Ticker

6/recent/ticker-posts

Karya Fure Take Ba Ta ‘Ya’ya: Tsokaci Daga Labaran Dandalin Sada Zumunta Na Zamani (Social Media)

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Ashafa Garba
ashafagarbagusau@gmail.com
Aliyu Mu’azu

Department of Hausa, Federal College of Education, Zaria, Kaduna State, Nigeria

Tsakure

Hanyoyin sada Zumunta na zamani wato (social media), sun kasance wani dandamali na isar da saƙonni da kuma sada zumunci a cikin sauri da kuma sauƙi a tsakanin Hausawa da al’ummu daban-daban da ke fadin duniya. Kasancewar Hausawa kamar sauran al’ummar duniya ne sun samu kansu a wani sabon yanayi na amfani da kafar sadarwa na zamani kamar facebook da watsapp da tuwita da tiktok da sauransu. Hakan ya ba su damar isar da saƙo a cikin sauri ba tare da wata wahala ba. Wajen ganin an cim ma wannan ƙudiri binciken, an waiwaye yadda Bahaushe yake isar da saƙonsa a gargajiyance da kuma sauyen da ya samu a yanzu. Kafin haka za mu dubi ma'anar labarin ƙarya da ma’anar kafofin sadarwa na zamani. Wannan maƙala ta nazarci wasu hanyoyi da kafafen sadarwa na zamani suke bi domin isar da saƙonnin ƙarya a cikin al’ummar Hausawa. A ƙoƙarin ganin an kai gaci a wannan binciken an bi hanyoyin ziyarar ɗakunan ajiye littattafai na jami’o’i da kuma shafukan intanet musamman na BBC Hausa da RFI Hausa da kuma VOA Hausa. Sannan an yi amfani da ra’in alamomin rayuwar al’umma wato (Social Semiotics Theory). Binciken ya gano yadda kafofin sada zumunta na zamani suke yaɗa labaran ƙarya, da kuma hanyoyin da suke bi wajen yaɗa labaran ƙarya da kuma illolin da yaɗa labaran ƙarya suke haifarwa a cikin al’ummar Hausawa.

Fitilun Kalmomi: Ƙarya, Labarai, Dandalin Sada Zumunta

 

 

 

 

 

 

1.0 Gabatarwa

Alal haƙiƙa sha’anin sadarwa musamman a wannan zamani ya yi tasiri ƙwarai, ta fuskoki daban-daban da suka shafi al’ummar Hausawa da ma wasu sauran al’ummu. A al’adance Bahaushe yana da wasu hanyoyin sadarwa waɗanda suka haɗa da magana ta baki da baki, wadda ta haɗa da amfani da sanƙiran gari, shi ne ake umurta da ya zaga gari unguwa-unguwa yana shaida wa jama’a saƙo (Zaruk, 1986, sh 13).

Bayan haka, akwai sadarwa ta amfani da sassan jiki, kamar amfani da kai da fuska da hannu da baki da ido da sauransu. Haka kuma akwai sadarwa ta amfani da wasu kayan kiɗa kamar su: Tambari da Kalangu da Kuge da Kurya da Ƙaho da sauransu, (Umar, 2012, sh 21).

A duniyar yau al’ummar Hausawa sun samu wasu sababbin hanyoyin sadarwa na zamani waɗanda suka shaƙu da su a sanadiyyar ci gaban al’umma, wanda bunƙasar ilimi da fasaha da ƙere-ƙere ya haifar a sassa daban-daban na duniya. Hulɗar Hausawa da wasu al’ummomi na duniya kamar Larabawa da Turawa ya sa Hausawa sun sami wasu sababbin dabarun sadarwa na zamani, waɗanda a yanzu a iya cewa sun mamaye wasu ɓangarori na rayuwar Hausawa.     

 Sai dai kash! A iya cewa ci gaban mai haƙin rijiya ne, domin al’ummar Hausawa tun suna Maguzawa ba su yarda da yin ƙarya ba, yin ƙarya a al’adar Bamaguje wani babban laifi ne wanda yake zubar da mutuncin al’ummar, duk wanda ya yi ƙarya akwai hukunci ko horon da tsafin gidansu zai yi masa. Ƙarya na ɗaya daga cikin munanan ɗabi’un Maguzawa, saboda haka ne ya sa suke kaucewa yin ƙarya a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Haka kuma lokacin da Musulunci ya zo, bai ci karo da al’adar Bahaushe na kyamatar ƙarya ba, hasali ma, Musuluncin ya ƙara jaddada haramcin yin ƙarya, (Abdullahi, 2008: 45).

Kamar yadda aka sani, labarin ƙarya ya girmi kafar yanar gizo wadda a kanta ne aka gina kafofin sada zumunta. Farfaganda da take cike da labaran ƙanzon-kurege sun daɗe ana yaɗa su a ƙarnoni da dama da suka gabata tun kafin zuwan fasahar sadarwa ta yanar gizo. Kasancewar abubuwa da dama na fasaha kan iya zama masu amfani ko kuma su zama matsala gwargwadon yadda mai amfani da su ya sarrafa su.

Labaran ƙarya ba ƙaramar matsala ce ba kuma ta daɗe tana ci wa masu mu'amala da shafukan sada zumunta tuwo a ƙwarya. Abin bakin ciki matsalar ta zama ruwan dare. Misali da za ka shiga dandalin Facebook ka nemi Aljazeera ko BBC Hausa za ka tarar da shafuka da yawa masu waɗannan sunaye alhali guda ɗaya ne kawai na asali. Don haka, abin takaice ne yadda wasu ke mu’amala da waɗannan dandali a matsayin kafafen yaɗa labaran ƙarya maimakon cin moriyar abin da aka gano a kanta.

2.0 Ma’anar Shafukan Sada Zumunta

A mahangar kimiyyar sadarwa ta zamani, idan aka ce (social media) ana nufin dandalin shaƙatawa da yin abota. Kerric (2000) ya bayar da gamammen ta’arifi inda yake cewa “Kalmar Soical Media (SM) da Social Networking Sites (SNSs) da social media Websites (SMWs) na nufin wasu shafuka ko manhajoji da ake amfani da su a yanar gizo, domin sadarwa tsakanin mutane da musayar ra’ayoyi ta hanyar sauti (Voice notes) da hotuna daskararru (Still Images) da masu motsi (Videos) ko rariyar liƙau (Hypertext links).

2.1 Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Shafukan Sada Zumunta

Tun bayan samuwar Telegraph (1792) da Telephone (1876) da Radio (1891) a ƙarni na ashirin (20 Century) bayan samuwa da yaɗuwar manyan kwamfutoci (Super Computers) a 1940s masana kimiyyar na’ura Kwamfuta suka himmatu wajen faɗaɗa nazari da bincike da haɓaka wannan fasaha wadda har ta kai ga rikiɗa da haihuwar fasahar intanet a shekarar 1969. Bayan sadarwa ta Imel 1971. Da farko an fara hirar ga-ni-ga-ka ta Internet Relay Charts (IRC) ne a shekarar 1988.

Haka dai wannan siffa ta ci gaba da yaɗuwa, tare da canza akalar sadarwa. Shafin sada zumunta na farko a tarihi shi ne Six Degrees, wanda aka fara amfani da shi a watan Mayu 1997. Wannan shafi yana bai wa masu ta’ammali da su damar ɗora bayanan rayuwarsu, matakan karatu da sunayen abokansu (Profiles) da kuma yin abota da wasu mutane ta wannan shafi.

Daga nan sai Open Diary a watan Aktoba, 1998 da Live Journal a shekarar 1999 da Ryze a shekarar 2001 da Friendstar a shekarar 2002. Daga nan sai aka ƙirƙiri Blogging, aka samar da shafuka irinsu Myspace a shekarar 2003 da Linkedin a shekarar 2003 da Orkut a shekarar 2004, waɗannan shafuka sun samu shahara da karɓuwa a wancan lokaci.

A farkon ƙarni na 21, an sami bayyanar waɗansu shafukan sada zumunta kamar irinsu, Photobucket a shekarar 2003 da Flicker a shekarar 2004, waɗannan shafuka suna bayar da damar karɓa da tura saƙonnin hotuna. Bayan haka sai kafar tashar yaɗa hotuna masu motsi (Videos) wato YouTube ya kunno kai a shekarar 2005, sai ƙaraminsu babbansu Facebook a shekarar 2004 da majalisan dattijai da mahankalta wato Twitter a shekarar 2005. Waɗannan shafuka guda biyu wato facebook da twitter sun zama wanzazzun shafukan sada zumunta masu dogon zamani da shahara a sararin yanar gizo.

Daga baya an sami shafuka irinsu Bebo a shekarar 2005 da Spotify a shekarar 2006 da Tumblr a shekarar 2007 da WhatsApp a shekarar 2009 da Foursquare a shekarar 2009 da Pinterest a shekarar 2010 da Instagram a shekarar 2010 da marigayi Google+ a shekarar 2011 duk sun fito da irin nasu keɓantattun salo na sadarwa.

A yau waɗannan manhajoji da shafuka sun yi yawan da zai alamta mana abubuwa barkatai za su iya faruwa a wannan ƙarni, da kuma sauran ƙarnuka masu zuwa, musamman Ƙarya” wanda ake nazari a kanta.

 2.2 Ire-Iren Shafukan Sada Zumunta

A matakin farko za a iya kasa shafukan sada zumunta kashi uku, ta fuskar gudummawar da suke bayarwa. Akwai waɗanda suke tura saƙonni da dukkan nau’ukansa (post-based social media) kamar Myspace da Facebook da Twitter. Akwai waɗanda aka gina su a kan karɓa da tura hotuna (Image-based social media) misali Instagram da Snapchat da Tumblr. Akwai kuma waɗanda suke kamar gidajen talabijin (Video-based social media) kamar Vime da Vimeo da Youtube.

Akwai kuma masu keɓantattun manufofi da aka ƙirƙira domin wasu keɓantattun mutane, misali: shafukan da suka keɓanci tambayoyi da amsa a kan komai (Quora), da kuma na ƙwararru (Professionals) kamar Linkedin ɗaliban kimiyya scienceStax, karatu da littattafai goodreads, anobii, librarything, shelfari, wattpad, Weread, akwai wanda ya keɓanci ‘yan kasuwa talkbiznow, na ‘yan baiwa masu ƙwaƙwalwa (talented) ibibo, akwai kuma shaiɗanun shafukan da suke na musamman ga masu LGBT11. Sannan akwai waɗanda sun keɓanta ga wasu ƙasashe kamar wechat ga ‘yan China da Vkontakte (VK) ga ‘yan Russia da kuma Taringa ga ‘yan Latin America da sauransu.

3.0 Ma’anar Ƙarya

A cikin CNHN (2006) an bayyana ma’anar ƙarya da cewa; maganar da ba ta gaskiya ba ce. Shi kuwa Musa (2021) ya bayyana ma’anar ƙarya kamar haka; Ƙarya wata aba ce da mutane suke ƙirƙirarta kamar abu ba a yi ba sai mutum ya ƙirƙira ya faɗa alhali ma ba a san da maganar ba. Haƙika duk wanda yake ƙarya to tabbas duk tsananin gaskiyarsa ba a yarda da shi, saboda baya faɗin gaskiya sai ƙarya. Saboda haka, ƙarya na nufin duk wani zancen da aka ƙaga aka faɗa ba na gaskiya ba shi ne ake nufi da ƙarya.

3.1 Ma'anar Labarin Ƙarya

Labarin ƙarya shi ne duk wani zance da aka furta da fatar baki, ko aka rubuta ko suranta a hotuna ko bidiyo da ba ya da asali ko sahihanci da aka faɗa tare da wata manufa ta kariya ga abu, tallata haja, kambama wani gwarzo ko ɓata sunan wani ko wata da sauran manufofin da mai faɗin labarin ya kunsa a zuciyar sa. Wato ita ƙarya ko ta bayyana kuma ta burge jama’a, to ba za ta tabbata ba, domin kuwa za a gano ta kuma masu yaɗa ta za su kunyata.

4.0 Ra’in Bincike

An ɗora wannan binciken ne a kan ra’in alamomin rayuwar al’umma wata (Social Semeotics Theory). Ra’in nazarin alamomin rayuwar al’umma yana bayyana alamomi na rayuwar al’umma masu matuƙar muhimmanci waɗanda suka shafi zamantakewar al’umma. Ana danganta wannan ra’in da Ferdinand de Saussune (1857-1913).

Ra’in wannan mazhabar ya danganci nazarin ma’ana wato saƙo tare kuma da tantance ayyukan ɗan’adam, musamman hanyoyin fassarawa da ta bayyana siffar maganganun baka da rubuce-rubuce da hotuna da zane-zane na gargajiya da makamantansu.

Kamar yadda wannan binciken yake ƙoƙarin bayyana labaran ƙarya a kafofin sada da zumunta na zamani wato (social media) ta hanyar maganganun baka da rubuce-rubuce da hotuna mai motsi da mara motsi da zane-zane da sauransu. Wannan ra’in ya yi daidai da binciken da ake yi wajen bayyana irin rayuwar da al’umma suke gudanarwa musamman a kafofin sada zumunta.

Fitaccen mabiyin wannan ra’in shi ne Halliday, M.A.K, an haifi shi a shekarar (1925) mashahurin masani ne a nazarin kimiyyar harshe da nazarin rayuwar al’umma, wanda ya rubuta littafi musamman a kan nuna ra’i na mazhaba mai suna Social Semiotic (1978).

Wasu mabiyan wannan ra’in sun haɗa da Robert Hodge (H. 1940) da Gunther Rolt Kress (H. 1940). Waɗannan manazarta sun nazarci alamomin rayuwar al’umma na al’adunsu wato (Cultural Scripts) na maganganunsu wanda suka gina, suka kuma aiwatar ta hanyar kimiyyar harshe, ta haka aka samar da ayyuka da dama.

5.0 Hanyoyin Yaɗa Labaran Ƙarya

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen yaɗa labaran ƙarya a cikin a’umma, amma a wannan takardan an zaɓi hanyoyi guda biyu ne domin gudanar da bincike a kansu kamar haka.

5.1 Hanyoyin Kuskure: Su ne ɗaukar bayani da wata ma'ana a cikin rashin sani daban da abinda wanda ya faɗe ta yake nufi, ko kuma faɗawa tarkon da take sa masu rubutu a shafukan blog ke yi don su sa ka danna rariyar liƙau. Hanyoyin kuskure wajen yaɗa labarin ƙarya na samuwa ne dalilin jahilci ko mummunar fahimta ga abinda aka faɗa. Wannan kashi ya ƙunshi waɗannan kashe-kashe guda uku kamar haka:

5.1.1 Hargitsa Raha: Wannan labari ne da wani zai bayar da manufar raha watau wasa, amma sai mai karatu ya ɗauke shi matsayin gaskiya kuma abin da ya faru kuma sai ya yaɗa shi a matsayin abin da ya faru alhali asalin labarin an ƙirƙira shi ne don ba da dariya. Misali, wasan "April Fool" wadda mutane ke ba da labari ƙirƙirarre mai ɗaukar hankali a cikin watan Afrilu wanda ba gaskiya ba ne , amma sai wasu su ɗauke shi a matsayin gaskiya, kuma su yaɗa ga abokansu. Wani lokacin kuma wani zai ba da labarin a kan wani abu da mutane suke ɗokin ji sai a ƙarshe ya ce "Sai kawai na ji ana tada ni ana cewa "wane wane! Tashi! Ka yi Sallar Asuba, ka makara" watau ke nan duk labarin mafarki ne.

5.1.2 Hargitsa Gatse: Wannan labari ne da ya ginu a kan kuskure gatse a kan abin da yake haƙiƙa. Mutum ne zai rubuta labari don kushe abu a cikin gatse amma sai mai karatu ya ɗauke shi a cikin lafazin rubutun ba tare da la'akari da ma'anarsa ta gatse ba. A turance ana kiran irin wannan rubutu ko magana "sarcasm" wanda adon harshe ne mai ƙarfin gaske sai dai ba kowa ke da kwarewar fahimtarsa ba musamman a nan Nijeriya.

5.1.3 Dogara ga Take: Marubuta musamman 'yan jarida ta takarda ko yanar gizo na amfani da dabarar jan hankali wajen ba da take ga labari don kwaɗaitawa mai karatu shauƙin karanta labarin. Wurin yin haka wani lokacin a kan siffanta abin da ba shi ne ke ƙunshe a cikin gangar labarin ba. Wani lokaci kuwa ma'anar taken na da harshen damo watau ma'ana biyu, ɗaya ta gaskiya, ɗaya kuwa matsayin tarkon kama makaranci. Misali "Several Lives Lost During Sallah-Xmas Celebrations" watau "An Rasa Rayuka da Yawa a Lokacin Bukukuwan Sallah da Kirsimeti". Ma'anar wannan ta asali shi ne an yanka raguna da kaji da sauran dabbobin da ake yankawa don buki amma akwai tarkon kama makaranci inda zai yi zaton an samu rikicin addini har aka samu salwantar rayukan mutane. A cikin irin wannan, dogara ga take yana da matukar hadari don sai mai karatu ya yaɗa labarin da ba shi ne gaskiya ba. A nan ana buƙatar mai karatu ya cire ƙyuya ya karanta uwar labarin gaba daya don samun cikakken bayani da kaucewa yada karya.

5.2 Hanyoyin Ganganci: Waɗannan hanyoyin yaɗa ko ƙirƙira labaran ƙarya ana bin su da gangan kuma tare da manufar da ake son a cimma. Wasu daga cikin hanyoyin ganganci na yaɗa labaran ƙarya su ne kamar haka:

5.2.1 Shigar Burtu: Wannan wata hanya ce ta ɓoye bayani a kan wanda ke Magana, inda mutum zai bude shafin sada zumunta ko karamin shafin yanar gizo da wani suna daban da na shi, da manufar kada a gane ko shi wane ne. Wani lokaci mai yin haka yana ɗaukar sunan wani babba ko tauraro a fagen siyasa ko kasuwanci don yaudarar mutane da sunan ko ɓata masu suna ta hanyar yin magana da yawunsu. Wasu kuma kan yi haka ne domin su ci mutuncin wani abokin hamayya ba tare da an gane su ba.

5.2.2 Ƙarawa Miya Gishiri: Kamar yadda sunan ya nuna, wannan wata hanya ce ta yi wa labari Ƙari a kan ma'ana ko adadin da aka fadi a cikin sahihin labari.

52.3 Murguda Labari: shi ne juya labari da samar da sabuwar ma'ana ga zance wanda asalinsa sahihi ne, amma sai a canja shi da nufin isar da wani sako da ba shi ne asali ba.

5.2.4. Siddabarun Hotuna/Bidiyo: Siddabaru ga hotuna da Bidiyo na ɗaya daga cikin hanyoyin yada labaran ƙarya da su ka yi fice a duniya. Wannan shi ne sarrafa hotuna tsayayyu ko masu motsi don bada sabuwar siffa da isar da saƙon da ya sabawa zahirin gaskiya. Wannan fasaha an fara amfani da shi ne a shekarar 1987 bayan da wasu 'yan uwan juna Thomas Knoll da John Knoll suka ƙirƙiri manhajar kuma suka sayar da lasisin ta ga Kamfanin Adobe System. Wannan fasaha tana taimakawa matuƙa wajen aikin gyaran hotuna ga kafofin yaɗa labarai da dama, amma kuma bara-gurbi kan yi amfani da ita ta mummunar hanya wajen shirya hotuna na ƙarya ko harhaɗa bidiyoyin da aka sauyawa sura ko sauti don yaɗa wata farfaganda ko ɓata sunan wasu mutane.

6.0 Misalan Zahiri A Kan Labaran Ƙarya

Akwai misalai na zahiri da dama a kan labaran ƙarya da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta. Wasu daga cikin su na hotuna ko bidiyo, wasu na rubutu, wasu kuma na rubutu tare da hotunan da aka sauya ko aza su ba muhallin su ba. Misali:

a.      A watan Oktoba shekara ta 2019 an yi ta yaɗa hotunan Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari tare da Ministar Ma’aikatar Lamurran Jinkai Sadiya Umar Faruk da katin gayyatar ɗaurin aurensu a shafukan sada zumunta na facebook da kuma whatsapp. Wannan labarin ƙarya ne kamar yadda tashar BBC Hausa suka ruwaito a ranar 11 ga watan oktoba a shekarar 2019 kamar haka:

 Wannan labarin dai ba a san daga inda ya fito ba, amma zancen da ake ta yi ke nan a shafukan sada zumunta, an ƙirƙiri wani maudu’i mai taken BUSA2019, wato auren Buhari da Sadiya a shekarar 2019. Sai dai BBC ta samu bayanai daga wani makusancin fadar shugaban ƙasar, Kakakin shugaban ƙasa wato Garba Shehu ya musanta wannan labarin a kan cewa shugaba Buhari ba zai ƙara aure ba”.

Saboda haka ne muke ganin cewa wannan labarin ya yi daidai da karin maganar nan da Hausawa suke cewa ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya, domin kuwa wannan ƙaryar ba ta yi ‘ya’ya ba.

b.      A watan Nuwamba na 2019 an samu harin 'yan bindiga masu satar shanu a yankin Gummi, wasu masu tu'ammali da kafofin sada zumunta na Facebook da WhatsApp sun yi amfani da hotunan wasu rikice-rikice da suka faru a wasu wurare wajen wannan labarin inda har suka ɗauko hotunan rikicin Bachama da Fulani a Jihar Taraba suka ɗora a matsayin gawarwakin mutanen yankin Gummi. Wannan labarin ma ƙarya ne kamar yadda wani mazaunin yankin Gummin ya shaida min mai suna Ibrahim Na-Allah, cewa waɗannan hotunan da ake yaɗa wa ba hotunan rikicin yankin Gummi ba ne, kawai ƙarya ce ake ta yaɗawa.

c.       Jubril Assudany ƙirƙirarren suna ne da ya yi fice a kafofin sada zumunta, bayan da shugaban fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu ya ƙirƙiro wani labarin shaci-faɗi a kan samun lafiyar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan dawowar sa daga Ingila jinya, inda yake nuna cewa Shugaban ƙasa Buhari wai ya mutu, an turo madadin sa ne mai suna Jubril Assudany bayan likitoci sun dasa masa wasu ƙwayoyin halitta irin na Buharin tare da koya masa dabi'u irin na sa. Sai dai wannan labarin ba gaskiya ba ne, domin kuwa da kansa shugaba Muhammadu Buharin ya ƙaryata a tashar RFI Hausa, inda suka gabatar da rahoto a ranar 3 ga watan Disamba shekara ta 2018 mai taken Ni ne haƙiƙanin Buharin da Kuka sani, ba Jibril daga Sudan ba, ga labarin kamar haka;

A karon farko, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan jita-jitar da wasu ke yaɗawa kan cewa ba shi ne haƙiƙanin Buharin da aka sani ba. Shugaba Buhari ya ƙaryata bayanan da ke cewa wai shi wani mutum ne mai suna Jibril daga ƙasar Sudan, da aka yiwa gyaran kamanni, kuma aka turo domin ya ci gaba da mulkin Nijeriya, bayan rasuwar Buhari na asali da ya yi rashin lafiya. Shugaban ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Poland.

 Saboda haka ne, muke ganin cewa wannan labarin shi ma ya yi daidai da karin maganar da Hausawa ke cewa ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.

d.     Baccin Ministan Buhari: A watan Fabrairu na 2020 ne Shugaban ƙasa ya ziyarci babban birnin jihar Borno wato Maiduguri inda aka ɗauko hoton sa yana jawabi a tare da shi Ministan tsaro Bashir Salihi Magashi zaune. An yi ta yada hoton da bayanin cewa Ministan tsaron bacci ya ke yi a lokacin da Shugaban ƙasa ke jawabi kuma a kallon farko mai duba zai ga kamar haka ɗin ne, amma a haƙiƙanin gaskiya Ministan ya sunkuyar da kansa ne kawai yana rubuta wani abu akan littafi. Wannan labarin ma ƙarya ce domin da kansa ministan ya ƙaryata labarin a shafinsa na tiwita.

e.      A shekarar 2014 da aka samu ɓarkewa cutar Ebola a Nijeriya bayan wani da ake kira Sawyer ya shigo da ita, wata yarinya da ake kira Adesewa ta rubuta a shafin ta na Facebook cewa shan ruwan gishiri da wanka da su na warkar da shi, wannan kuwa ya saba wa hakikanin gaskiya da ilimin lafiya. Wani abin ban haushi sai da aka samu wasu da yawa sun sha gishirin wasu ma har suka mutu, musamman waɗanda da ma suna da hawan jini, sai ga matar ta fito da bidiyo tana cewa wai da wasa ne take faɗa bayan wani zancen raha da suka yi da ƙawayenta, tana neman gafara bayan 8 ga watan Agusta an samu mutuwar mutum biyu a Jos da kwantar da mutane kimanin 20 akan shan ruwan gishiri kamar yadda Jaridar Thisday da Vanguard bugun 8 ga watan Agusta suka ruwaito.

f.        Alaƙar 5G da cutar Murar Alaƙaƙai ta Covid19: Bayan samun ɓarkewar wannan cutar ta COVID19 a ƙasashen Turai, sai masu yaɗa yasasshiyar magana da kimiyya ƙarya da masu farfagandar ƙyama a kan gogayyar kasuwanci da ƙasar Sin (China) suka fara ƙoƙarin tunzura mutane da da'awar cewa wai tsirkiyar sadarwa ta 5G ce ke haddasa mutuwar mutane amma ana fakewa da COVID19, a wani ƙaulin kuma, wasu na faɗar wai 5G ɗin ke haddasa COVID19. Wannan shafa-labari-shuni ya sa wasu 'yan Birtaniya sun lalata aƙalla turakun 5G guda 20 a ƙasar kamar yadda Jaridar The Guardian ta faɗa a ranar 6 ga watan Afrilu 2020.

7.0 Illolin Yaɗa Labaran Ƙarya

Illolin yaɗa labaran ƙarya na da matuƙar yawa kuma mummunan tasirin su ga al'umma ba ƙarami ba ne. Ga wasu daga cikin illolin:

7.1 Tunzura Jama'a

Mafi yawan boren da ake samu a duniya da tashin hankali na afkuwa ne dalilin ƙarya da yaudara. Misali, yaƙin da George W. Bush ya jagoranta a Iraki tare da zargin wai Shugaba Saddam Hussein ya tara makaman ƙare-dangi har aka samu mutuwar 'yan ƙasar kimanin 600,000 a bisa alƙaluman hukuma, hakan ya faru ne a kan farfagandar ƙarya. Gaskiya ta bayyana bayan da haɗakar jami'an binciken ƙwaƙwaf na Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka su 1,625 sun kwashe shekara biyu suna aikin bincike a wurare 1,700 a cikin ƙasar ba tare da gano makaman ƙare-dangin ba.

Haka lamarin yake a lokacin kisan kiyashi a Rwanda tsakanin Hutu da Tutsi a shekarar 1994. An dasa ƙiyayya ne ta hanyar ƙirƙira ƙarya da juyar da ƙwaƙwalen ƙabilar Hutu a kan su ƙyamaci Tutsi don wai su "baƙi ne da darajar su ba ta wuce ta kyankyaso ba, kuma su makiya".

A nan Nijeriya, ran 23 ga watan Yuni 2018, an ɗora wasu hotuna masu ta da hankali na gawarwakin mata da ƙananan yara da aka sassara da adduna a kai, hotunan da aka kalla fiye da sau 11,000 da ke nuna fasasshen ƙoƙon kai tare da bayanin cewa wai kisan kai ne da Musulmi suka yi wa mutanen Gashish na Filato. Wani abu da zai baka mamaki hotunan da aka yi amfani da su sun fito ne daga Congo-Brazzaville dubban kilomitoci daga Nijeriya kuma kisan ya faru tun 2012.

Bayan yaɗa waɗannan hotuna ne na tunzura fitina, 'yan ƙabilar Berom suka datse hanya suka kashe mutane da dama dalilin hotunan da aka dora a Facebook. Duba labarin a shafin BBC da ke nan:

7.2 Ɓata Suna

Ɓata suna na daga cikin illolin yaɗa labarin ƙarya. A bisa wasu dalillai na saɓani na siyasa, zamantakewa, kasuwanci ko makamantan haka a kan samu wasu mutane suna jifar mutane da wasu miyagun ɗabi'a, yi masu ƙazafi ko yin suka ga abin sana'ar su a kan ƙarya.

7.3 Cutar da Jiki

Yaɗa labaran ƙarya ta hanyar yin kutse ko shiga sharo ba shanu a kan sha'anin lafiya da magunguna na haddasa cuta da mutuwa ga wanda ya ɗauki bayanin a matsayin gaskiya. Idan ba a manta ba, na ba da misali a kan shan gishiri a kan Ebola.

7.4 Cusa Tsoro

Ko shakka babu yaɗa labaran ƙarya a kan sha'anin da ya shafi zamantakewa na kawo fargaba da rashin natsuwa. Da yawa ana ƙara wa miya gishiri a kan wasu matsalolin al'umma bisa dalillai na siyasa wanda wannan na sa fargaba ga jama'a. Misali, na taɓa karanta wani rubutu a Facebook da ke cewa: "Yanzu haka ɓarayi ɗauke da miyagun makamai su ɗari da goma sha biyar sun tunkari gari kaza". Ta yaya mutanen wannan yanki idan suka yi tuntube da wannan labari za su iya bacci? Duk mai tunani zai yi mamaki ace har mai bada wannan labari ya ƙididdige yawan barayin da yake ba da labarinsu.

7.5 Hasarar Dukiya

A duk sa'ada mai yaɗa labarin ƙaraya yaci nasara wajen tunzura jama'a aka samu ɓarkewar fitina da tashin hankali, akwai yiyuwar samun hasarar dukiyoyi kamar yadda misali a kan lalata turakun 5G ya gabata dalilin alaƙanta shi da cutar Corona Virus. A nan Kaduna an sha yaɗa jita-jita a kan ƙarya har ta yi sanadiyar ƙone-ƙone kamar yadda ya taɓa faruwa a ranar Lahadi 28 ga watan Afrilu 2019.

Wannan ya sa Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da al’umma cewa duk wanda aka kama yana yaɗa jita-jitar cewa ana rikici a wani sashe na Kaduna ko yana sanya hotuna ko bidiyo a shafukan sada zumunta wanda za su iya harzuƙa mutane ya tayar da fitina, hukuma za ta kama shi.

Asalin jita-jitar ta samo asali ne a kasuwar Sabo inda wani mutum ya saci takalmi ya gudu inda mutane suka bi shi don su kamo shi. Kawai da ganin ana gudu sai wasu suka yaɗa labarin cewa wai rikici ya ɓarke a Kaduna tsakanin Hausawa da Igbo har an kashe mutane kuma ga hotuna.

7.6 Rarraba Kawuna

Babu ko shakka yaɗa labarai maras tushe ko asali na kawo rarrabuwar kawuna da hargitsa ƙasa da ba maƙiyan ƙasa damar kutse har su dagula al'amurra.

7.7 Ruguza Kasuwanci

Wannan yana faruwa ne ta hanyar yin suka ga hajojin kasuwanci kamar ka ji an ce Maggi da naman jaki ake yin sa, da ire-iren waɗannan.

8.0 Hanyoyin Magance Labaran Ƙarya

Akwai hanyoyi da dama da ake magance labaran ƙarya, amma a wannan aikin za mu yi bayanin hanyoyi ne guda biyu kamar haka.

8.1 Matakan Magance Yaɗa Labaran Ƙarya Ta Hanyar Fasaha

A lokacin da duniya ta fahimci haɗarin yaduwar labaran ƙarya, sai aka fara tursasa wa masana kimiyyar na'ura mai ƙwaƙwalwa da yanar gizo da su ɗauki mataki a kan matsalar. Duk da masu hajojin yanar gizo na ribantuwa a fakaice da irin waɗannan labaran kamar yadda aka sani kuma ake faɗa "Ƙarya na tafiyar rabin duniya a lokacin da gaskiya ke sa takalmi". Duk da haka an samu ci gaba ƙwarai wajen tace bayanan da ake ɗorawa a yanar gizo. Misali, mai kafar sada zumunta ta Facebook ya sanar da cewa sun yi haɗin guiwa da mai masu manhajar binciken tabbatar da gaskiya don hana yaɗuwar labarin ƙarya sai dai kammaluwar wannan zai ɗau lokacin saboda sanya wannan fasahar ta yi aiki ga dukkan harsuna.

A bangaren masu ƙirƙira manhajojin komfuta da tarho, akwai wata manhaja da ake kira "Reverse Image Search" da take aiki da kamfanin Google da wasu fitattun rumbunan binciken bayanai watau "Search Engines". Aikin ta shi ne idan ka saukar da ita a wayar hannu misali ta Android daga rumbun manhajoji na "PlayStore" za ka iya tantance sanannun hotuna da aka ɗora a shafin sada zumunta don gane ko sababbi ne da ke da alaƙa da labarin da suka zo da shi ko kuwa an debo su ne daga tsohon labari aka danganta su da faruwar wani abu sabo.

Bugu da ƙari, ana iya tantance sahihancin labari ta hanyar tuntubar kafofi masu ƙima da mutunci waɗanda aka tabbatar da wuya a samu sun yaɗa abin da ba gaskiya ba.

Wani lokaci ana yaɗa magana daga shafin Twitter a Facebook ta hanyar ɗaukar hoton allon waya (screenshot) a ce wane yace kaza kuma ga kwafin hoton. A nan ya zama wajibi a yi taka-tsan-tsan don wani lokacin ana juya maganar da ke kan allon bayan an ɗauke ta, wani lokacin kuma farfajiyar (profile) da aka ɗauko zance ba ta asali ba ce. Abin yi anan shi ne, ka ɗauki adireshin farfajiyar ka tafi shafin Twitter ka nemo ka gani da kan ka kuma idan sananne mutum ne tauraro, to ka yi la'akari da ko akwai hatimin tantancewa a kai kuma adadin masu biyar sa suna da yawa.

9.2 Ta Hanyar Faɗakarwa

Wannan wata hanya ce mai matuƙar muhimmanci. Wannan taron na ɗaya daga cikin hanyoyin faɗakarwa da ke da alfanu wajen daƙile yaɗa labaran ƙarya musamman a kafofin sada zumunta. Abu na gaba shi ne. A yi amfani da malaman adddini wajen faɗakarwa game da illar yaɗa labaran ƙarya. Bayan haka, Hukumomi su ɗauke ɗamarar hukunta duk wanda aka kamashi da laifin yaɗa labaran ƙarya. Sannan kuma, a yi dokoki masu tsanani kuma a yaɗa su.

10.0 Kammalawa

Bisa la’akari da abubuwan da aka gabatar za a tabbatar da cewa lallai shafukan sada zumunta na zamani ana tafka ƙarya a cikinsu, tun daga kan shafin facebook da twitter da whatsApp da tiktok da youtube da sauransu, sai dai ƙaryar tasu fure ta ke ba ta ‘ya’ya, domin kuwa ana bankaɗo ƙaryar tasu, ta hanyar waɗanda ake yi wa ƙarya da kansu su ƙaryata ko makusantansu ko kuma binciken da kafofin yaɗa labarai suke yi a kan sahihancin wannan labarin. Wannan maƙala da aka gabatar ta yi bayani ne a kan ma'anar labarin ƙarya da sigoginsa, manufofinsa, misalansa da illolinsa, hanyoyin magance shi da mahangar addini akan sa a takaice. Muna godiya ga Allah (SWT) bisa samun damar gabatar da wannan muƙala. Allah Ya ba mu ikon kiyayewa, Ya gafarta mana zunubanmu, ya ba mu lafiya da zama lafiya a Nijeriya baki ɗaya.

Manazarta

1.      Abdullahi, S.S (2008)Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye A Kan Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa.” Kundin Digiri Na Uku, Sashin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

2.      BBC Hausa (2020) Gudummuwar Shafukan Sadarwa Na Zamani ga Cigaban Tattalin Arzikin Ƙasa.”

3.      CNHN, (2006) “Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayaro.” Ahmadu Bello University Press. Zaria.

4.      Halliday, M.A.K. (1978) “Language As Social Semeotic: The Social Interpretation of Language And Meaning”. University Park Press. Maryland.

5.      Ibrahim, Z. (2019) Gudummuwar Hanyoyin Sadarwa ga Ci Gaban Ƙasa.” Kundin Digiri Na Ɗaya: Sashin Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Tarayya Gusau.

6.      Ibrahim, M.S. (1982) Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Al’adun Hauwasa”. Kundin Digiri Na biyu: Sashin Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

7.      Musa, S. Z. (2021). Ƙarya A Musulunci”. Takardan Da Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani.

8.      RFI, Hausa. (2018). ”Hanyoyin Magance Labaran Ƙarya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani”.

9.      Umar, M. M. (2012). Nazarin Saƙon GSM A Wayar Salulan Hausawa”. Kundin Digiri Na Biyu, Sashin Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

10.  V.O.A, Hausa. (2018) Illolin Shafukan Sada Zumunta na Zamani”.

11.  Zarruk, R. M. da Wasu (1986) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi Na Ɗaya, Ibadan University Press Zaria.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.026

Post a Comment

0 Comments