Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 28)
Baban Manar Alƙasim
d) Duk wani jagoranci da kake
ji ko kake gani ko ma kake yi ka san cewa yana buƙatar tsari, hatta jagoranci
irin na gida bai yuwuwa sai da tsari, misali tattalin kudi da yadda ake kashe
su, wannan yakan taƙaita ne da yadda ake samo su, gwargwadon shugowarsu gwargwadon
shigewa, sai kuma tsarin mu'amalla, matsayin uwargida da na 'ya'ya, da duk abin
da kowanne yake buƙata na rayuwa, dole maigida ya riƙa duba yawan iyalinsa da abin
da zai ishe su, kar ya ƙara ya wuce ƙima, kar kuma ya yi ƙoro. Sai kuma haduwa da sassan
iyali don tabbatar da ginuwar zuriya, duk wani da ka gani a cikin gida yana da
gudummuwar da zai bayar don ginuwar iyali, a gurguje dai shi maigida shi ne zai
mai da gidansa dinkakke yadda kowa zai yi alfahari da cewa daga zuriyar yake,
in dai maigida ya iya dinke gidansa, za ka taras akwai zaman lafiya, cikakkiyar
ƙauna, riƙo da addini ga yalwatuwar jin
dadi, tarbiyar yara bisa kyakkyawar hanya tana ƙara kyautatuwar alaƙa tsakanin maigida da uwargida,
don uwaye, ma'aurata da diyoyinsu rukuni ne na ginin iyali, in har wani yanki
ya sami matsala to zai shafi zamantakewar ma'aurata, sau da yawa wasu
matsalolin aure daga uwaye ne suke tasowa, wasu kuma da wani É“angare ne na ma'auratan, wasu kuma da
'yan yara ƙanana. Ka lissafa waɗannan nan abubuwan don jin dadinka da na iyalinka:-
a) Kar ka yawaita kushe ta,
kamar yin magana a kan yadda take sanya tufa, ko yadda take ci ko dafa
abincinta, ko yadda take yin magana. b) Kadan riƙa yi mata ba-kan-zata wajen
siyo mata wasu abubuwa, hatta yadda za ka miƙa ma ta abin da kasiyo ma ta ya
zama yanayi ne na masamman. c) In za ka riƙa kiranta da wani suna na
masamman za ta so, ya zama ba mai kiranta da shi sai kai, mu dai ba mu cika
wannan ba, amma akwai masu yi da dama. d) Kadan riƙa yi ma ta hanzari a dan wasu
lokutan, masamman lokacin da aiki ya kicime ma ta, ko yaro ya ishe ta da kuka,
ko a halin al'ada ko samuwar ciki, sau da yawa za ka iske ta da saurin hasala,
kar ka biye ma ta don gyaran gidanka. e) Zai yi kyau ka taimaka ma ta a wasu
ayyuka na cikin gida, matuƙar za ka iya, in kuma wasu za
ka samo ma ta ba laifi, in duk wannan ba zai yuwu ba, to ka riƙa rage ma ta wankin
kayayyakinku, akwai wadan da sana'arsu kenan wanki da guga. f) Abinci yana da
tsarin da ake cin sa, yin bismilla, ci da dama, kuma kowa ya ci ta gabansa,
wasu sukan so su ci da iyali, ko su ci lokaci guda, gaskiya wannan ya fi
burgewa sama da a ce mutum yana daki shi kadai, su kuma iyalin suna na su
dakin, wasu matsalolin iyali ba a cika ji ba sai lokacin cin abinci, sau da yawa
in yara suna yin wata ƙiriniya sukan yi tunanin
lokacin cin abinci, don galibin yara duk da sakewar da mahaifinsu yake yi, in
har suka bata masa rai sun san abin da zai faru, to sukan kiyaye.
g) Wasu magidantan ba su cika
kula da lamuran zumuntarsu ba, alhali abu ne mai matuƙar mahimmanci, sau da yawa akan
sami sakaci a wurin uwargida in ta fahimci cewa maigidan bai cika damuwa da
mahaifansa ko 'yan uwansa ba, matsalar da ake samu in mace ba ta kyautata wa
uwaye da 'yan uwan mijinta, ba su cika kai ƙararta wajen maigidan ba, su a
ganinsu yana sane da abin da yake faruwa, ko kuma suna tsoron su haifar masa da
wata matsalar da iyalinsa, abin da zai zama mafita a wannan wuri shi ne,
magidanta su riƙa duba alaƙoƙinsu da uwayensu, kuma su riƙa bin diddigin kyautatawar da
suke musu, su kuma tabbatar da cewa akwai ƙauna da son juna a tsakanin
iyalansu da uwayensu.
h) Wai shin dole ne maigida ya riƙa ba wa iyalinsa albashi duk wata? I to ban taba karanta wannan a wani littafi ko wani rubutu ba, bare na yi ƙaryar cewa ina da wani hadisi da Annabi ya ce a yi haka, abin da na sani kawai ita mace tana da zumunta kamar yadda kai ma maigidan kake da shi, ba shakka za a riƙa tambayarta 'yan gudummuwoyi na biki da suna, zai yi wahala ta riƙa tambayarka zumuntarka da tata, sai dai mafita a nan ka tura ta makarantar koyon sana'a yadda za ta dogara da kanta, ko ka ba ta jari, in ta sami abin da za ta dogara da shi kai ma ka huta, sau da yawa wasu matsalolin suna ginuwa ne daga rashin aikin yi. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.