta adalci,[5] ya sa talakawa suka kafa ƙungiyar da ake kira ‘Yan
sa-kai. Ayyukan ‘yan sa-kai sun ƙara hura wutar rikicin
domin sun riƙa ɗaukar
doka a hannunsu, ta hanyar kisan ɓarayin da suka kama, ba
tare da hukuma ta yanke masu hukunci ba. Su ma al’ummar Fulani suna zargin
hukuma ba ta ɗaukar matakin da ya dace a
kan ‘yan sa-kai domin hana kisan gilla da suke yi wa waɗanda suke tuhuma.Wannan sai ya sa Fulanin
suka riƙa kai
hari a ƙauyuka,
suna kashe mutane, don ramuwar gayya da ɗaukar
fansa. Haka dai lamarin ya kasance har zuwa lokacin da gwamnati ta yi sulhu da
‘yan ta’adda.
A tunanin wannan muƙala, rashin adalci, da cin
hanci da rashawa da jahilci da yawaitar jama’a da
uwa uba matsanancin talauci, su ne suka jawo wannan matsala ta tsaro da Zamfara
ke fuskanta a yau.
3.0 Hangen Muƙala
A tunanin wannan muƙala, har kwanan gobe da jibi, matakan tsaro na gargajiya
na iya kasancewa masu matuƙar amfani wajen tabbatar da tsaro na al’umma da dukiyoyinsu, idan dai aka kafa
su, aka kuma kiyaye su sau da ƙafa. Irin matsalolin tsaro da jihar ke
fuskanta a ‘yan shekarun
baya-bayan nan, ba sa rasa nasaba da watsi da aka yi da waɗannan matakai, aka rungumi na zamani masu matuƙar tsada da wuyar aiwatarwa. Da wannan
dalili ne muƙalar ta yi ƙudurin waiwaye a kan matakan tsaro na
gargajiya da suka biya bukatun tsaro na jiya, a kuma ƙyallaro yadda za a yi amfani da su
domin magance matsalolin tsaro na wannan zamani a jihar Zamfara. Gabanin
bijirowa da waɗannan bayanai, ya dace a yi taƙaitaccen tsokaci game da muhimman
tubulan da suka kafa taken muƙalar.
4.0 Hanyar Gudanar Da Bincike
Domin tunkarar wannan bincike, muƙala ta ƙuduri anniyar bibiyar rubuce-rubucen
magabata da suka jiɓinci tsaro a gargajiya domin zaƙulo dabarun tsaro da aka kawo a
cikinsu. Haka ma za a yi hira da masana lamarin wasu sanaa’o’in gargajiya kamar
farauta da sarkanci da ‘yan tauri domin jin irin hanyoyin da suke bi da ma
magunguna da suke amfani da su domin tabbatar da tsaro. Tattare da haka za a
tattauna da waƙilan tsaro, a kuma sadu da wasu da suka
shaidi abubuwa domin tattaunawa da su duk da nufin zaƙulo sahihan bayanai dangane da wannan
batu.
5.0 Ma’anonin Tubulan Take
Domin fito da taken wannan muƙala, an yi amfani da wasu kalmomi waɗanda su ne tubula da aka yi amfani da su wajen gina taken
wannan muƙala. Tubulan ginin taken kuwa su ne,
matakan tsaro na gargajiya da kuma matsalolin tsaro. Ya dace a yi tsokaci game
da ma’anonin waɗannan kalmomi gabanin a shiga warware
zare da abawa na abin da muƙalar ta ƙuduri tattaunawa.
5.1 Matakan tsaro
A kalmomin da aka
haɗa a tubala na gina da taken muƙalar akwai, matakan da kuma tsaro.
Kalmar mataki ita ce tilo, yayin da matakai take kalmar jam’i. Idan aka haɗa kalmar da harafin nasaba na ‘n’ sai ta kasance
‘matakan’. A ma’ana kalmar tana iya ɗaukar ma’anar matsayi[6] Idan kuwa aka yi la’akari da yadda aka yi amfani da
kalmar a cikin taken muƙalar, ma’anarta na iya kasancewa shiri ko tsari
ko dabaru ko hanyoyi ko tanadi. Kalmar tsaro kuwa tana nufin kare wani abu[7] kalmar tana kuma iya ɗaukar ma’anoni kamar kiyayewa, ko kula, ko kariya, ko
fako.
A wannan muƙala, ‘matakan tsaro’ na nufin dabaru ko hanyoyi ko
tsare-tsare, ko tanade-tanaden gargajiya domin kiyaye ko tabbatar da kariya ga
rayuka da dukiyoyin al’umma.
5.2 Gargajiya
Bunza, (2006: xxvii) ya kawo asalin kalmar da cewa an
samo ta ne daga kalmar gado, aka kuma sami gadajje, ciki har da kalmar gargajiya.
A cikin Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero, an faɗa cewa kalmar gargajiya tana nufin dabi’a ko wani kaya
irin na zamanin da.[8] Idan an yi la’akari da bayanan da suka gabata, ana iya
cewa gargajiya tana nufin duk wani abu da aka gada tun kaka da kakanni. Wato
abin da ba kwaikwayon sa aka yi daga wata al’ummma ba, tun fil azal, Hausawa ne
suka ƙirƙiri abin, ba tare da sun ɗauko shi daga wasu ƙabilu ba kuma babu tasirin zamananci a cikinsa.
5.3 Matsaloli
Jam’i ne na kalmar matsala. Dangane da ma’ana kuwa kalmar
na iya ɗaukar ma’anar lalura ko uzuri.[9] Haka ma tana ɗaukar ma’anar rashin tafiyar lamari
daidai. Wato abubuwa da ke ci wa wani lamari tuwo a ƙwarya. Haka ma samun cikas ga wani
lamari, na kasancewa matsala ga wannan sabga. Duk abin da aka tsara amma ya
kasance ana samun koma baya ko tasgaro ko gurguncewa ga abin, to an sami
matsala. A wannan muƙala, matsaloli na nufin taɓarɓarewa ko cikas ko tasgaro ga lamuran
tsaro da ake samu a yanzu.
5.0 Matakan Tsaro na Gargajiya
Al’ummar Hausawa wayayyiya ce da aka san ta da tsarin
shugabancinta, da kyawawan al’adunta da suka dace da buƙatunta, da kyakkyawa da ingantattu da
kuma managartan sana’o’i daban-daban. Ta fuskar tsaro da kariya ga rayuwa da
dukiyoyin al’umma, akwai ingantancen tsari na tafiyar da tsaro wanda ya biya
bukatu tun a wancan lokaci, kuma wannan muƙala take ganin har yanzu zai iya bayar da gudunmuwa wajen
tabbatar da tsaro a wannan jiha ta Zamfara. A wannan sashe, za a yi waiwaye
game da matakan tsaro na gargajiya. Matakan tsaron gargajiya kuwa, suna iya
kasancewa nau’i biyu. Matakan tsaro na kai ko jiki, da kuma na gari.[10]
5.1 Matakan Tsaro Na Kai
Matakai ne da ɗaiɗaikun mutane suke ɗauka domin samar da kariya daga duk wani mugun nufi ko
ta’adi ko cuta da wani abokin gaba ko adawa zai iya haddasawa ga mutum. Irin waɗanan matakan kan haɗa da yin magunguna irin su basanyi, da ƙago da baduhu, da layar zana.[11] Haka ma ana cin maganin tauri don kare kai daga cutar da
za a iya wa mutum ta sara da makami.[12] Wasu mazaje har magani sukan ci, wanda ke hana bindiga
tashi ko ta kasa yi masu lahani a duk sa’ilin da aka kai masu farmaki da ita.
Wannan duk ana yi ne domin kariyar kai daga cuta, da makami ka iya yi ga jiki. Hausawa
kan ce ‘maigida takobin daga’. Wannan ya sanya ɗaukar matakan kariya bai tsaya ga kai kaɗai ba. Magidanci kan ɗauki matakai don kariya ga cutar da duk ahalin gidansa.
Wannan ne ya sanya ake yin kafi ga gidaje don kange miyagu daga samun damar
shiga gidan da nufin cutarwa. Haka manoma a ɗaiɗaikunsu kan nemi kariya ga gonakinsu da
albarkatun gona da aka samu domin hana sata ko ɓarnata kayan gonan[13]. Akan yi haka ne ta hanyar yin kafi a cikin gona, ko a
kayan gona da aka rufe a zabaro ko bushiya.
5.2 Matakan Tsaro Na Gari
Matakai ne da ake ɗauka
don kariya ga rayuka da dukiyoyi na gaba ɗaya al’ummar da suke
zaune a gari ko ƙauye ko ma tunga. Irin
waɗannan matakai ana iya
kallonsa ta ɓangare biyu. Kafin a
kafa matsuguni ko gari, ana la’akari da dacewar yanayin muhallin wurin wajen ba
da kariya daga abokan gaba. Bayan kafa gari kuma ana ɗaukar ƙarin matakai domin
kiyaye tsaron al’ummar garin. A kan haka,
muƙalar za ta kalli wannan
ta waɗannan fuskoki.
5.2.1
Dacewar Muhalli
A Bahaushiyar al’ada,
ana duba dacewar muhallin da za a kafa gari gabanin kafa shi. Addinin gargajiya
na Bahaushe shi ne bautar Iskoki da Bori. Ɗaya
daga cikin wurare da Bahaushe ke ganin matattara ce ta Iskoki shi ne tsaunuka
da duwatsu. Ba domin buƙatar kasancewa kusa ga
abin bauta[14] kaɗai ya
sa Bahaushe yake kafa gari a gindin duwatsu da tsaunuka ba. Ta fuskar tsaro ma,
irin wannan muhalli ya kasance mai biyan buƙatu na tsaro ga mazauna
gari. Wannan ba ya rasa nasaba da kasancewar irin wannan wuri mai wuyar ratsawa.
Ko baya ga haka, tsaunin ko dutsin na bayar da dama ga mutanen da ke zaune a
wurin su riƙa hawa domin hango ko
akwai mahara ko abokan gaba.[15] Galibi, ana kuma kafa
garuruwa a gaɓar koguna da gulabe ba
domin samun sauƙin ruwa kawai ba. Waɗannan
gulabe da rafuka ko ƙoramu da ma fadamu na
taka rawa sosai wajen ba da kariya ta tsaro ga mazauna wurin.[16]
5.2.2 Matakan Tsaro Bayan
Kafa Gari
Kiyayewa da dacewar muhalli da aka kawo a
sama kaɗai, ba ya wadatarwa wajen
dukkan buƙatun tsaro
a gari ko matsuguni. Bayan an zauna, an natsu, fafutukar neman abinci da abin
biyan buƙatun
rayuwa ta kankama, wajibi ne a Bahaushiyar al’ada,
mahukunta su ɗauki ƙarin wasu matakan tsaro da
za su ƙara
taimakawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin talakawa da ke ƙarƙashinsu. Waɗannan ƙarin matakai na tsaro da akan ɗauka kan haɗa da zagaye birni ko gari da ginin ganuwa ko
garu ko badala, da tsara shiyoyi ko unguwanni bisa tsarin la’akari da masu
aiwatar da sana’o’in gargajiya, ya kasance kowace sana’a, a keɓe masu aiwatar da ita don su zauna wuri ɗaya, da yi wa gari kafi domin neman tsari da
jawo bunƙasarsa
ta fuskar yawaitar jama’a da ƙaruwar arziki da wadata ga al’umma. Ana kuma
kafa dakarun tsaro da ‘yan sintiri, da ma naɗa ƙananan sarautu na bayi da na ‘ya’yan sarauta,
waɗanda za su taimaka wajen
tabbatar da tsaro. Tare da haka, ga kuma shimfiɗa mulki a bisa tafarki na gaskiya da adalci. A
yanzu ya dace a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi bayani a kansu.
5.2.2.1 Gina Ganuwa
Smith, (1987:101) ya kawo bayanin cewa birane
da akasarin garuruwa na ƙasar Hausa zagaye suke da ganuwa ko garu ko
badala tun ma gabanin kafa dauloli a ƙasar. Ana gina wannan ganuwa ne domin a samar
da kariya da tsaro a garuruwan da ma birane. A waɗansu birane kamar Kano da Katsina ga misali,
har yanzu ana samun sauran ginin ganuwa a tsaye, ko ɓirshinta. A Surame[17] ga misali, duk da tsawon lokaci ko daɗewar da birnin ya yi a matsayin cibiyar
daular Kabi[18], da kasancewar wurin kufai, har yanzu ana
iya ganin alamu na rusasshen ginin ganuwar birnin. A kowace ganuwa ko badala,
ana barin ƙofofi
da ake saka wa ƙyamare. Ƙofofin kan kasance ƙarƙashin kulawar wasu keɓaɓɓun
mutane da aikinsu shi ne buɗewa ko rufe su, safe da
yamma. Akan haƙa wani babban rami a bayan ganuwar daga waje.
Ƙetare
wannan rami yana da matuƙara wahala, balantana a kai ga ganuwar, wadda
haura ta ba zai yiwu ba saboda tsayinta. A wasu manyan birane, yayin katangance
gari da ganuwa, akan bar fili mai yawa domin noma. Hakan yana bayar da dama,
yadda zai kasance ko da abokan gaba sun kawo hari, suka yi wa gari ƙawanya na matsakaicin
lokaci, ana iya samu a noma abinci da gwargwado zai iya wadatar al’umma na wani
lokaci.[19]
A daular Zamfara, Nadama (1977:31-32) ya
labarta cewa, a wasu garuruwa, ana shuka itatuwa masu ƙaya kamar gumbi da ɗunɗu, ta
yadda za su yi surƙuƙin ƙunci mai kauri. Wannan, ingantacciyar dabara
kan hana mahara da duk wani abokin gaba samun damar shiga garin cikin sauƙi. A garin Gummi misali, an
sare ƙuncin
da ya kusan zagaye sashen gabas maso arewa na garin a wajajen shekara ta 1972. An
sare gumbin ne domin buƙatar da ake da ita na faɗaɗa gari
a wannan ɓangare, ganin cewa
gine-gine tuni har sun fara tsallaka wajen ƙuncin.
5.2.2.2 Yi wa Gari Kafi
A gargajiyance, magabata sukan yi wa gida ko
gona ko gari kafi ta hanyar amfani da magungunan tsafi. Ana yin haka ne domin a
kange mugwayen mutane da mahara shiga garin. Wani lokaci idan mugu ya tunkari
gona ko gida ko gari da niyar aibatawa ko cutarwa, hanya takan ɓace masa ko makuwa (ɗemuwa) ta kama shi, ya kasa gane hanyar zuwa
garin. A cewar Soba, (2017:201) idan aka yi wa gari ko gida ko mata kafi, da
zarar mugu ya zo wurin da niyar cutarwa, ba abin da zai gani sai ruwa ko
falalin dutsi. Ba domin wannan dalili kaɗai ake
yi wa gari kafi ba, ana kuma yin haka domin jawo albarka da wadata a gari.[20] Hanyoyin yi wa gari kafi ya haɗa da saka magungunan tsafi, ko rubuta hatimai
waɗanda za a haƙa rami a bisne, bayan an
saka su wata tukunya ko kasko.
5.2.2.3 Bukukuwa da
Siddabaru da Tsafi
Ire-iren waɗannan bukukwa ya haɗa da buɗin
daji da ɗaurin daji da gyaran ruwa. Ɗaurin daji biki ne na ‘yan
bori da ake gudanarwa ta hanyar tsafi domin gano abin da shekara mai zuwa za ta
zo da shi. Alherin da ke cikin ta da kuma abubuwa marasa daɗi da za su faru a shekara, duk za a iya hango
su domin ɗaukar matakin magance su.. Ɗaurin daji, kuwa ana
aiwatar da shi ne domin a ɗaure bakin duk wani ƙwaro ko wata dabba da ka
iya cutar da mutane yayin da aka shiga jeji, da nufin yin farauta. Wato ya
kasance a shiga jeji lafiya, a kuma fito lafiya. Galibi mafarauta ne suka fi
aiwatar da waɗannan bukukuwa biyu don ɗaukar matakan tsaro da kariya. A ɓangaren Sarkawa kuwa, suna gudanar da
bukukuwan al’ada irin su bikin gyaran ruwa da ɗaurin ruwa. Gyaran ruwa ana yin sa ne da
nufin gyara ruwa na cikowa da ambaliya da ke tafe, da kuma hana Iskokin da ke
tare da ruwan, cuta wa mutane. Ɗaurin ruwa ana yin sa domin a ɗaure bakin duk wata dabbar ruwa kamar kada da
dorina da kuma Iskokin ruwa kamar Jittakuku da Harakwai da Tamashaya, da nufin
hana su cutarwa; yadda za a shiga ruwa lafiya a kuma take lafiya.[21] Ana iya yin shashatau da saka wa mugu ɗimuwa a jeji ko hana abokin gaba shan ruwa.
5.2.2.4 Tsara Unguwanni ta La’akari
da Sana’a
Wani matakin tsaro na Bahaushe a gargajiyance
shi ne tsara shiyoyi da unguwanni a gari ta hanyar la’akari da sana’ar da
al’umma take aiwatarwa. Aba ne mai sauƙi ka ji sunayen unguwanni a garuruwan Hausawa
kamar Unguwar Malamai, Marina ko Kan Karofi, ko Majema, da Dukawa da shiyar
Masunta ko Sarkawa, da unguwar Runji, da dai sauransu. A kowace unguwa akan
sami jagora ko shugaba na masu wannan sana’a, wanda zai jiɓinci al’amuran wannan unguwa. Daga cikin
ayyukan shugabannin sana’o’i, akwai kiyaye tsaro a tsakanin al’ummarsu. Suna
kuma bayar da gagarumar gudunmuwa wajen yaƙi, ta hanyar amfani da laƙunƙuna da asirai irin na sana’rsu.
Jagoran Sarkawa (Sarkin ruwa) ga misali, yana iya hana abokan gaba shan ruwa,
ko idan sun shiga kogi, ya sa dabbobi ko Iskokin ruwa su yi masu lahani. Idan
wani baƙo ya
zo, yakan zauna ne a unguwar da masu irin sana’arsa suke zaune. Su za su saka ido
ga duk halayensa da ɗabi’unsa kyawawa ne ko
miyagu. Idan an yaba da kirkinsa, nan take sai ya saje da su. Idan kuwa mugu
ne, sai a yi maganinsa tun nan, ta yadda ba sai ya aibata wa gari duka ba.
Lallai nan gaba idan hukuma za ta faɗaɗa gari ta hanyar fitar da sababbin unguwanni,
ta riƙa
kulawa da irin wannan tsarin.
5.2.2.5 Ƙarfafa Wasannin jaruntaka
Tsakanin Matasa
Shugabanni a masarauta sukan shirya ko bayar
da goyon baya ga matasa ta fuskar wasanni da ayyukan motsa jiki irin na
gargajiya. Wannan yana ba da kafa ga samari su motsa jiki sosai, su kuma koyi
jarunta don kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana. Irin waɗannan wasanni sun haɗa da dambe tsakanin masu sana’ar fawa, da
kokawa. Haka ma a Zamfara, akwai wasan baura, wanda ya yi fice sosai a tsakanin
matasan da suka ci tauri. Akwai kuma wasannin kalankuwa da akan shirya bayan an
kakace. Ba wasannin kaɗai ba, sana’ar farauta da
ake fita jeji domin kambaɗar dabbobin dawa, wata kafa
ce ta koyon juriya da jaruntaka. Wasan tauri, wasa ne da mutane ke wasa da wuƙaƙe da sauran makamai, ana
yankawa a wuya da sauran sassan jiki, tare da kakkarya ƙarfe cikin sauƙi. Wasan shahararre ne a
Zamfara[22] da sauran sassan ƙasar Hausa. Duk waɗannan wasanni, suna taimakawa matuƙa wajen tayar da tsikar
jiki da jan hankalin matasa su shiga sabgar, ta kuma motsa jikn matasa da
sauran al’umma. Wannan zai saka masu kuzari da karsashi sosai ta yadda za su
iya tunkarar kowane irin artabu da karafkiya domin kare gari daga mahara da
mayaƙa.
Daga cikin irin waɗannan mutane ne ake samun
gwaraza da suka shahara a yaƙi.[23] Yana da matuƙar muhimmanci hukuma ta
farfaɗo ayyukan Ma’aikatar
Wasanni ta Matasa tare ƙara zaburar wasu wasanni na gargajiya domin
gujewa salwanta da cusa karkasashi da kuzari a tsakanin matasa.
5.2.2.6 Kafa Sarautu da
Suka Jiɓinci Tsaro
A kowace masarauta ta ƙasar Hausa, ana naɗa sarautu daban-daban domin kiyayewa da
tsaro. Akwai sarautu na fada waɗanda aikinsu shi ne kiyaye
tsaro a fadar sarki. Ire-iren waɗannan sarauta na cikin fada
ya haɗa da Sarkin dogarai da Shamaki
da Barga, wanda aikinsa ne ya kula da bargar Sarki. Ana amfani da dawaki domin
hawansu zuwa yaƙi. Ana kuwa yaƙe-yaƙe ne don kare mutuncin ƙasa da kiyaye dukiya da
zama lafiya ga al’umma, tare da ƙara faɗaɗa
yankin riƙo.
Hakan yana kawo bunƙasar ƙasa ta fannin yawaitar jama’a da za su
kasance ƙarƙashin ikon masarauta. Akwai
ƙarin
wasu muhimman sarautu kamar Sarkin yaƙi da Barade da Ubandawaki, waɗanda su suke jagorantar yaƙi, idan ya samu.[24] Akwai sarautar Sarkin karma ko Karma wanda
shi ke jagorantar ‘yan tauri, waɗanda galibi su ne dakarun
yaƙi na ƙasa (waɗanda ba saman dawaki suke ba) Akwai Sarkin
kofa wanda ke kula da ƙofofin ganuwar gari, ga kuma Sarkin baƙi wanda shi ke saukar da baƙi waɗanda ba na nauyi ba. Aikin Maidaji ko Sarkin
daji shi ne kula da dazuka da albarkatunsu. Duk waɗannan ana yi ne domin kiyaye tsaro a gari.
5.2.2.7 Tanadar Makamai na
Yaƙi
A bisa al’ada Hausawa a ɗaiɗaiku
da kuma matakin masarautu, sukan tanadi makamai don kare kai da kuma yaƙi, idan ya kama. Daga cikin
makamai da ake tanada, akwai na ƙarfe waɗanda
maƙera
suke samar da su. Misalinsu ya haɗa da wuƙa da adda da takobi da
gariyo da barandami da mashi da zago da zamai, waɗanda sara da sukar abokin gaba ake yi da su.
Ana kuma tanadar majajjawa da kibau, tare da kwari da baka, har ma da bindiga,
waɗanda harba su ake yi. Haka
ma akan tanadi sulke da garkuwa domin kariya. Ana kuma tanadar dafi da ake
sakawa a jikin makamai ta yadda dafin zai ƙara kassara da lahanta wanda aka sara da su.
Kowace masarauta tana tanadar barga mai tarin dawaki, waɗanda da su ake zuwa fagen fama. Duk akan
tanadi waɗannan ne domin tsaron ƙasa. Hukuma ta ƙarfafa wa maƙera guiwa domin samar da
makamai na cikin gida ba kawai dogaro da makaman waje ba.
5.2.2.8 Samar da Tsarin
Sasantawa da Yin Hukunci
Shimfiɗa
al’adaci ga mabiya, wani babban sinadari ne na kawo zaman lafiya tsakanin
al’umma. Fahintar hakan ya sa a tsarin zamantakewa na Hausawa, akwai tanadi na
sasantawa tsakanin mutane. Idan aka yi sulhu ko jan hankali, amma bijerewa ta
biyo baya, sai a yi wa wanda ya bijire hukunci irin na ba sani ba sabo. Wannan
yana cusa shakku da tsoratarwa ga duk wani mai son tayar da zaune tsaye a cikin
al’umma. Wajibi hukuma ta tabbatar da bin wannan domin rashin aiwatar da
hukunci na ‘ba sani, ba sabo’ ga mai laifi yana haifar da matsaloli ciki har da
bijirewa da ɗaukar doka a hannu.
5.2.2.9 Samar da Hurumi da
Burtali
A al’ummar ƙasar Hausa, kiwo yana ɗaya daga cikin sana’o’in gargajiya. Hausawa
sukan kiwata ƙananan dabbobi kamar awaki da tumaki, waɗanda ake yankawa domin samar da naman ci, da
kuma biyan wasu buƙatu na addini kamar tsafi a can da, da kuma
layya da suna a yanzu. Haka ma talakawa sukan mallaki jakuna da raƙuma domin ayyukan yau da
kullum na sufuri da aikin gona. Yanzu har shanu Hausawa sukan kiwata a ƙauyuka da garuruwa da ma
birane. Saboda samar da filin da waɗannan
dabbobi za su yi kiwo, akan keɓe hurumi.[25] Samar da wannan fili ya taimaka wajen hana ƙananan dabbobi shiga gonaki
wajen ɓata shuka. Da dama a wasu
lokuta, ɓarnar da dabbobi ke yi a
gonaki kan kasance matsala a zamantakewar mutane. Fulani su ne abokan zaman
Hausawa kuma babbar sana’arsu ita ce kiwo musamman na manyan dabbobi kamar
shanu. A yunƙurin kauce wa tashin-tashina da tayar da
zaune tsaye tsakanin manoma da makiyaya, kowace masarauta ana keɓe burtali. Burtali shi ne filin da aka
tanada, wanda ba a noma cikinsa. An keɓe shi
ne kawai domin kiwo, da kuma samar da hanyoyi domin shawagin dabbobi ko dai
yayin da za su je kiwo ko shan ruwa a mashaya. Ɗaukar wannan mataki ya
taimaka matuƙa wajen kiyaye faɗace-faɗace a
tsakanin manoma da makiyaya a wancan lokaci.
6.0 Amfani da Matakan
Gargajiya na Tsaro don Magance Matsalolin Yanzu
Bahaushe na cewa ‘Da tsohuwar zuma ake magani’
kuma ba mamaki, tunanin muƙalar shi ne ‘ana
iya cin tuwon bana da miyar bara.’ A nan za a yi tsokaci ne dangane da yadda za
a yi amfani da matakan tsaro na gargajiya wajen magance matslolin tsaro da jihar
Zamfara take fuskanta a yanzu. A tunanin wannan muƙala, bin waɗannan matakai zai taimaka matuƙa wajen magance matsalolin
tsaro a Zamfara. Ga matakan kamar haka:
6.1 Komawa ga Malicci
A Bahaushiyar al’ada, idan musiba ta sami
mutane, sukan koma ne ga abubuwan bautarsu da tsafe-tsafensu domin neman
mafita. Yanzu da aka rungumi addinin Musulunci, ya dace sosai al’ummar wannan
jiha ta koma ga Ubangiji mahilicci. Kowa ya san saɓo da butulcin da yake yi wa Allah maɗaukakin Sarki. Jama’a su yi tuba zuwa ga
Allah, su kuma duƙufa wajen yin addu’o’i na
neman tsari da kariya da neman Allah ya yaye wannan matsala ta rashin tsaro a
jihar. Wannan ba wai ya tsaya kawai ga ɗaiɗaikun mutane ba, ya dace matuƙa, hukuma ko gwamnati da ma
manya da ƙananan
sarakunan jihar nan, su yi ruwa da tsaki wajen saka malamai da salihan bayi su himmatu
wajen yin addu’o’i na neman Allah ya kawo ƙarshen wannan bala’i.[26] Tattare da gudanar da addu’o’i. Ya dace
mutane a ɗaiɗaiku su mallaki asirai waɗanda ba su saɓa wa addininsu ba. Asirai irin na kariya daga
bindiga, da ma sauran makamai duk ana samun su. Sarakuna da hakimai da dagatai
su yi ƙoƙarin sabunta ko yi wa
garuruwa da ƙauyukansu kafi domin kariya ga al’ummarsu.
Wannan ya zamo wajibi domin ga dukkan alama, tanade-tanaden da hukumomin tsaro
na ƙasar
nan suke yi ba ya wadatar da buƙatun tsaro na yanzu.
6.2 Shimfiɗa Mulkin Adalci
Hukuma ta riƙa kamanta adalci, a
tabbatar da zartar da hukunci ga duk wanda ya taka doka. Wato ya kasance ana
zartar da hukunci ba tare da nuna bambancin siyasa ko addini ko yanki da mutum
ya fito ba. Yin haka yana sa mutane su shiga taitayinsu kuma su guji aikata
laifi. Shehu Usmanu Ɗanfidiyo, a ruwaitowar Bunza, (2019)[27] yana cewa:
“ Ɗaya daga cikin guguwar musibar da ke ruguza daula (gwamnati)
ita ce,
fifitar da wata ƙabila
bisa wata ko a nuna son kai (alfarma) ga wasu sashen
mutane
koma bayan wasu.”
A wani
wurin, Shehu Ɗanfodiyo, ruwaitowar Bunza (2019: 133)
Ya ce:
“Cin
nasarar kowane irin al’amari yana cikin adalci, rushewar sa da kasawarsa, yana cikin rashin
adalci.”
Ƙari bisa ga haka, Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello yana cewa:
“Ainihin tushen zaman lafiya a
duniyar mutane shi ne adalci”[28]
Wannan ya nuna
cewa baya ga kawo zaman lafiya a ƙasa, kamanta adalci yana kuma
tabbatar da ɗorewar mulki a kowace daula, ko da
dular kafira ce. A kan haka ya zama wajibi ga hukuma ta tabbata ana shimfiɗa adalci a tsakanin al’umma. Lallai Sarakuna manya
da ƙanan su himmatu wajen kare al’umma
da suke ƙarƙashin ikonsu. Irin yadda tsohon ministan tsaro na
Nijeriya, Janar Mansur Ɗan’ali murabus, ya fito fili ya faɗa cewa, wasu daga cikin Sarakunan jihar suna da hannu cikin
wannan badaƙala ta rashin zama lafiya, abin kunya
ne. Mahukunta su tuna cewa, talakawa da suke jagoranta amana ce
a wurinsu. Su tamfar makiyaya ne kuma haƙiƙa, Allah zai tambaye su kan abin
da ya ba su kiwo.
6.3 Gina Ganuwa ko katanga
Gina katanga ko wani shinge domin kariya ga gari ko ƙasa, wata daɗaɗɗiyar dabara ce ta kawo tsaro a gari ko ƙasa. Har yanzu wannan dabara idan an yi
amfani da ita, tana iya magance matsalar tsaro a yanzu.[29] A ƙauyuka da ake samun yawan hare-hare na ‘yan bindiga da masu satar mutane don
karɓar kuɗin fansa, ana iya amfani da wannan dabara. Idan kuma ana
tunanin yawan kuɗin da aikin zai ci, ana iya dabarar
kewaye ƙauyuka da shinge na itatuwa masu ƙaya, kamar gumbi. Wannan zai rage yawan
hanyoyi ko kafofi barkatai da za a iya shiga ƙauye cikin sauƙi. Ai da can wasu garuruwan Zamfara
zagaye suke da irin wannan shinge. Ko ba komai, yin haka zai ƙawata muhalli kasancewarsa kure shar,
ga kuma furanni kyawawa. Fargabar da ake da ita, na barazana dar muhalli ke
fuskanta, dalilin gurgusowar hamada, za ta ragu sosai idan aka yi haka. Yekuwar
da ake ta yi ta mutane su dasa itatuwa, zai daɗa bunƙasa.
6.4 Samar Da Makiyaya da Burtali
Sakamakon yawaitar al’umma ya wanzar da buƙatar ƙara faɗaɗa gonakin noma a mafi yawan garuruwa na
wannan jiha. Wannan ya haddasa mayar da hurumi da makiyaya da burtali gonaki.
Hakan ya sa makiyaya ba su da wadataccen filin da dabbobinsu za su yi kiwo.
Hanyoyin da suke bi a cikin karkara domin zuwa kiwo yanzu yawanci duk an mayar
da su gonaki. Samar da hurumi a bakin gari da
makiyaya a jeji domin kiwon dabbobi, da keɓe burtali domin samar da hanyoyin wucewa ga
dabbobi, ko dai zuwa kiwo ko zuwa rafi domin shan ruwa, abu ne mai matuƙar muhimmanci. Yin haka
wani babban mataki ne na tabbbatar da tsaro a ƙasa domin yana rage yawan
faɗace-faɗace da ke wanzuwa tsakanin manoma da
makiyaya.
6.5 Samar wa Matasa Aikin
yi
Lallai ne hukuma ta tashi tsaye wajen samar
wa da matasa aikin yi. Zaman kashe wando da matasa ke yi yanzu, ba zai haifa wa
wannan jiha ɗa mai ido ba. Zaman banza
da rashin aikin yi kan sa matasa shiga aikin bangar siyasa. Hukuma ta fito da
wani shiri na saka matasa su shiga aikin noma gadan-gadan. Haɗawa da kiyo musamman na kaji da kifi, zai
tabbatar da ƙarin tsaro ta fuskar kore yunwa, ga kuma uwa
uba, gusar da talauci. Yin haka zai kange su daga shiga cikin ayyukan
ta’addanci da sace-sace.
6.6 Hana shaye-shayen Kayan
Maye
Lamarin shan miyagun ƙwayoyin da kayayyaki masu
sa maye ya ta’azzara matuƙa a tsakanin matasa. Wannan
ɗabi’a ta shan maye, ba ta
tsaya ga samari kawai ba. A halin yanzu, ‘yan mata budare, kai har ma da matan
aure, ba a bar a baya ba wajen shaye-shaye. Shan kodin da sauran magungunan
cutar mura na ruwa ba, a yanzu, ya kasance yayi ko wata sabuwar sabga a
tsakanin matasa. Wannan barazana ce mai yawa ga sha’anin tsaro a zamanin nan na
yanzu.
6.7 Cusa Kishin Ƙasa a Zukatan Mutane
A halin yanzu, gaskiya kishin ƙasa ya ƙaranta a tsakanin mutane.
Akasarin mutane ba kasafai suke sadaukar da kawonansu ga sha’anin kariyar ƙasa ko al’umma
ba musamman idan aka kwatanta da zamanin da. Dubi irin yadda ‘yan tauri suke
alfahari da sarakunansu a yayin da suke kirari bayan da makaɗansu suka tsima su. Haka ma sukan nuna cewa
ba batun yin raki ko guduwa yayin ta ɓaci,
aka tsunduma fagen daga.[30]
6.7 Saka Masana Asiran
Gargajiya Aikin Kula Da Tsaro
Hukuma ta ɗauki matasa masu gaskiya, waɗanda suka mallaki asira na gargajiyai, a saka
su aikin banga. A ƙarfafa masu guiwa sosai ta yadda za su sami
damar yin sintiri domin sa ido a kowane saƙo da lungu na jiha. Lallai ne a cire son kai
wajen zaɓen ‘yan banga. Kada ya
zamana kasancewa ɗan ta’adda ko ɗan bangar siyasa shi ne mizani ko ma’auni na ɗaukar matasa aikin banga. Idan da hali, a
fito da wani tsari na ‘yan sintiri shigen wanda ƙasashen Yarbawa suka ƙirƙira a kwanakin nan, wato ‘Amotekun’.
Dalili kuwa shi ne ‘yan ƙasa su ne suka san lungu da saƙo na jiha kuma su suka san
takun masu aikata miyagun laifuka fiye da ‘Yan sanda. Yana da kyau a aiwatar da hakan
domin a sami tabbatacce kuma ingantaccen tsaro mai ɗorewa a jiha.[31]
7.0 Sakamakon Bincike
Al’ummar Hausawa wayayyiyar al’umma ce tun gabanin
saduwarta da kowace al’umma, walau daga gabas ko yammacin duniya. Tana da tsari
na sarautu wanda wani muhimmin mataki ne na samar da tsaron rayuka da dukiyoyin
al’umma. Wannan muƙala ta yi ƙoƙarin yin waiwaye, da nufin zaƙulo daɗaɗɗun hanyoyi da matakan tsaron da
Bahaushe ya gada kaka da kakanni. Bayan bijirowa da matakan, an tattauna a kan
yadda za a yi amfani da waɗannan tsofaffin matakai, domin yin
amfani da su a magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a yanzu. Matsalolin
tsaro da ake fuskanta a yanzu, sun yi kusan yin canjaras da irin waɗanda aka fuskanta a can inda aka fito. Kai wa gari hari,
da satar mutane don bautar da su, da sace-sace, da ciren mata da fashi da
makami, da ma can, daɗaɗɗun laifuka ne da akan aikata. Kafa
daular musulunci ta Sakkwato ya sa aka sami sauƙinsu, sakamakon adalcin da shugabanni
suka shimfiɗa. Tun da a yanzu matsalolin tsaron sun
yi waiwayen baya, tunaninmu shi ne a yi waiwayen baya wajen ɗaukar matakan tsaro na gargajiya domin magance su.
Kammalawa
A Bahaushiyar al’ada akwai ƙwaƙƙwaran matakai da ake ɗauka domin tabbatar da tsaron al’umma.
Matakan sun haɗa da waɗanda mutane suke ɗauka a ɗaiɗaikunsu, domin kare lafiyar su da iyalansu,
har da dukiyoyinsu. Irin waɗannan matakan sun haɗa mallakar magungunan tsafi kamar basanyi da
sagau (Ƙago)
da layar zana da baduhu domin ɓacewa a duk lokacin da aka
fuskanci barazanar da za ta kai ga munana wa lafiyar jiki ko ta dukiya. Haka ma
ana yi wa gida ko gonaki kafi, domin samun kariya daga mtsalar kutse da sata. A
gari baki ɗaya, mahukunta kan ɗauki matakai na tsaro domin kariya ga gari da
al’umma baki ɗaya. A da can, akan zagaye
garuruwa da ginin ganuwa, da rami mai zurfi daga waje. Ana kafa ƙofofi, a kuma saka masu
kula da rufe su, idan yamma ta yi. Akwai sarautu daban-daban da akan naɗa, waɗanda
aikinsu yana da nasaba da tsaro. Daga ciki, akwai Sarkin yaƙi, da Barade da Ubandawaki
da Zarumi da Karma da Sarkin baka da dai sauransu. Sarautu na sana’a ba akan
bar su a baya ba wajen bayar da gudunmuwa ga sha’anin tsaro a masarauta.
Shawarwari dangane da yadda za a yi amfani da
matakan tsaron nan na gargajiya wajen magance lamarin tsaro a yanzu sun bijiro
a cikin wannan muƙala. A tunanin muƙalar, har yanzu ana iya
amfani da dabarar zagaye gari da katanga domin kange ‘yan ta’adda
daga samun sauƙin yin kutse, da nufin kai hari na ta’addanci.
Wasu garuruwa na Zamfara a can da, an zagaye su ne surƙuƙin itatuwa masu ƙaya, irin gumbi. Haka dai
waɗannan matakan suke. A jiya,
sun biya buƙatunmu na tsaro kuma ko yau, amfani da su zai
sa mu kai gaci, a sha’anin tsaro.
Ƙarshe, muƙalar ta fito da shawarwari
dangane da yadda za a yi amfani da tsofaffin matakan tsaro na gargajiya domin a
sami ƙwaƙƙwaran zama lafiya mai ɗorewa. Lalle
a tashi tsaye, a duƙufa wajen addu’o’i na
neman zaman lafiya. Wajibi ne a yi tsaye, a samar wa matasa aikin yi domin
maganin zaman kashe wando. A ƙara kyautata yadda ake ɗaukar ‘yan banga. Kada ya kasance mizanin ɗaukarsu shi ne zama ɗan kuwar siyasa, ko ɗan sara- suka ko saka hannu a ta’addanci
siyasa. Akwai maharba da ‘yan tauri, waɗanda
suka mallaki asirai, kuma suka san su. Ire-irensu ya dace a danƙa wa lamarin sintiri a
dazuka, da ƙauyukan wannan jiha domin maganin tsaro da
kawo rahoto ga hukuma. Waɗannan, da ma wasu
ashawarwari da aka kawo, za su taimaka gaya wajen magance matsalolin tsaro na
yau a jihar Zamfara.
MANAZARTA
Abbas, H. (2013).
“Taɓarɓarewar Tsaro A Nijeriya da Hanyoyin
Magance Ta a Gargajiyance” Muƙala da
aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na biyar. Tsangayar Harsuna, Kwalejin Ilmi ta Tarayya, Zariya ta
shirya.
Abdullahi, S.
(1987). A Little New Light: Selected
Historical Writings of Professor Abdullahi smith. The Abdullahi Smith Centre
for Historical Research, Zaria, Nigeria.
Achi, B. (1984).
“The Development and Functions of City Walls in
the Savannah Belt Area of Nigeria.” M.A. Thesis, Ahmadu Bello University.
Adamu, M. (1978). The
Hausa Factor in West African History Ahmadu Bello University Press.
Alkali, M.B. (1969) ”A Hausa Community
in Crisis: Kebbi in the Nineteenth Century.” M.A. Thesis, Department
of History, Ahmadu Bello University.
Augi, A.R. (1984). “The Gobir Factor in the Soccial and Political History of
the Rima Basin, C.1650 – 1808 A.D.” Ph.D. Thesis, Department of History, Ahmadu Bello University.
Bargery, G.P.
(1934). A Hausa – English Dictionary and
English – Hausa Vocabulary Oxford University Press,
Bunza, A.M. (1989). “Hayaƙi Fid Da Na Kogo (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)” Kundin Digiri
na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M. (1995). “ Magungunan Hausa A Rubuce: Nazarin Ayyukan Malaman
Tsibbu.” Kundin Digiri na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M. (2006).
Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Wallafar Maɗaba’ar Tiwal Nigeria, Ltd.
Bunza, A.M. (2019). “Zama Lafiya Ya Fi Zama Ɗan Sarki: Shirin Tunkarar Zaɓen 2015 a Nijeriya”Takardar da aka a taron ƙara wa juna sani kan kyautata zaman lafiya
a zaɓen da za a gudanar a shekarar 2015. Shiryawar Ƙungiyar Orphans and Huffaz Educational
foundation, Birnin Kebbi,
Nijeriya.
Bunza, A.M. (2015).
“Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato.( Abin Koyi ga Shugabannin Zamaninmu)” Cikin
Dunfawa, A.A. (Ed) Jagora Ga Matasa A
cikin Karantarwar Shugabannin
Daular Usumaniyya Cibiyar Hidimar Rubuce-Rubucen Shugabannin Daular Usmaniyya.
Bunza, A.M. (2016).
“Ƙunar Baƙin Wake: Ƙalubalen Tsaron Ƙarninmu (Duba Cikin Tunanin Bahaushe Abin da ya koro ɓera.....” Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, a Tsangayar Fasaha da nazarin Addinin
Musulunci, jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, ranar Talata, 1ga watan Maris zuwa 3 ga Maris, 2016.
CNHN (2006) Ƙamusun Hausa Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Nigeria.
Francic, D.J.
(2006). “Peace and Conflict Studies: An Overview of Basic Concepts” in
Shedrack, G.B. (ed) Introduction to Peace and Conflict Studies
in West Africa Spectrum Books Ltd.
Gusau, S.M. (2009).
Diwanin Waƙoƙin Baka. Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa Century
Research and Publishing Ltd.
Lugga, S.A. (2007).
Conflict and Security Management: A
Traditional Approach to Security and Conflict Management in Hausaland, Nigeria.
Lugga Press, Gidan Lugga, Ƙofar Marusa Road, Ƙatsina.
Nadama, G. (1977).
“The Rise and Collapse of A Hausa State: A Social and Political History Of Zamfara.” Kundin Digiri na Uku, Sashen
Tarihi, Jami’ar Ahmadu Bello.
Sarkin Gulbi, A.
(2015) ‘Traditional Title Holders As Ambassadors of Peace in maraɗi Region’Maraɗi: Muƙalar da aka gabatar a Taron Ƙawa wa Juna Sani Na Ƙasa da Ƙasa ( Maraɗi Kwalliya),
Daga 14-16 Disamda, 2015.
Shehu, M. (2008).
“Zama Lafiya Ya Fi Zama Ɗan Sarki: Tunanin Bahaushe A kan Zaman
Lafiya Da Sasantawa” Kundin Digiri
Na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Soba, A.S. (2017).
“Tanadin Tsaron Gargajiya A Ƙasar Zazzau (Waiwaye Cikin Zamunnan
Sarakunan Haɓe 1435 – 1804)” Kundin Digiri na Uku, Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
[1] Duba Nadama, G. (1977) ‘ The Rise and Collapse of a Hausa State: A Social
and Political History of Zamfara’ Kundin Digiri na Uku, Sashen Tarihi, Jami’ar
Ahmadu Bello Zaria. Nigeria.
[2] Daidai da tushen bayani na 1, shafi na 1.
[3] Daidai da Tushen bayani na 1 amma shafi na 31- 32.
[4] Tun farko, a wajajen 2010/2011 makiyaya suka riƙa shiga gonaki, suka riƙa saran dawa da aka
shuka daidai lokacin da ta fitar da kai, tana dab da nuna. Duk gonar da suka
sare dawar, sai su saka shanunsu ciki ta yadda za su cinye kararen dawar sarai.
A wannan lokaci, abin ya fi tsanani a ƙaramar Hukumar
Mulki ta Anka.
[5] Kowane ɓangare na al’ummar da rikicin ya shafa tun daga farko, wato manoma da
makiyaya, suna zargin hukuma tana yi masu rashin adalci da rashin ɗaukar mataki a kan
masu laifi. Manoma suna zargin idana aka yi masu ɓarna a gona, a
faye bi masu kadin haƙƙinsu ba. Makiyaya a ɗaya ɓangaren kuma suna
zargin cewa, idan ‘Yan sa-kai suka kai masu farmaki a rugagensu, hukuma ba ta
bi masu kadinsu. Wannan sai ya sa kowane ɓangare ya riƙa daukar doka a hannunsa ta hanyar yanke wa kansa hukuncin zartar da duk
abin da suka ga dama.
[6] CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Shafi na 338
[7] Daidai da tushen bayani na 4 amma shafi na 452, ƙarƙashin kalmar ‘tsara’.
[8] Daidai da tushen bayani na 5 amma shafi na 159.
[9] Daidai da tushen bayani na 6, shafi na 340.
[10] Duba Sarkin Gulbi, A. ‘Dabarun Tsaro A Ƙasar Hausa: Bin Diddiginsu A
Masarautar Gummi’ A Cikin The Hausa People, Language
and History. Past, Present, and Future. Malumfashi, A.M.I. da wasu (2016)
Garkuwa Publishing, Ltd. Shafi na 372.
[11] Domin ƙarin bayani a kan waɗannan magunguna,
duba Bunza, A.M. (1990 )”Hayaƙi Fid da Na Kogo”: (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa). Kundin Digirin
M.A., Jami’ar Bayero, Kano.
[12] Ƙasar Gummi ta yi fice sosai wajen yawaitar ‘yan tauri. Ko baya ga dalili na farauta, samun mutane
masu yawan gaske da suka ci maganin tauri a wannan yanki na Zamfara, ba ya rasa
nasaba da irin barazanar da manoman ƙwarya suka riƙa fuskanta daga makiyaya. A wancan lokaci, ƙwaryar da akan shuka a bayen gulbi da fadamu kan kai har
zuwa kokacin da ruwan shuka kan sauka, ba tare da gonar ta tashi ba. Makiyaya a
irin wannan lokaci sukan suƙunci fadamu da
bayen gulbi domin nan ne kaɗai sauran wurin da ya rage, inda
dabbobi za su iya samun koriyar ciyawa. Wani lokaci dabbobi kan shiga gonakin ƙwarya su yi ɓarna. Idan manomi ya fusata ya yi
magana a kan rashin gaskiyar da aka yi masa, ko ya kori dabbobin daga cikin
gonarsa, sai sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da makiyayi. Fulani makiyaya koyaushe
ba ka raba su da makamai da suke yawo da su a duk inda suke. Wannan ne ya sanya
idan irin wannan jayayya ta yi tsananai, sai ta kai ga faɗace-faɗace. Idan kuwa faɗa ya ɓarke, ba abin da
Bafulatani zai yi sai kai sara da makaminsa. Kan ka ce kwabo, an yi wa manomi
saran guro (kuɓewa). Ganin yawaitar ire-iren wannan artabu da ta’addanci, manoma a yankin
Gummi suka duƙufa wajen mallakar maganin tauri da
sagau, don kare kai daga duk wani ɓacin rana, na kawo masu farmaki da
makami. Wannan ya sa duk manomin da makiyaya suka san ya ci tauri, to ko
kusantar gonarsa ba sa yi, domin sun san buwayayye ne shi.
[13] A wani labari, an ce a wani ƙauye na ƙaramar Hukumar Mulkin Bunguɗu, an yi wani
manomi da ba a ɗibar kayan gonarsa sai da izninsa. Wata rana jikansa ya ɗebo kuɓewa a gonarsa, ya
kawo gida aka yi miya, ba tare an sanar da shi ba. Gabanin a gaya masa cewa an ɗebo kuɓewarsa an yi miya,
sai wani ƙaramin yaro a gidan ya matsa kuka sai
an ba shi abinci ya ci. Sai bayan da aka ba wa yaron abincin ne, sannan aka
aika a sanar da shi cewa an ɗebo kuɓewa a gonarsa.
Kafin manzon da aka aika ya dawo; duk ɗan abincin da yaron nan ya ci sai da ya
amaye shi. Yaro kuwa ya ci gaba da amai. Ciwon ciki ya tirniƙe shi. Kan ka ce kwabo, yaro ya ce ‘ga garinku nan (ya
mutu)’.
[14] Duba Smith, A. (1987) A Little New
Light Salected Historical Writings Of Professor Abdullahi Smith The
Abdullahi Smith Centre for Historical Reseach, Zaria, Nigeria. Shafi na 101.
[15] A nan Zamfara garuruwan da aka kafa a irin wannan muhalli sun haɗa da Kanoma ta ƙaramar Hukumar Mulkin Maru. Garin kacokam a saman tsauni
yake kuma akasarin gonakinsu duk a saman wannan tsauni suke, musamman ma dai
kanoma birni. Garin Kwatarkwashi na ƙaramar Hukumar
Mulki ta Bungudu ma ai wani babban misali ne Garin Maru ma a cikin kware yake.
Ga tsaunukan Baraba da Ɓaramangu da suke dab da garin ta ɓangaren yamma.
[16] Dubi yadda Makaɗa Kara Buzu Mai Kan Kuwa, makaɗin Sarkin kabin
Argungu Sama’ila, yake cewa a wani ɗan waƙa nasa cikin Gusau, S.M. (2009:5) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa Century Research and Publishing Ltd.
Kano.
Jagora: In taƙamakku gulbi,
‘Y/Anshi: Sama ɗan Andi ga
masuntanai,
: Nitso mukai muna tsama,
:
Cewa kakai agwan kifi.
Gindin Waƙa: Tsare hwaɗa na Mainasara,
Ɗan Nagwandu ba kango.
Dubi yadda muhallan akasarin garuruwan
Zamfara suke a gaɓar gulaben da suka ratsa yankin. A gaɓar gulbin Sakkwato kaɗai akwai garuruwa
kamar Gusau da Bungudu da Maru da Maradun da Bakura. A gaɓar gulbin Zamfara
kuwa, akwai Wuya da Anka da Bukkuyum da Gummi. Garuruwan Ƙauran Namoda da Moriki suna gaɓar gulbin Gagare, yayin da Zurmi take a
gaɓar gulbin Bunsuru.
[17] Surame shi ne garin da Muhammadu Kanta ya kafa a matsayin babban birni na
daular Kabi. A yanzu, kufai na wannan birni yana nan kudu kaɗan daga garin
Binji a kan hanyar zuwa Gande.
[18] Don ƙarin bayani a kan daular Kabi, duba
Harris, P.G. (1938) ‘Sokoto Provincial Gazetter’, da Alkali, M.B. (1969) “A Hausa Community in Crisis,
Kebbi in the Nineteenth Century”. Kundin Digiri na Biyu,Sashaen Tarihi, Jami’ar
Ahmadu Bello, Zaria.
[19] Duba tushen bayani na 12, shafi na 101.
[20] Magunguna irin waɗannan na buƙatar sirri domin a bisa al’ada masu su ba za su so a bayyana su a sarari ba.
[21] Don ƙarin bayani a kan yadda ake aiwatar da
waɗannan bukukuwa a al’adance, ana iya duba Harris P.G.(1942) “The Kebbi Fishermen (Sokoto Province)” Journal
Anthropological of The Royal Anthropological Institute. PP 283-334 da
Nadama, G. (1977) “The Rise and Collapse of A Hausa State: A Social and
Political History of Zamfara” Kundin Digirin Ph.D, Sashen Tarihi, Jami’ar
Ahmadu Bello, Zaria.
[22] Abin da ke tabbatar da haka shi ne wanzuwa ko kasancewar shahararrun makaɗan tauri a
Zamfara. Misalinsu ya haɗa da Makaɗa Kassu Zurmi da
Makaɗa Garba Ɗanwasa Gummi.
[23] Dubi yadda aka nuna Muhammadu Kanta na Kabi shahararren ɗan kokawa da ya
buwaya a zamaninsa. Wannan ne ya sa ya yi fice a fagen yaƙi, ya kasance ɗaya daga cikin dakaru na daular Sanwai; kafin daga baya ya yi wa daular ta
Sanwai tawaye. Wannan ne ya ba shi damar kafa daular Kabi. Don ƙarin bayani, tarihin Kabi a cikin Harris, P.G. (1938) “Sokoto Provincial Gazatter.”
[24] Domin ƙarin bayani dangane da sarautu masu
kula da sha’anin tsaro a masarautu, duba muƙalar Sarkin gulbi, A. “Dabarun Tsaro A Ƙasar Hausa: Bin
Diddiginsu A Masarautar Gummi.” Cikin Malumfashi, I.A.M. da Wasu (2016) The Hausa People, Language And History: Past, Present And Future.
Shafi na 369-377.
[25] Wato wani yanki da aka ware ko aka keɓe a bakin gari, wanda ba a nomawa. Ana
keɓe shi ne domin kiwon dabbobin gari.
[26] A gargajiyance, idan musiba ko fitina ta riski mutane, komawa suke yi ga
abin bautarsu na Tsafi da Bori. Akan yi wa abin bauta yanke-yanke na dabbobi
manya da ƙanana, da nufin abin bauta ya taimaka a
sami sauƙin lamari. Yanzu da yake al’ummar Hausawa akasari an yi watsi da addinin gargajiya,
an rungumi na Musulunci, ya dace a yi abin da addinin Musulunci ya tanada na
komawa ga Allah ta yawan ambatonsa, da neman sauƙi daga wajensa. Allah ma ji roƙon bayinsa ne.
Dubi yadda a wani lokaci can baya,
tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, General Yakubu Gowon (murabus) ya yi
ta fafutikar, shela da ƙaddamar da shirinsa na jagorantar
al’umma wajen yi wa ƙasar Nijeriya addu’a.
[27] Duba muƙalar Bunza, A.M. (2019) “Zaman Lafiya Da Tsaro A Daular Musulunci Ta SakkwatoLAbin Koyi Ga Shugabannin Zamaninmu)”
Cikin Dunfawa, A.A. (ed)) Jagora Ga
Matasa: A Cikin Karantarawar Shugabannin Daular Usmaniyya Shafi na 121 –
145.
[28] Daidai da tushen bayani na 25, shafi na 133.
[29] A duniyar zamannmui, har yanzu ana
amfani da dabarar katangance gari ko iyakokin ƙasa don magance matsalolin tsaro. Ƙasar Amurika ga
misali, shugabanta George W. Bush, a shekarar 1990, ya umurci a kafa shinge na
tsawon mil14 tsakanin iyakar ƙasarsa da Mexico.An kammala shinge a shekara ta 1994. A watan oktoba na 2006, an sake
gina wani shingen a ɓangaren Arizona, na iyakar ƙasarsa da Mexico. A isra’ila ma, daidai shekarar
1994, an gina wata katanga tsakanin ƙasar da zirin Gaza
na Palasɗinu, da nufin daƙile yawaitar samun hare-haren Palasɗinawa ‘yan sara
suka. Wannan katanga ta kewaye gaba ɗayan iyakar ƙasar Isra’ila da zirin na Gaza, mai tsawon
kilomita 708, wato mil 440. A shekarar 2000, sakamakon wannan katanga, an sami
ragowar kai hari daga adadin da ya kai 73 zuwa 12 kacal a sheakara ta 2003.
Duba adireshin intanet https://en.m.wikipedia.org don ƙarin bayani.
[30] Dubi kirarin ɗaya daga cikin
‘Yan taurin Garba Ɗanwasa inda yake cewa:
Garba
ai nace ma takarda,
Ta hito dah hannun Abubakar ɗan Bello,
Ta
faɗa ga jami’inmu Sarkin Mafara,
Shi
kau shi biɗo malamin jimilla,
Shi
kau ya duba takarda,
Takarda
ta ce ana biɗab busasshi,
.......................................................
Garba
ka san ba batun gudu in bak ka
Garba
dur radda taɓ ɓaci ,
Niy
yi gudu nib bakka,
Garba
ko ga gangara ko ga tudu,
Rannan
ka sa a ɗebe kai a ɗebe ƙahwahu,
Hanjin
maza ka tura rame
Ƙassan maza ka ka kai wa tsohuwa ta yi
alli,
Tsuwayyan maza ka
tattala,
kai wa Maidawo yarinya,
Ka
ce mata wurin hwaɗa,
Ɗiya maza sunka gaza.
(Kirarin Namailamba, A waƙar Garba Ɗanwasa Gummi)
[31] Dubi irin yadda ake samun nasarori ta yin amfani da mafarauta da ‘yan
tauri, waɗanda aka fi sani da suna ‘civilian JTF’ a yaƙin da ake yi da ‘yan boko haram a jihohin
arewa maso gabas. A wasu lokuta, su ne suke yi wa sojoji jagora, a dajin
Sambisa, inda nan ne maɓuyar ‘yan ta’adda.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.014
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.