Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 27)
Baban
Manar Alƙasim
g) Akwai babbar gudummuwa da
maigida zai ba wa iyalinsa wajen ganin gida ya ginu sosai yadda ake buƙata, galibin aurarrakin da ake
yi yau za ka taras ko dai hadawa aka yi, ko kuma a kan hanya ya gani kuma ya
dauka, amma akwai wasu 'yan daidaiku da ba a rasawa wadan da a makaranta aka
hadu ko a wajen aiki, irin wannan gamuwar ta daidaitacciyar wayewa ta fi sauƙi nesa, sama da wata, in ya
kasance akwai tazara mai girman gaske ta ilimi ko wayewa a tsakanin maigida da
uwargida zai yi kyau shi ma ya jefa ta makaranta, ko ba za ta yi aiki ba za ta
dan sami damar da za ta riƙa yi masa hirar da yake so, ko
ta fahimci abubuwan da yake buƙata da lokacin da yake buƙatarsu, in ta yi nesa da shi ba
dole ba ne su riƙa fahimtar juna. Sau tari za ka ga dan boko zalla wanda bai da
wata wayewa a karatun muslunci sama da karatun sallah, in ya ga wata yarinya
kamammiya ko kyakkyawa sai ya auro don tarbiyyar yaransa, galibi akan dan sami
matsala don ita tana yi masa kallon jahili ne tuburan, wasu lokutan ma takan
kai ga sai ta dan yi masa wa'azi, shi kuma ba dole ne ya fahimce ta ba,
masamman idan ya gano cewa tana raina ƙoƙarinsa a addinance ga shi kuma
shugaba, kyau dai ya saka ta a makarantun bokon, shi ma ya dan koma wata
islamiyyar manya don ya gyara yanayin zamantakewar. A binciken da muka dan yi
da wasu 'yan uwa marubuta mun gano cewa galibin matan da suke da karatu ba a
wurin mazansu suka koya ba, karatun miji da mata bai cika ƙarko ba, shi yana ganin shi
malami ne, ita kuma ta san maigidanta ne kawai, dan abu kadan zai nemi yin
fada, ita kuma ba za ta jure ba, da ma wani ne ba shi ba, to in ba a yi dace ba
sai ka ga ana ta samun sabanin fahimta, in ka lura da kyau galibin matan
malamai ba malaman ba ne, to amma da mazan za su kai su makaranta tabbas za su
yi karatun a can. h) Kamar dai nuna ƙauna da fadi a baki galibin
mata suna son haka, in namiji ya ga ba zai iya ta sa matarsa a gaba ya ce
"Wallahi kina bala'in burgeni" ba, to ya dace ya namo wata hanyar da
za ta maye makwafin wancan, kamar dai 'yan wasanni, ko ba-kan-zata, wato ya dan
riƙa siyo mata wasu abubuwan da ba ta yi tsammanin samunsu a daidai
wannan lokacin ba, kamar sarƙoƙi, kayan shafe-shafe, da na
fesawa, sai kuma 'yan kayan ƙwalama gwargwadon yadda Allah
ya hore wa mutum, wani lokaci har irin bugo wayannan ka tambaye ta halin da
take ciki yana da dadi.
i) Wasu lokutan fa dole sai an
sai da rai kafin a sami abin da ake so, wasu matan suna da wahalar sha'ani, in
suka gan ka da waya ka hau yanar gizo sai su fara ƙirƙiro maka wasu abubuwa, kamar
dai karatun yara ko na su, ko su ce ka watsar da su ka shiga wata saugar, sau
da yawa maza kan zaci cewa kishi ne, wata ƙila tana zaton cewa yana hira
da wasu ne, sai ya yi watsi da ita, alhali ita tana neman hankalinsa ne gaba
daya, in za mu lura wata ko talabijin kake kallo ka riƙa haduwa da irin waɗannan tsirfaffakin kenan, idan
ka fahimci yadda za ka shawo hankalinta yana da kyau, don dai a dawo da
nashadin cikin gida. j) Yakan zama wajibi kuma maigida ya dan riƙa yaba wa uwargida kan ayyukan
da take yi a cikin gida, ba shakka abubuwa ne da suka zama wajibi a kanta, amma
tana da buƙatar a riƙa yaba ma ta, wata ko kwalliya
ta yi, ko lalle, ko kitso tana son ta ji ra'ayin maigidanta a kai, in za mu
lura mace ba ta son kashe kudinta, lura da ƙarancin hanyoyin samo shi, amma
in za ka yi maganar gyaran kai, ko nawa ne za ta iya kashewa, don dai kawai ta
burge maigida, sabo da wannan shi ma ya kamata ya nuna gamsuwarsa, in ta dan yi
kuskuren da ba ta saba yi ba ya dan daga ma ta ƙafa, ya tuna ƙoƙarin da take yi daga lokaci
zuwa lokaci. k) Lokacin da wasu abubuwa da suka shafi gida suka taso, a kanta
ne ko shi ko yara, ya kamata ya saurare ta tukun ya ji ra'ayinta, in bai yi
masa ba to kar ya musanta kai tsaye, ko ya ƙaryata, ko kuma ya nuna ba ta
da tunani, ya yi ƙoƙarin gamsar da ita ne da wani ra'ayin da yake ganin shi ya fi
dacewa, lamurran da suka shafi gida da zumunta, in dai aka sami mace ta gari to
ta fi kowa gwanancewa wajen tafiyar da su, in mutum ya fahimci cewa iyalinsa
tana da matsala da uwayensa ko 'yan uwansa kar ya taba yarda matsalar ta ci
gaba, ya yi ƙoƙari ne ya gano asalin matsalar, kuma ya magance ta, kar ya aibanta
matarsa a gabansu, kar kuma ya goyi bayanta alhali suna wurin, ya dage wajen
kyautata tsakaninsu.
Ta É“angaren shugabanci kuwa, ba ja
maigida shi ne jagora, kuma ba a samun jagorancin sarakuna biyu a kan lardi
daya, kuma suna yin aiki iri guda, ƙarshe sai dai a haifi dan da
bai da idanu, amma in har ya bar gidan to uwargidansa ita ce shugaba har sai ya
dawo, to in dai zai riƙe shugabanci bari mu ga
abubuwan da suka lazimce shi:- a) Shi ne mai riƙe da linzamin gidansa, mai
sakawa a yi ko ya ja linzamin a dakata, ya yi ƙoƙarin sanin kowa da yake ƙarƙashinsa, kuma ya riƙa bincike in kowa yana samun
abin da yake buƙata. b) Ciyarwa da shayarwa na iyali, 'ya'ya da uwaye abu ce da
Allah SW Ya daura a wuyar maigida, don haka ya riƙa kallon wanda ya sanya ta a
uwarsa, kar ya riƙa kallon wanda yake kyautata masa din, wani lokacin in iyali suka
munana wa maigida sai ka ga yana ƙoƙarin daukar mataki, ta wajen ƙuntata wa wanda yake ci a ƙarƙashinsa, wani lokaci ma in yana
fushi da matarsa, hatta 'ya'yansa da duk mai ci a ƙarƙashinsa yana iya aukawa cikin
matsalar da bai ji ba bai gani ba, dole a riƙa jin tsoron Allah, ba horo da ƙuntata abin da Allah SW ya yi
umurni da a kyautata ba. c) Sanin yadda za a riƙe gida a muslunce shi ne babban
manhajin samar da yalwataccen gida cikin farin ciki da annushuwa, Annabi SAW ya
zauna da mace guda, shekarunsa Talatin da wani abu da aure, ya kwashe mafi
yawancin shekarunsa ne da mace guda, wato Khadija RA, ya yi sama da shekara 20
tare da ita har sai da ta rasu, to ya mu'amallarsa da ita? In kuma kana da mata
ne daga biyu zuwa sama waiwaya ka ga rayuwarsa da matansa, shi a matsayinsa na
Annabi ya ajiye mata tara a lokaci guda, yaya ya zauna da su? Tabbas akwai
ababan koyi a wurinsa, don ya auri wace ta haife shi (in maganar ta inganta) ya
auri yarinya danya sharaf, kuma kowacce ta fi son sa sama da kowa. A nan zan
dakata. Sai mun haÉ—u a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.