Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 02)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  02)

Baban Manar Alƙasim

Soyayya ta gaskiya tana nufin saduwa ne da juna a jiki da zuciya, ta yadda masoyi zai yi ta fatar a jingina shi da masoyinsa, in a ka ce wane masoyinka ne, dadi za ka ji ko da ma tsokanarka aka yi, sam ba za ka ji zafi ba bare kuma ka hasala, don an kai matsayin da kake jin masoyinka tamkar rabin jikinka, ba ka ƙaunar baƙin cikinsa kamar yadda ba ka fatar damuwarsa, lokacinka, kudinka, hidimarka, jikinka da duk wani abu da ka mallaka na ka ne matuƙar bai buƙata ba, ba ka damu ka sha madaci ba matuƙar shi zai ji zaƙin zuma, kuma za ka iya yin kuka don dai ka ga dariyarsa.

Masoyi shiri ake yi masa na taimako ta kowace sifa, ta yadda za ka gyara komai na ka dominsa, sannan ka yi tattalinsa da 'ya'yansa da duk wanda ya jibance shi, ka ƙarfafa zumuntarsa, ka kare mutuncinsa da sunansa, ka tsaya tsakaninsa da duk abin da zai iya jefa shi cikin damuwa ko tashin hankali, ka kwadaitar da shi a kan duk wani abu da addini ya kwadaitar, ko ya wajabta a yi, ba shakka wannan abu ne mai tsada, wanda yake buƙatar kula da shiri na tsawon lokaci, ba yadda za a yi daga kallo daya a sami lamunin komai, sannan yawan zama da namiji ko mace don hira, ko adon mace da abin hannun namiji ba su suke ba da wannan amincin ba, binciken dabi'ar mutum da tarbiyya ta ƙwarai su suke tabbatar da dauwamammiyar soyayya. In don mu kasa nau'o'in soyayya da ƙauna ne, haƙiƙa za mu iya kasawa har gida Bakwai, wasu sukan taru wa mutum guda, sai ka ga ya iya musayar soyayya kamar yadda ake buƙata, duk yadda aka rasa wani sai ka ga soyayyar ta ragu, kenan kowa bai rasa ƙauna da soyayya a tare da shi, sai dai kuma da fuskar da yake fassarawa ne, in abokin soyayyar ya ga bai samun damar yin musaya ta daya daga cikin bangarorinta sai ka ga ya damu, shi ma sai ya sami rauni ta wasu bangarorin.

Daga cikin rabe-raben soyayya akwai:- 1) Ƙauna ta sha'awa: Wannan tana iya samuwa ne daga kallon fari, tsarin halitta, ko kyawun ado da iya wanka, ko shaharar namiji da abin hannunsa, ko ma iya zance da lallaba, galibin irin wannan ƙaunar ana ganinta a fima-fimai da sauran littafan soyayya, takan yi ƙarfin da ba a taba zato ba, ta burge kowa da kowa, masamman ta fuskar yadda ake gudanar da ita, sai dai da zarar an kawar da sha'awar shi kenan ta tafi, sai kuma zaman haƙuri, irin wannan soyayyar ita ce iyayemmu suke tsokaci a kai da cewa: Da zarar an yi aure ta ƙare sai kuma zaman haƙuri. 2) Wata soyayyar tabbas akwaita amma tana da alaƙa ne da haihuwa da ƙaunar zama uwa ko uba, wato dai buƙatar namiji a ce masa baba, ko mace a ce ma ta mama, masamman in tsararraki sun sami gidajensu na kansu, an fara lissafin cewa wane 'ya'yansa kaza, ko wance 'ya'yanta kaza, in irin wannan soyayya ta maƙure mutum takan yi masa illa, domin tana da ƙarfin da za ta sanya shi ya dauki kowani irin mutum, koda bai dace a rayu da shi ba, ita kam ana iya jure ma ta, amma ba dole ba ne a sami musayar motsin rai da faranta wa juna. An yi wasu bayin Allah da suka so junansu amma Allah Bai ba su haihuwa ba, ganin halin da uwargidan ta fara shiga, sai maigidan ya ba da shawarar cewa su auro wata wace za ta hayayyafa musu, amma komai za su kasance kamar yadda suke, Allah ne dai mafi sanin gaskiya, maigidan ya musluntar da wata, ya kuma aura, har ta haifa masa 'ya'ya biyu, sai mai rabo ya raba su, uwargidar ta kwashe 'ya'yan da hujjar cewa ba za a kai musu diyoyi inda babu muslunci ba, a taƙaice dai amaryar ta bar gidan na tsawon lokaci ba ta yi aure ba, kuma tsohon maigidan na ta yake daukar nauyinta.

3) Sai kuma soyayya ta gaskiya, wannan ba ta furuwa lokaci guda, wai daga zarar ka ga mutum shi kenan kuma ya zama masoyi, wai har kana iya fadawa rijiya a dalilin raba ka da shi, ka zagi kowa ka saba wa iyaye a dalilinsa, soyayya ta gaskiya cike take da tsarin da matattara ta shirya, addini kuma ya tanadar, iyaye sukan ba da gagarumar gudummuwa wajen tabbatar da ita, addini kuma ya yi wa mutum seti ya nuna masa abubuwan da suka dace da wadan da dole ya rabu da su don samun natsuwa da dan uwansa masoyi, wannan tarbiyar mutum take sakawa ya gwanance wajen zama tamkar masoyinsa a lokacin da yake gida ko lokacin da baya nan. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments