Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsarin Zumuntar Bahaushe Maganaɗison Tsaron Ƙasar Hausa

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Aliyu Muhammadu Bunza
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
mabunza@yahoo.com

Tsakure

A shekarun baya ƙasar Hausa tana da aminci da tsaro. Tsaron da Hausawa ke da shi na da nasaba da tsarin zumuntarsu. A baya-bayanan nan kuwa, al’amarin tsaro a ƙasar Huasa na fuskantar ƙalubalen ƙara taɓarɓarewa. Wannan takarda ta mayar da hankali wajen nazartar alaƙar da taɓarɓarewar tsaro da tsarin zumuntar Bahaushe a yau. A matsayin dabarar gudanar da bincike, an nazarci jaridu tare da bibiyar kafafen watsa labarai da na sada zumunta. Bugu da ƙari, an bi diddigin waɗansu ayyukan ta’addanci har zuwa wuraren da suka wakana domin samun bayanai daga tushe. Sakamakon binciken ya yi daidai da hasashensa inda ya bayyana akwai alaƙa ta kai tsaye da ta kaikaice tsakanin tsaro da tsarin zamantakewa. A fahimtar wannan bincike, lamarin inganta tsaro ya kasance tamkar kurar gardi. Tabbatar da tsaro da zaman lafiya na buƙatar saka hannun dukkannin ɓangarorin al’umma tun daga kan jami’an gwamnati, shuwagabanni, har zuwa kan ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun al’umma.

Gabatarwa

Hausawa sun ce; “shirin shiga ruwa tun tudu ake kimtsa shi” domin ba a fafe gora ranar tafiya. Idan an shirya wa abubuwan da ke kawo cikas ga zamantakewa tun ba su wakana ba, za a ji daɗin tunkarar su in suka fara barazana. Idan suka ayyana, za a san matakin da ya kamata a ɗauka musu. Matsalolin mutane ba sa ƙarewa, a koyaushe in an fita a wannan a faɗa wancan. Idan an magance wannan, wani sabo ya ɓullo, haka ƙasar Hausa ta yi zama, yau ciwo gobe lafiya. Gabanin zamanin gaba, lafiya lau ake, da gaba ta zo aka yi ta, kamar a yanke ƙaunar samun sarari, sai Allah Ya kawo zaman lumana. Bayan zaman lumana, sai ga yaƙe-yaƙen jihadi. Da suka kawa, Turawa suka zo da nasu salon ta’addanci. Da aka kore su, lumana ta wanzu. Ana murnar an gama da fitina sai baya ta haihu, fitinun ƙabilanci da addini da yanki da ɓangaranci da siyasa da tawaye. A ƙarnin da muke ciki ga ta’addanci ya tsayu da ƙafafunsa da makaman kashe-in-kashe. Tunanin wannan takarda Hausawa su sake bitar tsarin zumuntarsu domin wasu su yi koyi da su, zaman lafiya ya samu a farfajiyar Afirka.

Fashin Baƙin Matashiya

Tsarin shi ne shirya wani abu, a kan madaidaiciyar manufa da za ta amfani mai tsarin da waninsa. Idan aka tsara abu, an huta da zullumin wargajewarsa. Wannan ita ce dabarar da kowace ƙasa ke bi, ta shirya dokokin zamantakewarta da sunan “Tsarin Mulki” mai suna “Constitution” da Ingilishi. Zumunta kuwa, tushe kalmar daga “zuma”, “Zumu” “zama”. Ita dai zuma mai zaƙi, wasu na ganin daga nan tushen kalmar yake. A wani karin harshe a ce, “zumuwa”, A nan gaɓoɓin biyu wato “zumu” da an yi musu ɗotanen “-nta”, an samu “zumunta”. Masu ganin daga “zama” take suna nuna zaman da ‘yan uwa suke yi tare nan aka samu “zaman tare” sannu a hankali, furuci ya mayar da shi “zumunta”. A nasu gani ke nan, wasali /a/ da /a/ na /z/ kalmar “zama” su suka sauya zuwa wasalin /u/ aka samu: “zumu”.

A fassarar ƙamusun Bargery (1951) ya ce:

Ingilishi:              

1.       Relationship by blood or marriage

2.       Chan feeling, e.g. between two people of the same town or district who meet in a place strange to both (=zumunta)

A Bahaushen tsari, zumunta wata babbar abu ce ga rayuwar al’umma, domin da ita ne aka kusanci juna; har fahimta ta kasance bai ɗaya. Ban ƙi fassarar Bargery ba, amma ina ganin sabunta tunani ba laifi ba ne, ci gaba ne. Ina hangen ma’anar zumunta da faɗi kamar haka:

Zumunta ita ce dangantaka ta jini ko aure ko harshe ko ta addini ko sana’a. Zumunta ta jini ita ce wadda ake samu ta tsatson uba ko uwa. Ta harshe kuwa ita ce zumuntar ƙabilanci, saɓanin ta addini da take zumuntar ban gaskiya ga abu ɗaya a ƙudurce.

Idan mutane sun kusanci junansu haka da sunan zumunci, zumuncin zai kasance wani sinaɗari irin maganaɗiso ya haɗa kansu wuri ɗayan a gudu tare a tsira tare. Ƙasar Hausa haka ta kasance, gabanin gaba, da bayan da ƙura ta lafa.

Dabarun Bincike

Matsalolin tsaron da ƙasarmu ke fuskanta su suka ba ni tunanin in bincike a kan dangantakan tsaro da zumunta. Mataki na farko shi ne, ratsa ayyukan da suka shafi tsaro da zumunta wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba. Bayan samun madafar aiki daga ayyukan ƙwararru; sai aka shiga karance-karance jaridu, da kafafen yaɗa labarai musamman na wayoyin hannu. An bi diddigin wasu ayyuka na ta’addanci har wuraren da suka wakana, domin daidaita akalar ɗora aikin ya yi kyau a samu misalan kafa hujjoji masu sauraruwa. An yi hirar ga-ni-ga-ka da wasu da suka faɗa tarkon rashin tsaro. An ga wasu ‘yan gidan jaridu, da rahotanni tsaro a kafafen yaɗa labarai; domin tattaro abubuwan da suke yayatawa na rashin tsaro da ta’addanci, Bayan haka, an samu sauraron waƙoƙin baka da rubutattun musamman waƙoƙin gasa na tsaro da aka gabatar shekarar 2021, fiye da ɗari. Wannan ya ba ni damar in hango abubuwan da ba su hango ba, na dabarun tsaro na ƙasar Hausa da ya kamata a yi bitar su a yi ƙoƙarin jarraba su. Na samu tattaunawa da ma’aikatan tsaro, na kuma samu gudunmuwarsu sosai.

Tsaro a Tunanin Bahaushe

A nahawun Hausa kalmar “tsaro” daga “tsari” take. Daga tsari aka samu, tsaro, tsarewa, tsararre da tsararru. A luga yakan ɗauki hana abu walawa da rashin sake masa mara, a ƙi ba shi sararin sakewa. Idan aka kai mai laifi kurkuku akan ce: “an tsare shi”. Idan aka sa dabbobi wurin kwanansu, ko wurin kiyo, akan sa mai tsaron su gudun su yi ɓanna. Mai tsaron su aikinsa “tsarewa” su da aka tsare su ne, “tsararru”. Saɓanin biyar diddigin nahawu Bahaushe yana kallon tsaro da:

i.            Samun kwanciyar hankali da lumana

ii.            Zaman lafiya mai sa walwaa da sake jiki.

iii.            Samar da sukuni natsattse ga ‘yan gida da baƙi

iv.            Wadatuwar abinci da zai hana wa yunwa barazana da kore fatarar da za ta hana hijira da ƙaurace-ƙaurace.

v.            Kare ƙasa, da mutanenta, daga kowace irin tashintashina ta cikin gida da waje,  wanda zai haddasa salwantar rayuwa da hasarar dukiya da lafiyar jiki.

vi.            Kawar da kowane irin ta’addanci da sace-sace, da samame, kowa ya shagaltu ga abin da ya sa ma kai.

Waɗannan abubuwa a ko’ina suka wanzu tsaro ya samu gindin zama. Muna iya taƙaita su, mu ce:

Samun kwanciyar hankali, da natsattsen sukuni, wanda zai ba da damar walwala, da wadatuwar abinci da sha, kowane ɗan ƙasa ya sake jiki, ya shagaltu da abin da ya sa gabansa. Cikarsa da batsewarsa shi ne, kare ƙasa da mutanenta ga kowane irin barazanar cikin gida, da waje, wadda za ta toshe kowace kafar tunanin yunƙurin tashintashina da ta’addanci, ga ‘yan ƙasa, da baƙinsu.

Yaya za a yi irin wannan yanayi ya samu,a wurin da aka rasa shi? Yaya za a dawo da shi, wurin da ya taɓa wakana ya sake salwancewa? Tunanin wannan bincike a kan Bahaushe, da ƙasar Hausa, ya tattara, don haka, sai mun tantance, wane ne Bahaushe, kana mu gano, ina ne ƙasarsa?

Ƙasar Hausa da Hausawa

Rubuce-rubuce da aka yi kan wannan matashiyar yawa ke gare su, kuma bayanansu wadatattu ne. Abdullahi Smith (1980) ya fara bayyana samuwar ƙasar Hausa da kafuwar biranensu. Neil Skinner (1979) Ya fayyace asalin kalmar “Hausa”. Hambali Jinju ya yi yunkurin tantance wane ne Bahaushe? (1989). Mahdi Adamu (1978) Ya kalli ƙaurace-ƙauracen Hausawa da bazuwarsu, da rawar da suka taka, a Afirka ta Yamma. Ga su nan dai. To, a taƙaice, ƙasar Hausa makekiyar ƙasa ce a cikin ƙasashen duniyar baƙar fata. A halin yanzu, ita ce ta mamaye Arewacin Nijeriya wato a jihohin Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kebbi da wasu sassa na Bauchi da Kaduna da Jigawa da Neja, A cikin ƙasa, ta yi iyaka da daular Borno da Nupe da wasu sassa na daular Oyo. A wajen ƙasa, wasu sassanta na maƙwabtaka da jamhuriyyar Nijar da Benin. Mutanen ƙasar Hausa, Hausa ce harshensu na gado, al’adunsu na ‘yan zuriyar harshensu ɗaya ne, kuma ban gaskiyarsu iri ɗaya ne. Ƙasa ce mai manyan dauloli, bakwai Gobir da Kano da Zazzau da Zamfara da Kebi da Katsina da Yawuri (Adamu; 2002). Hausawa bisa rinjaye, baƙaƙe ne wulit, masu gajeren zubi, da baƙin gashin kai mai kauri, da baki matsakaici.

Tsarin Zumuncin Hausawa

A fashin baƙin zumunci, an fara kawo zumuntar jini wadda ita ce babba ga tsarin zumunci na kowace al’umma a doron ƙasa. A tsarin zumuncin Bahaushe na jini ɓangare biyu ne: na wajen uba (mahaifi), da wajen uwa (mahaifiya); kowanensu mai ƙarfi ne a zamantakewa. Tsarin zumuntar jini ta kasu kashi biyu:

1.       Jelar salsalar tushe (dugi)

2.       Jelar sallsalar dangi

3.       Dangin auratayya

Jelar Salsalar Tushe:

Ita wannan wata bishiya ce da ake samun ta wajen uba da uwa, kuma duk amatakin jelar ɗaya ne; da ita ake rarrabe ‘yan uwan jini na gehen uba da uwa, matakanta shi ne:

a.       Kaka ya haifi Uba

b.       Uba ya haifi Ɗa

c.        Ɗa ya haifi Jika

d.       Jika ya haifi Kama kunne/tattaɓa kunne

e.       Kama kunne ya haifi Tankaɗɗa Hauɓi

f.        Tankaɗa Hauɓi ya haifi Taka Kusheyi

g.       Taka Kusheyi ya haifi Ihm!

A tsarin zumunci, waɗannan duk ana kiransu ‘yan kaka ɗaya; kuma kowanensu da kakan yake bugun gaba. Za a ga cewa, a gida ɗaya suke komai yawansu, har sai gidan ya zama wata ‘yar unguwa; har ya faɗaɗa ya zama tunga, wani lokaci ya zama gari zuwa birni. Haka mafi yawan garuruwan Hausawa suka tsira, har suka bunƙasa. A tsarin gonaki, za a ga duk a gandu ɗaya suke, sai mutum ya yi aure a fitar da shi gandu, a ba shi nasa gona babba. Yaran da ba su yi wa aure ba, suna nan cikin gandu, amma kowanensu za a ba shi ɗan gonan noma na kansa da ake kira gayauna/gamana, domin shi samu abin biyan buƙatocinsa. A cikin wannan tsarin za mu ga, a can da, ‘yan zumu ɗaya:

a.       A wuri ɗaya ake cin abinci, manya daban, yara daban.

b.       A gona ɗaya ake noma mai suna “gandu”.

c.        A gida ɗaya ake zaune, duk ma’auraci da ɗakinsa/ɗakunansa

d.       A tare yaran zumu suke wasa a cikin gida, da wajensa.

e.       Ƙananan ayyukan gida tare yaran gida ke yin su.

f.        Manyan ayyukan gida tare manya ke gudanar da su

g.       Bukukuwan farin ciki, da baƙin ciki, tare ake gudanar da su.

Waɗannan  dabarun ƙarfafa zumunci su ke hana a ga wallen juna. Su suka bai wa kaka ko Uba, ko duk wani babban a jelar zumunci zama alƙalin zuriya, da ya yanka ko ba daɗi a ci. ‘Yan’uwan zumunta su ke rankon ɓannar da ɗan uwa ya yi, da biyan bashin da ya kasa biya; da tilasta shi ƙaura idan ya aikata abin kunya, ko laifin da ke ɓata zuriya. Su za su yi tsaye ƙwato haƙƙinsa ga wanda yake bi, da wanda ya ƙware shi ko zalunce shi. Ƙawainiyar da ta fi ƙarfinsa, tana wuyan ‘yan uwansa; wadda ta fi ƙarfin ‘yan uwansa, tana kan wuyansa in mai karfin ɗaukarsa ne. Wanda duk ya aikata laifi gidansu ke hukunta shi, gabanin bunƙasar ƙasa, da kafa manyan birane da hukuma. Har yanzu ba a makara ba, idan kowane gida ko zuriya, za a ɗau ire-iren waɗannan matakai ana samun ɗan ta’adda a gida, ko unguwa, ko a gari? Idan kowane ɗan ta’adda tun cikin gidansu za a ta’addance shi, zancen ta’addanci ya kawa ga gari. Da za a hukunta kowane mai laifi tun cikin gidansu, babu tazarar da laifi zai fita waje, har a nemi mai shi. Ga ‘yan misalai:

Bukkar Tauri

Dubara ce da ‘yan uwa kan taru kan mai laifi, a yi ta dukansa har sai ya ce: “ya bari ya tuba”. Kowane ɗan uwa ya zo, da abin dukarsa, kuma doka wa zai ji, babu mai ba da haƙuri.

Taron Dangi

An ce taron faɗan-so-kanka ne. Idan an ga take-taken ɗan uwa na wuce gona da iri, tun bai jawo abin kunya ba; za a taru cikin gida a gaya masa cike da kunensa. Kowa ya zo da mugun kalaminsa na bakinsa, na ƙin halin da ɗan uwa yake son shiga, kar ya bar musu abin faɗi. Dubi zancen Narambaɗa a waƙar Ƙansanda Maikwatarkwashi.

Jagora: Ba shawagi sa maza yawon duniya

Yara: Suna yada abin hwaɗi ga ‘yan uwa.

Yanke Ƙauna                    

Idan aka ga take-taken zumu na haddasa wa zuriya kunya akan ɗauki matakin yanke ƙauna. Abin da ake shi ne, in an yi masa Taron Dangi ko Bukkar Tauri, bai razana ba, sai a yi gangamin yankar ƙauna. Za a taru a haɗe kai gaba ɗaya a ce:

a.       Wanda ya ba shi auren zumunta ya karɓe

b.       Wanda ya ba auren zumunta, ya mayar masa da ‘yarsa

c.        Wanda ya ba shi wata kyauta ya karɓo abinsa

d.       Wanda ya ba kyauta, ya mayar masa da ita

e.       A sa darni a raba gidansa da na ‘yan uwa

f.        A raba ƙofar shiga gida da shi

g.       In ya je bukin zumu a watse a bar shi, shi kaɗai

h.       In buki ya same shi, ka da kowa ya je

i.         In an haɗu da shi a hanya a kau da kai, in ya riski ‘yan uwa zaune a kofar gida kowa ya yi malle.

Duk waɗannan matakai shi kaɗai ta shafa ba da iyalansa ba. Ka ga an bar wata ‘yar kafa da zai saurari iyalansa, su kuwa su jawo hankalinsa. Sannu a hankali dole ya lura ya waiwayo ko ya zama shi kaɗai. Idan ɗan uwa nagari ne, aka gan shi cikin matsala dole a taru a fuskance ta, ka da ya shiga wani hali ya bar musu abin faɗi. Daga cikin dabarun taimakon dangi akwai: gayya da ajo da kyauta da ɗegiya da aro da bashi da talme da ɗauke da da aike. Ga bayanin “Aike” domin a ga misali:

Aike

Idan aka fahinci hatsin rumbun ɗan uwa ya ƙare ba sauran abinci. Babba daga cikin zuriya ko dangi zai kira shi ya aike shi wajen wasu ‘yan uwa na gari ko ƙauye mai ɗan nisa. Za a ce, ya bi sanyin marece ya kwana can, da safe. Yana barin gari da maraice, ‘yan uwa za su kawo gudunmuwar damman abinci na hatsi a cika masa rumbu dam! Za a yi haka cikin dare, kowa shi da kansa yake zubawa rahewa har sai ta cika; babu wanda zai riski wani wurin balle a tsaya a yi tsegumi, kowa jinin zumunta ya yi wa.

 

Kaico! Gidan daɗi na nesa in ji angulu da ta tsinkayi masai/salaga. Waɗannan dabaru su suka taru suka ba ƙasar Hausa cikakken tsaro da babu irinsa a sauran dauloli makwabtanta. Dabarun tsaron sun taso tun a cikin gida, da unguwa, da gari, da gunduma, da ƙasa baki ɗaya. Dalili ke nan, da ya sa, a tarihi a ƙasar Hausa ba a samu fitattun ‘yan ta’adda ko taƙadarai ba, sai dai fitattun buwayayyi na karfin tuwo da tsafi da siddabaru. Don haka muke da fitattun ‘yan dambe da ‘yan kokuwa da mafarauta da masunta da buwayayyi. Ina ta’addanci da rashin tsaro zai wanzu a ƙasar da aka riƙe hannun juna, a gudu tare, a tsira tare? Dole a samu nagartaccen tsaro ƙasar da duk ɗan ta’adda tun a gidansu ake yanke masa ƙauna a guje shi? Ai ko adda aka yi wa irin wannan kora da hali, ba ta kaifi bale ta sari wani.

Jelar Salsalar Dangi

Ita ce jelar da Bahaushe ke ce wa, “dangin-na-dange-ka”. Dangi ne na ɓangaren ba bisa matakin jelar salsalar tushe ba. Abin da ya fito daga ɓangaren uba da uwa su ne dangi kuma zumuntarsu ta jini ce.

a.       Wan Uba/’Yar Uba

b.       Ƙanen Uba/Ƙanwar Uba

c.        Mijin Uwa/Wansa/Ƙanensa/Yan’uwarsa

d.       Matar Uba/Iyayenta/’Yan Uwanta.

A cikin wannan riɓinjin za a samu wani zumunci mai ƙarfin gaske ya bayyana, a nan za a samu.

i.         K awu: ƙanen uwa ko wannan uwa

ii.       Goggo: ƙanwar uwa ko yar uwa

iii.     Taubashi: ɗan ƙanen uwa ko wan uwa

iv.     Taubashiya: ‘yar ƙanwar uwa ko ya, ko ta wajen uba

A nan ne ake smaun auren zumunci na haƙiƙa, kuma auren zumuncin ƙarfafa zumunta yake, ya ƙara faɗaɗa tsaro ga zuriya da ƙasa. Auren zumunci na ƙara faɗaɗa zuriya idan zuriya ta faɗaɗa danƙon zumunci ya ƙaru. Ƙaruwar danƙon zumunci na ba ‘yan uwa mafaka da kariya irin ta dangantaka. Idan kariya ta faɗaɗa an faɗaɗa tsaro da yi wa ta’addanci barazana. Da ‘yan uwa suka rinjayi bare a al’umma natsuwa da zaman taimakakeniya zai ƙaru, wanda shi ke haddasa kusantar juna, da kawar da baƙar fatar, da mugun nufin da zai haifar da tashintashina. Sarkin Kabi Kanta Kotal mahaifiyarsa Bakatsina ce, don haka aka zaman lafiya da juna, Kabawa na kallon Katsinawa bayinsu (yaransu) saboda su ne gidan maza. Arawan Kabi da Gimbanawan Kabi ‘yan mace da namiji ne, Arewa ne ɗiyan mata, Gimbanawa ɗiyan maza. Babu faɗa, bale ƙara, ko ramuwar gayya tsakninsu.

Dangin Auratayya

Auratayya in ba ta zumunta ba ce, ba ta kasancewa dangi jini. Daga cikin dabarun kashe wutar gabar yaƙi akwai auratayya. Da an yi aure, miji da mata sun zama abokan zaman juna, yan uwansu sun zama dangin juna. A tsarin aure ake samun dangantaka da zumunci da zai kasance:

(a)    Namiji ɗaya da mata da yawa ‘ya’ya daban-daban

(b)    Mace ɗaya ta auri maza da yara ‘ya’ya daban-daban

(c)     A nan za a samu ‘yan uba, uwa ɗaya uba kowa da nasa

(d)    Agola, wanda uwarsa ta zo gidan mijinta goye da abinta

(e)     Bawan gado wanda mata ta zo da abinta gidan miji.

 

Waɗannan duk da kasancewarsu ba ‘yan uwan jini ba ne, amma aure ya haɗa su wuri ɗaya. Haɗawar da aure ya yi musu, za a ga a koyaushe:

a.       Tare ake cin abinci akushi ɗaya

b.       Tare ake wasannin dare da rana

c.        Tare ake zuwa gona da kiwo da ban ruwa

d.       Tare ake kwanciya barci, tare ake zuwa wanka kogi

e.       Tare ake bukukuwa na madalla da wayyo!

f.        An san juna, an san halin juna, an saba da juna

An riga an zama ‘yan uwan juna zance a cutawa ɗan uwa bai taso ba. Abubuwan da ke aukuwa na rashin tsaro a yau, na ta’addanci rashin wannan kusanci ya haddasa su. Wa za a yi irin wanan zamunci da shi ya yi tunanin saka wa ƙauye ko gari ko birnin da ya tashi wuta? Wa zai yi ƙarfin halin yanka wanda suka tashi tare kamar rago? Tsarin zumuncin Bahaushe ya ba da sanayya da ke haifar da ragowa da wasu ƙabilu da ba Hausawa ba suka rasa.

Zumuntan Ƙasa da Harshe

Na yarda da cewa, an yi kuren kyawo tun ranar haihuwa, ƙasar Hausa da take makekiya mai dauloli girkakku guda bakwai suna da zumuntar harshe ɗaya, karin harshe bamban. Al’ada iri ɗaya tsagar gado ta fuska bamban. Ƙasa ɗaya dauloli daban-daban. Duk da kasancewarsu Hausawa kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. Mutanen Daura na bugun gaba da Abu Yazid (Bayajida); Kanawa da Bagauda; Katsinawa da Katsi; Kabawa da Kanta; Gobirawa da Jangwarzo; Zegezagi da (Amina); Zamfarawa da ‘Yargoje, Yawurawa da Jarbana. Duk suka yarda da cewa, sunan ƙasarsu ɗaya ƙasar Hausa, komai ya tashi kai haɗe ake tunkararsa. Da Turawan mulkin mallaka suka shigo ta gaba ɗaya aka yaƙe su. Yawurawa suka hana Mungo Park shiga ƙasarsu. Satirawa suka yaƙi Turawa (1906) suka kashe musu babban hafsansu Cat. Helary. Haɗejawa suka yaƙi Turawa suka kashe shugabansu Maitumbi.

Da jihadi ya zo, haka suka game kawunansu wuri ɗaya bisa fahimta iri ɗaya. A mafi rinjayen tunaninsu akwai ɗan surkin ƙabilanci da siyasa ga ma’abotan jihadin musamman bayan wafatin jagoran jihadin Mujaddadi Ɗanfodiyo. Rashin haɗin kan da ake samu na wani ɓangere daga cikin ɓangarorin Nijeriya kan yaƙi da ta’addanci shi ya sa ba a ci nasarar murƙushe shi ba. Tsaron ba ya samuwa sai an ɗinke ɓaraka ɗan ta’adda ya ga ba wurin kutsa kai.

Bayan haɗin kan Hausawa, akwai wasu al’adu na yaƙi da suke son ɓacewa a yau. A da can, kowane Bahaushe ka duba a fuskarsa akwai askar kakaninsa ba sai an tambayi ina ya fito ba. Idan ruwa biyu ne, uba Bagobiri, Uwa Ba’ara, za a ga askar uba a haɓar dama ta uwa a hagu. To, ko kamo su aka yi a yaƙi babu kasuwar da za a kai su ƙasar Hausa, domin zumunsu na taron dangin karɓo su, kuma babu mai sayen zumunsa ya bautar da shi a ƙasar Hausa. Me ke faruwa a yau? Ɗan gari zai kasance wakilin ‘yan samame, a game baki da sarakunan ƙasa, da jami’an tsaro, a yi wa ‘yan ƙasa fashi da samame. Dubi wannan labari:

‘Yan fashi suka tare hanya, suka kama mota ɗaya da ta fito daga Legas. Fasinjoji kowa ya ci albarkacin dugadugansa ya fantsama daji. Ɓarayi suka ce: “da wa aka haɗa mu ba da ku ba”? Can wani fasinja Ba’are ya gaji da gudu ya faɗi ɗan fashin ya zo ya kama shi. Yana duba fuskarsa sai ya ga askar Arabci, shi kuwa ɗan fashin Bagimbane ne, sai ya ce wa ‘yan uwansa, ‘yan fashi,: mu sake su, su wuce matsiyata ne, ‘yan gadon tsiya ko kwabo ba su da”. Da Ba’are ya gane Bagimbane ne mugun, sai ya ce: “Kai ɗan baya, ni ban gadi tsiya ba, ka duba ga bamburutu in babu kuɗi, ana buɗa taya sahiya ga kuɗi cike sai Bagimbane (ɓarawo) ya ce; “Lallai ba ku gaji rufi ba bale ƙarya”. An ce, Ba’are ya nemi a ba shi nasa kamisho na shiga mota, an ko ba shi.

Me ya haifar da wannan labari ba zumunta ba? Da babu wasa tsakanin Arawa da Gimbanawa, ɗan fashi na tsaya wa labari da wanda ya tare, ya ruga, aka kama shi? Ashe zumuntar ƙasar Hausa maganaɗison tsaro ce, da an nemi matakan inganta ta, da an rage musibun samame da fashi da tashintashina. Har yanzu ba a makara ba, a sa darusansu a manhajar koyarwa a makarantunmu tun daga firamare har jami’a a gani.

Zumuntan Suna

Idan matsala ta samu duk yadda ‘yar kafa take ta fita daga cikinta za a leƙa ta a gani. A da, ƙasar Hausa, suna wani maganaɗison zumunta ne. Har ma wata waƙa yara ke rerawa a dandalin suna cewa:

Jagora:   Da Ali da Ali Ana faɗa

: Wani Ali yaz zaka yar raba

: Kai Ali mis sa kar raba?

                : Don daɗin suna nar raba

: Don gobe ina yi su raba.

A ƙasar Hausa akwai al’ada ta zumuntan suna da ake cewa “takwara”. Mai sunanka shi ne “takwaranka”. Idan an yi wani mutum takwara har kyauta yake yi wa yaron da nuna ƙauna ka ce, ‘yan uwan juna ne. Ana yi wa yaro takwara saboda ficen sunan mai suna na farko na arziki, ko ilmi, ko sarauta ko wata baiwa can ta daban. A al’adar Bahaushe, suna wata babbar haja ce da Bahaushe ke danƙon zumunci da shi.

a.       Idan mutum na da suna ɗaya da kai kun zama takwara

b.       Mutum mai sunan mahaifinka ya zama baba

c.        Mai sunan yayanka ya zama yaya

d.       Mai sunan ƙanenka shi ma ƙane ne

e.       Mai sunan abokinka, aboki ne

f.        Mata mai sunan mahaifiya, mahaifiya ce

g.       Mai sunan mata, abokiyar wasa ce

h.       Mai sunan kaka abokin wasa ne.

Ga al’ada, matan Hausawa ba sa faɗin sunan mazansu na farko, da ‘ya’yansu na farko, da sunayen surukansu, sai dai su yi wani ƙaƙale ko su yi amfani da wakilin sunan shi/ita/kai. Kunyar da ke cikin waɗannan abubuwa suna da tasiri ga tsaron kasa, yadda ba a iya kutsa wa sunayen a al’adance haka nan ba a cuta musu a bayyane ko a ɓoye. Idan mai suna ya ci sunansa, yana tsira daga cutar mai jin kunyar sunansa. Alhaji Abubakar Imam ya kawo irin wannan ƙissa a Magana Jari ce, wurin da ɗan fashi ya tare wata mata da mijinta. Da ya zaro takobi zai sare ta, ta ce: “Wayyo! Ni Halima na mutu na lalace”. Ya ce ta yi sa’a domin sunan mahaifiyarsa ne. Ya je gun mijin ya ce: “kai fa”? Ya ce: “Ai ni ma sunana Halima”. Mujaddadi Danfodiyo ya faɗa a cikin littafinsa, Ihyau’us Sunna cewa, za a zo da mai ɗimbin laifi gaban ubangiji a karanta masa laifukansa, sai ya tabbata ba ta da gyara. Ubangiji ya ce: “Saboda kana da sunan masoyina Ahmad Na yafe maka”. Ashe suna maganaɗison tsaro ne, ko ranar hisabi. Zumuntan suna ya sa, Ado ya yawaita Kano; a Sakkwato Cika, a Zamfara Garba, a Birnin Kabi Ƙangara da Modi, a Tambuwal, Zaki, ga su nan dai.

Zumuntar Sana’a

Bahaushe ba zauna gari banza ba ne, bayan sana’o’in gado fitattu da aka sani, noma da ƙira da su da farauta da fatauci da saƙa, akwai sana’o’i a kowane zamani na hana zaman banza da sa ido. Kowace sana’a fitacciya amintacciya tana da sarauta. Idan mai irin sana’ar ya zo a gida sarkin sarautar sana’arsa ake yi masa masauki. Waɗannan sana’o’in an keɓe wasu daga ciki manya kamar Sarkin Noma da Sarkin Ruwa da Sarkin Daji  da Sarkin Fawa ko Wanzamai su kasance a cikin Majalisar da ke zaɓen Sarki. Dalili kuwa, gari bai kahuwa sai da su dan suna cikin masu zaɓen sarki tsaro babba ya samu. Baƙin da ke shigowa ta ruwa na Sarkin Ruwa ne. Waɗanda ke keto daji na Sarkin Daji ne, masu shigowa gari kwatsam a kai wa sarkin Baƙi da Magaji da Maikasuwa, in samari ne a kai su ga Maisamari. Idan kowane baƙo na da mai masaukinsa mai kula da shi, ba a tsoron wata tashintashina daga baƙin haure, Zumuntar sana’a na sa kowace sana’a ta san na ƙwarai da mugun da ke cikinta, ana kiyaye da kowa. Duk baƙon da bai da sana’a ba ya da masauki a gari sai dai ya hari gaba, da haka ake hana wa macuta bagiren zama a ƙasar Hausa. Ƙaddara da babu sana’o’in nan da sarautunsu wace dabara muke da ita ta tantance baƙin da ke kwarara a ƙasashenmu. Masu sana’o’inmu suna auratayya tsakaninsu, suna bukukuwa da wasanni irin nasu da nuna waibuwa da za su taimaka wa tsaro da buge kangara.

A Share Jini a Koma Wasa:

Bahaushe bai yarda da gabar sai baba ta gani ba. Haka kuma bai ɗauki a ci gaba da yaƙi a mutu har liman ba. Irin yaƙe-yaƙen jahiliyya na Larabawan Makka kamar yaƙin Basus da Taglib wanda aka share shekara (99) ana fafatawa. Har a tambayi gwarzon yaƙin ya kasa sanin dalilin da ya sa yake yaƙin. A tunanin Bahaushe, abokin yaƙi zumu ne, domin kar ta san kar aljani ya taki wuta. Fafatawar da aka yi lokacin gaba ta sa aka kusanci juna saboda abubuwa huɗu:

(i)      Babu sauran reni da takaicin juna kowa ya ɗanɗani kuɗarsa

(ii)    In dai wani ya rinjayi wani, in ko an rabu dutse hannun riga

(iii)  Kowa ya kwashi accakwamarsa ta gawawwaki da masu rauni.

Idan an ɗebe rainin juna, za a kusanci juna har zumuntan abokantaka da aure ya shiga. Dangantakar Fulani da Gobirawa a yau abin misali ne. Dubi dangantakar Fulani da Kabawa duk da sanin cewa; “Kabawa ke da galaba ga yaƙin, amma yau zumunta ta mamaye gaba, Sarkin Kabin Argungu, Muhammadu Mera na aure da ‘yar Sarkin Musulmi Abubakar III. Karon Sarki Sama na Argungu da Sanyinnawa babu wanda ya yi dariya. An kashe wa Sama dukkanin dakarunsa (‘yan gitta), shi ko ya kashe Sanyinnawa fiye da tis’in (90). Yau an maye gurbin juyayin hasarar da wasanni da auratayya. ,Abin da ya faru a Alwasa tsakanin Fulani da Kabawa fiye da gawa (200) aka yi na Fulani, amma bai hana a yau a zauna wuri ɗaya ba. Abubuwan da suka biyo baya su ne wasannin barkwanci (Peace talk) tsakanin Kabawa da Fulani, Fulani da Gobirawa; Katsinawa da Nufawa, da Fulani da Barebari. Ba fatar yaƙi a je kowa ya mutu ba, ai shi ya sa muke da tarihin a mazaya a mayar da iri gida inji Gobirawa. Ƙoƙarin ƙirƙiro hanyoyin sasantawa da ‘yan ta’adda, musamman kamammunsu da waɗanda suka miƙa wuya da ‘yan tawayensa da ‘yan gudun hijirarsu, yana dallashe kaifin ƙiyayyar gaba har a ci nasarar kashe wutarta.

Zumuntar Wasanni

Fitattun wasannin da suka shahara ƙasar Hausa su ne wasan dambe da kokuwa da tauri. Wasannin za a fara tun a ƙofar gida, a fita unguwa, a je tsakiyar gari a yi unguwa da unguwa. Daga nan, a fita gari, a yi ƙauye da ƙauye, har a kai na gunduma da gunduma daga nan a fita wajen gunduma ya kai ƙasa da ƙasa kamar Zamfara da Kano, Ko Gobir da Kabi, ga su nan dai. Zumuntar da wannan ke haifar wa ba ƙarama ba ce. Daga nan abota ke ƙulluwa tsakanin ‘yan wasa, har abin ya kai ga auratayya ko wani ya tare a garin wani, ga su nan dai. Haka ake da a ƙasar Hausa kowa ya san kowa. Yara samari sun san abokanin kokuwarsu da abokanin dambensu na unguwarsu da ƙauyensu da gundumarsu da ƙasarsa. Idan haka abin yake an san ɓata gari an san nagartacce. Zumuntar da aka ƙulla ta wasa ta sa, an zama ‘yan uwan juna. Wannan ɗan uwantaka ba ta bari a yi amfani da su, a cuta wa abokan wasansu. Ba sa sa hannu kuma ba sa yarda a shirya ta’addanci zuwa ƙauyensu ko ƙauyukan abokan wasansu. Ashe ke nan sai dai ɗan ta’adda baƙo ya je da kansa. In ta kasance haka, yaya zai ci nasarar kai farautar samame ba a samame shi ba? Misali shagon Ɗan’anace da yaransa sun yawace ƙasar Hausa dukkaninta har cikin Jos, da Bauchi, da Damagaram, da Maraɗi. Ko’ina ana da aboki, an san ka, ka san mutane, wace zumunta ta fi haka? Ai shi ya sa Bawa Ɗan’anace ke ce masa:

Jagora:   Rage faɗa ka samu aboki,

                Yawo hakan ga ba shi da daɗi

                Mutum shi na ta yawo shi ɗai.

                                (Bakandamiyar Shago)

Zumunta a matakan rayuwar Bahaushe

Matakan rayuwa su ne: aure, haihuwa, da mutuwa. A tsarin auren Bahaushe ranar ɗaura shi, amarya da ‘yar tahiya take zuwa, za ta tarar da ango da yaronsa. Waɗannan yaran, ba dangi ango ko dangin amarya ne ba, za a taras yaran maƙwabta ne kawai da kowa ke zaɓo wanda yake so. Yaran za su yi a ƙalla sati ɗaya zuwa wata ɗaya tare da su, da sauran yaran gida. Haka shi ma ango, abokaninsa za su riƙa ɗaukarsa kwana har na tsawon sati ɗaya ya kwan nan, ya kwan can, kuma duk wanda aka kwana gidansa lalurar komai na a kansa. Waɗannan matakan kyautata zumunci suna ƙara baza soyayya da kusanci tsakanin jama’a. Da ango da yaron ango, da abokanin ango, da ‘yan tafiya, da amarya, an sake wani sabon zama na zumunci a wani yanayi na daban da ba na gida da aka saba ba. A tunanin wannan bincike muddin akwai kusanci na zumunci ko ɗanuwantaka, ko abota, ta’addanci ba zai ci nasarar tarwatsa mutane ba a murƙushe shi ba.

Mu dubi tsarin bukin haihuwa da shagulgulan da ke ƙunshe cikin na raɗa wa jinjiri suna, da yi masa tsagar gado da kwalliya ranar buki. Iyayen nasa sai an tabbatar da tushensu gabanin a ɗaura aure. Haka nan ranar mutuwa tana da taron tanzanko na musamman. Ga al’ada kowa ya mutu sai an yi masa bukin bizne shi, ke nan, an san da mafarin mutuwarsa. In ba annoba ba, ba a zaman makoki gudan gari. Kowa ya san mutanen gidansu ya san yan zuriyarsu, ba wanda zai yarda ɗan wani gida ko ɗan wata zuriya ya zo ya yi musu ta’addanci. Bukukuwan aure da haihuwa da mutuwa ba bisa jahilci ake yin su ba, ana yin su domin sanayyar juna da sanin ƙaruwar da aka yi da raguwar da ake samu. A koyaushe ana sane da juna a ko’ina baƙo ya shigo an san da shi ana kiyaye da shi. Irin wannan tsarin shi ne, cikakken tsaro mai taushe ƙurar kowace irin tashintashina da hana ta gawurta. Ƙaddara idan kowa bai san kowa ba, babu wurin haɗuwa a ji zarmoɗan juna, yaya makomar zumunci? Idan zumunci ya salwance, so da ƙauna, dole su bi shi. Idan sun bi shi, ba a bar komai baya ba face, ta shi ka rama, tashi ka kare kanka, mu je mu yi gayya, da mu je mu rama gayya da hushi. Nan da nan duniya ta zama rana, babu inda ɗimin inuwa yake. Ta’addanci da tashintashina sun samu gindin zama.

Sakamakon Bincike

Wannan ɗan bincike da ya yi garkuwa da zumunta wajen tabbatar da tsaro da kawar da ta’addanci ya ɗan gano wasu abubuwa muhimmai kamar haka:

1.       Zumunta ita ce babban makamin tsaro kuma ita ce maganaɗison ɗinke kowace ɓaraka ta cikin gida da waje.

2.       A ko ina aka ga ‘yan ta’adda sun kai harin bisa, kan mai uwa da wabi a bincika maharan ba sa da alaƙa da wurin da suka kai hari.

3.       Fittattun ‘yan ta’adda, za a same su da abubuwa uku: ba su da tushe na ƙwarai; ba su da zamantakewar gargajiya da tarbiyarta; duhun jahilci ke ci musu tuwo a ƙwarya.

4.       Idan ana son nagartaccen tsaro, a ɗauko ta da tushe, tun yaranta, yaranmu a bari su ɗanɗani al’adun zamantakewar gargajiya. A saka tarbiyarmu cikin manhajar karatun yaranmu na addini da na boko.

5.       A dawo da yi wa samari aure tun da wuri, su shiga cikin sahun magidanta, su ji abin da kowa ka ji, da sun haihu dole su shagaltu da abin da kowa ya shagaltu da shi. Yin haka wata hanya ce ta hana wa ta’addanci da tashintashina sababbin ɗalibai. Makarantar duk da ba a samun sababbin ɗalibai tana rigayan rana faɗuwa.

Naɗewa

Aikin kulawa da tsaro da kawar da abubuwan da ke haddasa rashin tsaro taron dangi ne kowa sai ya sa hannunsa. Babu ƙasar duniya da ta samu tsaro dare ɗaya, dole sai an bi diddigin tarihi don ba a fafe gora ranar tafiya. Zumunta ita ce tushen tsaro, ita zumunta tana yi wa kanta aiki ne, don haka dole ta tsaya ta yi shi da kyau. Tun fil azal, babu mai nunin gidansu da hannun hagu bale ya shirya ta’addanci a kai wa garinsu, ko ƙasarsu, ko ‘yan uwansa hari. Mummunan hari na a mutu har liman sai bare wanda ke jin takaicin mutanen da ya kai wa hari saboda daaɗɗɗiyar adawa ta yankan ƙauna da ke tsakaninsu. Tabbas, rashin kusantar juna da zaman ‘yan marina wata babbar ƙofa ce, ta ba rashin tsaro kafa. Matuƙar bango ya tsage babu abin da ke hana wa ƙadangare kutsawa. Auratayya zumunta, da haɗuwa wuraren bukukuwa, da wasanninmu, da tsage-tsagenmu na gargajiya su ne maganaɗiso tsaron ƙasashen Hausa a da, waigawa baya, ba ci baya ba ne. Dabarun na zamaninmu sun kasa magance fitinun zamaninmu. Me zai hana mu jarraba tsohuwar zuma?

Manazarta

Muri, Aliyu Muhammed (2003) “The Defence Policy of the Sokoto Caliphate”, 1804-1903, PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Adamu, Mahdi (1979) The Hausa factor in West African History, Zaria, Ahmadu Bello University Press.

Alƙali, Muhammadu Bello (1968) “Hausa Community in crisis, Kebbi in the Nineteeth Centry”, MA Dissertation, Zaria, Ahmadu Bello University

Junaidu, Muhammad (1978) Tarihin Fulani, Zaria: Ahmadu Bello University Press

Last, Muarry (1967) The Sokoto Caliphate, London: Longman Publishers

Mani, Abdulmalik (1978) Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa, Zaria: NNPC, Press

Lugga, Sani Abubakar (2014) Natural Disasters Caused by Huamn Disorbedience to Allah as Prosphesed by Prophet Muhammad (SAW), Katsina: Lugga Press

Bunza, Aliyu Muhammadu (2009) Narambaɗa, Lagos: IBRASH, Publishers

Magaji, Ahmad (1980) “Nazari a kan Rayuwa da Waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi”, Kundin B.A. Kano: Jami’ar Bayero

Abbas, Nazir Ibrahim (2019) Nazarin Wasu Nau’o’in Kare-Karen Hausar Yamma da Siffofinsu PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Universiry,

Dalhatu, Suraj Muhammad (2012) “Historical Development of Shi’a, It’s Activities and Implication to Muslims in Northern-West Nigeria” PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Soba, Aliyu Sani (2017)” Tanadin Tsaron Gargajiya a Ƙasar Zazzau (Waiwaye cikin zamunan Sarakunan Haɓe 1435-1803)” kundin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo

Nadama, Garba (1977) “The Rise and and Collapse of a Hausa State, a Social and Political History of Zamfara” PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.010

Post a Comment

0 Comments