Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 22)
Baban Manar Alƙasim
Lura da inda ya dace mutum ya
miƙa diyarsa shehin malami Algazali RL yake cewa a cikin Ihya'ul
Islam: Lura ta ƙarshe ga yarinyar ita ce ma fi dacewa, domin hidimar aure yakan
maishe ta baiwa, ba yadda za ta yi ta kauce masa, ga shi kuma maigidan yana da
damar yin saki a kowani lokaci, in mutum ya aurar da 'yarsa ga azzalimi, ko
fasiƙi, ko dan bidi'a, ko mashayi, haƙiƙa ya yi wa addininsa illa, ya
kuma fada cikin fushin Allah AW sabo da yanke zumuntarta da kuma mummunan
zabinsa. Da wannan dole a nemo ma ta miji na ƙwarai, mace mutuncin namiji ce,
wajibi ne mutum ya tsare mutuncinsa, kamar yadda yake tsare dukiyarsa, mai
hankali shi ne yake yi wa 'ya'yansa mata tattalin inda za su zauna, da irin
mazan da za ta yi mu'amalla da su, a ƙalla dai in aka ce "Wane
ne sirikinka" ba zai damu ba, koda yake mu a wajemmu babban abin kunya ne
ka ce wa mutum "Ga 'yata ko za ka aura?"
Umar bnl Khattab RA da haibarsa
da matsayinsa a duniyar muslunci, ya ajiye komai ya tallata wa manyan sahabban
Annabi SAW diyarsa, ba faduwar girmansa ya duba ba, darajar wadan da ya je
wurinsu ya kalla, a ƙarshe dai Annabi SAW ya aure ta. Yanzu dai bari mu gani, wace mace
ce ya kamata a nema? 1) Ya zama dole a nisanci wace take ƙarƙashin wani, ba a neman matar
aure, shi ya sa nake ganin hatta hanyoyin sadarwa na zamanin nan ana mugun
kwabawa a ciki, don matar aure takan saki jiki da wasu mazan ta yi ta hira da
su, har sha'awa ta gindaya tsakani, dole a guji fushin Allah, macen da take ƙarƙashin wani ta haramta ga wani ƙato matuƙar tana cikin wannan halin, a
bayyane yake Allah SW ya hana wace take iddar wani mamaci ta yi zancen aure da
wani, har sai ta gama idda, to ina ga wace take ƙarƙashinsa kuma yana da rai? 2) Ta
biyun ita ce wace muka fada, wato wace mijinta ya sake ta, ko wace ya mutu ya
bar ta, matuƙar suna cikin idda bai halasta wani ya neme ta ba, ina da wani
babban lekcara na ji shi yana gunaguni kwanaki, wai wata da yake bala'in son ta
ta fito daga gidan miji, wai ya dan yi irin kawaicin addini dinnan har ta gama
idda, kawai sai ya ji wani ya shiga gabansa, ya zagi saurayin ba kadan ba, ya
fadi rashin dacewarsa da bazawarar, da sauran maganganu irin na kishi, tabbas
ba a neman mace a cikin idda, kamar yadda ba a ziga mace ta rabu da maigidanta
don a aure ta, Annabi SAW ya la'anci mai yin haka. 3) Ta ƙarshe ita ce wace wani ya fara
nemanta, a muslunci in dai wani ya fara neman aure, to bai halasta ba wani ya
shiga, irin wannan kuskuren da yawammu muna fadawa ciki, kuma kowa yana da na
sa kason gwargwadon hali.
i) Iyayen yarinya suna sane da
cewa diyarsu tana da saurayi amma suka zuba ma ta ido don ta yi abin da ta ga
dama, ta kawo musu kudi. ii) Yarinya kwadayi ya yi ma ta yawa, wani lokaci ba
ta son mutum amma ba za ta iya haƙuri da abin hannunsa ba, sai ta
riƙa ririta shi kafin wani ya zo. iii) Sai kuma mu ( ko na ce su )
samari, da gangan muke shiga neman yarinya bayan muna sane da cewa tana da
saurayi kuma ta shaƙu da shi, sau da yawa ma sai an kwashi dauki ba dadi da yarinyar
kafin a fara magana da ita, na taba raka wani sai iyayen suka ce tana da
saurayi amma ita mace allura ce a cikin ruwa, mai rabo ne ke dauka, ko tana da
saurayi bai nufin shi ba zai aura ba tun da har ba a daura auren ba, to ko uwayen
yarinyar ba su fadi wannan ba dama abin da yake cikin ƙwaƙwalwarmu kenan, sai dai yanzu
alhamdu lillahi da muka fara zuwa makaranta, wasu abubuwan mun san ba kyau mun
bari, bai dace ba wani ya fara neman aure kai ma ka je ka shiga. Duk da haka fa
ba laifi in mace tana idda misali iddar rabuwa kwata-kwata ko ta mutuwa mutum
ya dan yi shagube, kamar ka ce "Wance ashe abin da ya faru kenan? Gaskiya
mace kamarki bai dace a bar ki da wani abu a zuciya ba!"
Ko namiji zai iya gano irin
wannan to bare mace, masamman in haka ya faru sau biyu ko sau uku, na taba jin
wai wani ya dauki yaron wata mata yana masa wasa yana cewa "Ina ma a ce na
zama babanka!" Uwar tana kallon su tana murmushi, saƙon dai ya kai, sai dai dole a
ji tsoron Allah, neman mace a cikin idda abu ne mai matuƙar hatsari tunda Allah SW da
kanSa Ya haramta haka.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.