Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 29)
Baban Manar Alƙasim
2) Fadin mace ta gari kowa ya
saba da shi, kuma kowa ya san kalmar, sai dai wajen tantance mace ta garin shi
ne wata ƙila zai iya zama matsala, mace duk lokacin da aka ce ma ta matar
aure ana sa rai da ganin wasu abubuwa tare da ita, kamar ƙoƙarin kare kanta (wannan ya hada
kyawunta, muryarta, da duk wata sha'awar da za ta iya motsa wa wani namiji),
sai biyayya kan abin da bai saba wa addini ba, Ƙur'ani ya bayyana cewa ba a
halicci aljani da mutum ba sai don bautar Allah, a wata aya kuma Allah SW yana
cewa daga cikin ayoyinsa ne ya halitta mace don mijinta ya natsu da ita, kenan
hidimar miji ba bisa fahimtà r waɗannan ayoyin ibada ce.
Abu ne mai sauƙi a ce mace ta shirya za ta yi
wani abu, sai namiji shi kuma ya zo da na sa daban, a nan ya zama dole ta
girmama ra'ayinsa, ta ma sayar da ranta don kubutar da gidanta, kamar dai yadda
shi ma maigidan yake yi, kuma ko ba mu fadi ba ba inda mace take da sakakkiyar
'yanci kamar gidan mijinta, wace ba ta fahimci maganar ba ta tuntubi matar da
aka sake ta ta koma gidan iyayenta, yanzu bari mu duba abubuwan da suka lazimci
uwargida ta ƙwarai a dakin mijinta.
a) Mace ta ƙwarai takan sifantu da waɗannan sifofin ne: Ƙanƙan da kai, hikima wurin magana
da aiki, wadatar zuci da rashin kwadayi, taƙaita yawan ba ni-ba ni, amincewa
da abin da maigida ya kawo da rashin kallon maƙwabta ko wasu masu gidan,
yawaita godiya ga duk abin da ya kawo, babba ne shi ko ƙarami da rashin rainako, sai
kuma ba shi haƙuri ga duk wani kuskure da ta yi, ko ya ce ta yi, yalwatuwar mace
da waÉ—annan abubuwan takan sa
zuciyoyi guda biyu su zama daya, a duk lokacin da mace ta siye zuciyar namiji,
ba tausayi ba, komai take so za ta iya samu, babban ƙarfin mace shi ne ta yi ƙoƙarin siyan zuciyar namiji, in
har ta mallaka to ta bar shi kawai, rauninta a kowani lokaci yakan ƙara ma ta matsayi ne da ƙima a cikin zuciyarsa.
b) Wani daga cikin mahimman
abubuwa shi ne mace ta girmama 'yan uwan mijinta, ta dauki uwayensa tamkar na
ta, kar ta yarda ta sami wani bambanci a tsakaninta da su, in 'yan uwanta suka
hadu da na mijinta a lokaci guda ta gabatar da buƙatun 'yan uwan mijinta a kan na
ta, ta yi ƙoƙari ta mallaki zuciyoyinsu har su riƙa jin cewa ita ta su ce gaba
daya, ta yadda in za su roƙi wani abu za su biyo ta
hannunta, in ta kwana biyu ba ta gan su ba ta yi bikonsu, da haka maigidanta
zai sake da ita game da 'yan uwansa, galibin masu gida ba su cika yi wa mata
maganar 'yan uwansu da uwayensu ba, amma wannan ba ya nufin ba su san abin da
yake faruwa ba. c) Mata ne ko 'yan mata dole su san cewa Allah SW ya halicci
Annabi Adamu AS ne shi kadai, lokacin da ya riƙa fama da kadaici, kuma sifar
halittar kamar yadda ya yi ta tana buƙatar mai sanyaya ma ta, sai ya
halitta ma ta mace, ya yi ma ta duk abubuwan da namijin yake buƙata, kenan rayuwar kowani
namiji ba tare da mace ba tauyayyiya ce, ko da kuwa shi namijin ya yi
farfagandar cewa yana jin dadi, idan mace ta gane haka ina ganin ta sami kashi
26% na sanin yadda za ta bullo wa namiji.
Namiji yana buƙatar kwalliyarta ko da yana
nuna cewa bai damu da ita ba, in ma ba ta yi zai kalli ta wata don an yi masa
abin da zai buƙaci ganin, haka yana da buƙatar jin muryarta masamman
tattausar, shi ya sa nan da nan Ƙur'ani ya jawo hankulan maza da
kar su ƙura wa matar da ba ta su ba ido, ya kuma hana mata bayyana ado da
kwalliyarsu, ya hana su siriranta murya wajen magana sabo da tasirinta a wurin
namiji, kenan duk waÉ—annan in mace ta daure su da
girmamawa gami da biyayya to ta gama gyarar gidanta, malamina yake cewa: In ka
ga mace tana kukan bushewar namiji ta ga dama ne, tun da ga ruwa a hannunta sai
ta jiƙa shi. Mafi yawan maza masamman wadan da suka kai shekaru 35 ba su
shaƙu da mace ba, sai kwatsam suka ji suna son aure, galibi za ka
taras sha'awa ce a gabansu sama da komai, in mace ta yi dace da irinsu tana
fuskantar abu 3, mannewa da ita kowani lokaci da buƙatarta, jin cewa ta fi masa
komai a lokacin, yanzu ya sami 'yanci ba kamar da ba, babban abin da yake buƙata shi ne ya yi ido biyu da
ita, ko ya ga suna 'yan wasanni, a irin wannan lokacin sai ta bude masa duniya
gaba daya yadda zai tabbatar da cewa rayuwarsa ta baya ba komai ba ce sai
wahala, kuma yanzu ne zai shiga sabuwar rayuwa wace take cike da soyayya da ƙauna, kuma komai yake so zai
samu cikin sauƙi. Ta wajen ƙaunarta da shi, da yi masa
hidima cikin tausayi da son yin aikin, za ta samo shi a hannunta, zai tabbatar
da cewa kintsuwarsa fa ba za ta taba yuwuwa ba in ba da sanya hannunta ba, in
ya saba da haka to za ka ga tsoron rabuwa da shi ya kurdada zuciyarsa, duk
lokacin da ya yi ma ta abin da ya baƙanta ma ta rai za ka ga yana ƙoƙarin neman yadda za su shirya,
to in dai mace ta gano cewa matsayinta a wurin mijinta ya kai haka to ƙarawa za ta yi ba kuma ta bari
ba, soyayyaya kamar imani ce, tana ƙaruwa da yawan aiki ne, ta kuma
ragu da sakaci, in ta wofintar da abin da take yi wai don ta sami zuciyar
namiji ta shi guda zai yi ma ta abin da ba ta zata ba.
Don isa zuwa ga zuciyar namiji
cikin sauƙi, akwai buƙatar kula da waɗannan abubuwa:- a) Ta tabbatar
alaƙarta da Ubangijinta mai kyau ce, wannan zai sa alaƙarta da maigidanta ta ƙara kyau, in ta sami wannan to
alaƙarta da zuciyarta za ta gyaru, sai ka same ta cikin farin ciki da
annushwa a kowani lokaci, gida ya fara gyaruwa kenan. b) Maza sun bambanta,
kwalliyar da wani yake so wani sam ba ta dame shi ba, mace sabo da yau da
kullum takan iya ganewa ko namiji yana son nau'i kaza na adonta ko ba ya so,
misali lalle, wani bai damu da shi ba, wani zai ce shi ja yake so, wani kuma baƙi wani ma dyes, a hirata da
wata gwana a fannin ta ce: Kyawun lalle a wajen mace ya dogara ne da yanayin
hannunta da ƙafarta, da kuma kalar fatarta, kyawunsa kuma ga namiji ya taƙaita ne da yadda yake so, da
kuma irin kalar da yake sha'awa, haka tozali, akwai wasu wuraren da samsam ba
sa sanya tozali a idanunsu, mace don ta burge namiji sai ta lura da abin da
yake buƙata.
c) Sai kuma ɓangaren gyaran gida, ya bayinki yake? Me kike yi na ganin kin ƙawata shi? Kin kuwa ƙawata kicin dinki yadda ba za a raina miki ba? Ya falonki yake? Ya kika ƙawata makwancinki? Ana buƙatar amsoshin waɗannan tambayoyin su ba da yadda za ki burge maigidanki ne idan ya gani, hatta daki da irin turaren da yake buƙata, akwai na fesawa akwai na hayaƙi, na taba maƙwabtaka da wani balarabe, yau da kullum ya sa nakan gane ya dawo gida ko ba shi a garin, sabo da irin turaren wutar da ake kunna masa. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.