Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 21)
Baban Manar Alƙasim
Maganar kallon wace za ka nema,
ko ita ta san wanda zai aure ta abu ne mai matuƙar mahimmanci, Annabi SAW ma ya
kwadaitar a kan haka, kenan wannan ba wata matsala ba ce, to amma me ya sa wasu
'yammatan ba sa sanin wadan da za su aura sai dab da daura auren? Wani dalili
ne yake sa 'yammata suke zuw ga saurayi da niƙabi a ranar farko, bayan
bangajejen hijabin da ya sauka har ƙasa ga safar hannu da ta ƙafa? Wai gaskiya ne saurayi
yana da damar kallon ko'ina a jikin budurwa kafin ya fara nemanta? Ya zancen
shi saurayin, shi ma sai ta ga ko'ina a jikinsa kafin ta amince da soyayyarsa? Waɗannan mas'alolin nake so mu dan
bincika su gwargwadon fahimta. To da yake aure al'amari ne mai matuƙar mahimmanci, wanda yake da
alaƙa ta kai tsaye da dangantaka, ciyarwa, gado da wasu abubuwa da
suka shafi rayuwar aure, kamar dai jin dadin wasa da juna, kallo da saduwa, ya
zama dole kenan a tantance kafin a shaƙu, in da a ce auren holewa
wane, ba wata matsala, saduwa ce kawai kamar yadda sauran dabbobi suke yi in
sha'awarsu ta motsa, sannan abin da ake nema kowace mace tana da shi, kuma iri
daya ne, kowa ma sai mutum ya dauka in ya gama biyan buƙatarsa ta wuce, ba wata matsala
tunda zina ce, aure sam ba haka yake ba.
Na taba yin wani aboki da ya riƙa kwasan wata yarinya, sun yi
shekaru yana mu'amalla da ita, sai na yi niyyar sauya masa tunani da cewa, da
ya aure ta kawai, don auren yana da fa'idoji da yawa: 1) Zai hana ta yin zina
da kowa, za ta komo ta zama saliha, yana da lada. 2) Zai daina samun zunubin
zina ya koma samun ladar saduwa. 3) Za ta fara samar da diyoyin da muslunci zai
yi alfahari da su. 4) Za a daina yi masa kallon mazinaci kuma mutumin banza.
Sai gogan na ka ya ce shi sam ba zai iya mai da mazinaciya uwar 'ya'yansa ba,
na dai gaza yin haƙuri na ce "To ba da kai take yi ba, da wa take yi?" Ya
kafe kan cewa shi tsarkakakkiyar yarinya yake so ba wace yara suka hole da ita
ba, -ikon Allah- idan tunanin kowa ya zama neman tsarkakakkiyar yarinya wace za
ta zama lafiyayyen irin da zai ba da yabanya mai kyau, to ya zama dole a tantance
abubuwa da dama, lafiyarta, kyawun da ya bayyana da wanda ya boyu, da dai
sauran abubuwan da suka kamata. Kuma ya zama dole kowanne cikin ma'aurata ya
san komai dangane da wanda zai aura tun kafin a kai ga daura auren, shi namijin
ya yi bincike game da ita da irin tarbiyar da ta samu, ita ma kafin ta amsa
masa ta tambayi uwayenta, masamman mahaifinta kamin a je ga shaƙuwa, uwayen za su san sa, su
san halayyansa ta wurin abokansa da maƙwabtansa, da ma wadan da yake
mu'amalla da su, ta nan ba a yi wa aure shigar burtu ba kenan, rayuwa ce ta
dindindin mai ci gaba har lokacin da dayansu zai koma ga mahalicci ko su
dukansu biyun.
Galibi hanyoyin da muke bi
wajen zaben mace sun taƙaita ne ga kyawun sura, in dai
ita fara ce kyakkyawa shi kenan ta yi, wani abin da ya shafi mutunci da kyawun
dabi'a kuma sai daga baya a bincika, sau da yawa binciken ma bai da wani
amfani, tun da ba wani abin da za a canja, wannan dalilin ne ma ya sa macen da
ta fito baƙa sai ta nemi canja launi ko za ta sami shiga, su ma matan sukan
dauki sulalla a matsayin hanyoyin yarda da saurayi, shi ma sai ya fara ƙoƙarin gamsar da ita da ƙarairayi daban-daban na kudi,
sutura, sana'a da hurdodi kala-kala ko za ta amince, ba a neman aure da
yaudara, akwai buƙatar tantancewa. Wannan ya sa Shari'a take ganin wajibcin tantance
'yammata da samari, ta yadda in mutum yana son aure dole ya neme ta daga hannun
uwayenta, in kuma ya ƙi zuwa to ba ya son a tantance
shi ne, bai kamata budurwa ta yarda ta fara hira da saurayi ba har sai ta jira sakamako
daga mahaifinta, akwai abubuwa da dama da mahaifin zai duba cikinsu harda aƙida, al'ada, dabi'a, ilimi,
lafiya da mu'amalla, ita yarinya abu daya kawai take dubawa, ko dai ya yi ma ta
ko bai yi ba, irin wannan wautar da 'yammata suke yi na kwashe-kwashe ne yake
sa wa wata take auren wanda zai tilasta ta tafiya daga Kano har Kaduna a ƙasa, in kika ji ya ce ba zai
iya zuwa wurin babanki ba to ki ja layi. A addinin muslunci dole ne a nemi
yardar uwayen yara tukun don aure ba tare da nemansu ciki ba saba wa addini ne,
Allah SW yana cewa: {فانكحوا هن بإذن أهلهن} “Ku Aure Su Bisa Amincewar
Ahalinsu”.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.