Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 01)

    Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  01)

    Baban Manar Alƙasim

    Zai yi matuÆ™ar wahala mutum ya iya tantance haÆ™iÆ™anin ma'anar soyayya, don takan canja ta dauki surori daban-daban da launuka mabambanta gwargwadon mutanen da suke yin ta, akwai buÆ™atar kallon zamani: Ba dole ba ne soyayyar da aka yi ta a shekara 50 ta zama ita ake yi a yau, Wuri: Irin soyayyar da ake yi a Æ™asar Turai takan bambanta da wace Larabawa da mu baÆ™aÆ™e muke yi. Shekara: Manyan mutane da matasan da suke tasowa kowa da yadda yake nuna Æ™aunarsa ga masoyinsa, dattijo ba zai sauko ya zama yaro Æ™arami ba, ba ruwan soyayya da tsufa, amma akwai Æ™aruwar hankali da sanin ya-kamata, Wadata da rashi: In mai wadata zai nuna Æ™aunarsa ga masoyiyarsa yana da hanyoyin da yake bi, masamman wajen yin amfani da abin da yake hannunsa wajen zaben inda za a je, da inda za a zauna, da abin da za a ci. Aure: Akwai cikakken 'yanci wajen yin amfani da duk wasu lafazozi, da yin aiki da duk wata gaba don nuna soyayya, ga cikakkiyar hidima don jin dadin masoyi, wannan bai samuwa a samartaka zalla ba tare da aure ba, Ilimi da jahilci: Wanda ya yi karatu ya hadu da jama'a daban-daban masu sifar rayuwa mabambanta gami da cakuda da fahimtar Turawa, dole tsarin soyayyarsa da mace ya bambanta da wanda bai je makaranta ba, to kafin mutum ya tantance ma'anar soyayya yana da buÆ™atar ya kalli Æ™usurwoyi da dama, gami da nazari kan bambance-bambancen matattaran jama'a da addinansu. 

    Annabi SAW yana cewa: Dayanku ba zai yi imani ba har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa. Haka
    ƙauna take, duk wani mai yin magana a kan soyayya za ka ji ya ƙare kan musayar ƙauna ta kowace sifa, in mace za ta fito da zuciyarta gaba daya ta danƙa wa namiji, to lallai akwai buƙatar shi ma ya yanke hannayensa ya miƙa ma ta, soyayya a taƙaice hidima ce ta zuciya da sauran gabobi ba tare da sauraron godiya ko tukwici ba, aiki take sanyawa tuƙuru na taimakawa, tausayawa, tausasawa da ba da kariya, kenan ba kamar yadda ake rayawa cewa tana hana ganin laifi ba, takan yi ƙoƙarin maganin laifin ne kafin ya auku, in ya bayyana kuma ta yi ƙoƙarin gyarawa ba lullubewa ba. Ba yadda za a yi soyayya ta zama wata hanya ta biyan buƙatar wani shi kadai, ko ta taƙaitu da amfanuwa da abin da yake hannun wani, shi ya sa ma Annabi SAW ya ce: Ka guji abin hannun mutane sai su ma su so ka. In ƙauna ta taƙaita da zuciya sai ta koma sha'awa, wace take kamar wutar kara mai balbala da macewa a dan lokaci kadan, shi ya sa in mutum ya yi nazari mai zurfi zai fahimci shawarar da Annabi SAW ya bai wa masoya wajen zaben abokin rayuwa, sai ya lissafo abubuwan da galibi su suke daukar hankalin mutum wajen zaben abokin rayuwa. In mace tana da dukiya tabbas za a yi sha'awar aurenta don abin hannunta, haka in mutum yana da hali bai rasa samun wace zai zauna da ita komai muninsa, kenan zancen kudi ake yi, ba kuma hanyar da za a fassara kwadayi da soyayya, don zancen ya kasu biyu, ko dai ƙaunar mutum ko ƙaunar abin abin hannunsa, in dai za a yi zancen ƙaunar mutum to ko kadan ba za a duba cewa yana da hali ko bai da shi ba, bare a tambaye shi aikinsa da irin gidan da zai zauna, da matsayin danginsa a gwamnatance, ƙauna tana tsakanin zuciya ne da gabobi, ba ta ƙetare zuwa sutura ba bare a yi maganar aljuhu. In mutum zai nemi mace mai arziƙi, to tun farko kar ya yi zancen musayar motsin zuciya, ko ta yi masa hidimar yau da kullum, bare kuma 'yan uwansa gami da iyaye, yana iya miƙa wuyarsa in bai da buƙatar komai daga gare ta, a nan kuma ba mai iya kawo zancen soyayya, haka ko shi namiji in dai za a gwamatse shi don abin hannunsa shi kansa ya sani, zai yi wahala ya manta wahalhalun da ya yi kamin ya mallake ta, to duk wanda bai wuce ga-shi ba, to lallai bai fi ƙarfin wulaƙanci ba, da yawa wasu sai dai su turo mata abubuwan sawwaƙe rayuwa, ko su ajiye saduwar dare a matsayin hanyar nuna soyayya, tabbas waɗannan sun yi hidimar badawa, amma zuciya ba ta yi aiki ba.

    Daga yanzu za mu fara tunanin ko kallo daya zai iya sanyawa ka
    ƙaunaci mutum, ka iya kasadar miƙa masa rayuwarka har abada, ka ba shi amanar jin dadinka na dindindin, da sakankancewa da cewa ba zai cutar da kai ba, kuma ba zai yarda da duk wani abin da zai cutar da kai ba ƙarami ne shi ko babba, ka tabbatar da cewa komai kake bida na duniya da shiriyar lahira za ka iya samu a hannunsa, tabbas daga mace ta yi ado ba za a iya gane hakan zai samu ba, haka daga namiji ya sami kudi ba zai yuwu a sakar masa jiki ba. Hanyoyin da za a bi don cin ma soyayya ta gaskiya, da samun abokin rayuwa na ƙwarai, da juya tunanin masoyi gami da toshe barakar da take fatattakar alaƙoƙin masoya da ma'aurata su ne za su zama mana tafarki a wannan sabon shirin da yardar Allah. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.