Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Yunwa A Waƙoƙin Hausa Na Noma

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.


Yahaya Idris
Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto, Nigeria 

Muhammad Musa ‘Yankara
Department of Hausa, Federal University Dutsin-ma, Katsina State, Nigeria

Tsakure

A rayuwar yau da kullum ga wasu al’ummu na duniya ba abin da suke tinƙaho da shi kamar noma. Hausawa suna daga cikin waɗannan mutane da suka dogara rayuwar su ga noma tun fil azal. A tsakanin manoman kuma ba abin da suke ke sha’awa kamar a kira mutum sarkin noma. Suna kaiwa ga wannan matsayi ne ta hanyar yin aiki tuƙuru ta adda mutum zai sami abincin da zai ci a shekara har ya sami na sadaiwa. A ɗaya hannu kuma, akan sami wadda bai zai ia taɓuka komai ba, ko hanyar gona bai so a ambata bare a ce ya tafi, irin wannan mutum shi ake kira raggon mutum wanda yunwa take kamawa ta yi tasiri a jikinsa har ta zama ciwo. Irin wannan yanayi na yunwa shi ne aka hango makaɗan noma sun waƙe domin su faɗakar da mutane cewa, ba ɗabi’a ce mai kyau ba. Ya kamata kowa ya tashi a yi aiki tuƙuru ta yadda zai fi ƙarfin bukatun yau da kullum ba unwa kaɗai ba. Yanayi da yunwa takan sa mutum ya kasance kuma ya sami kansa a ciki suna daga cikin abubuwan da wannan takarda ta yi kiɗa kuma ta yi rawar kiɗan a cikinsu.

Fitilun Kalmomi: Yunwa, Waƙoƙi, Waƙoƙin Noma

 

1.0 GABATARWA

Makaɗan baka na Hausa suna ɗaya daga cikin rukunan jama’a waɗanda suka haɗu suka samar da al’ummar Hausawa tun kuwa a lokacin zama na farko na mazauna ƙasar Hausa. Ana jin rarrabuwar makaɗa zuwa rukuni-rukuni ya wanzu ne bayan da Hausawa suka sami matsuguni na dindindin. Makaɗan farauta da makaɗan yaƙi da makaɗan noma suna daga cikin rukunonin makaɗan baka da Hausawa suka samu a zaman farko, daga bisani, sauran rukunonin makaɗa suka biyo sahu.

Lokacin da masana da manazarta suke karkasa makaɗan baka na Hausa, wasu sun yi la’akari ne da yanaye-yanaye na kaɗe-kaɗe da Hausawa suke aiwatarwa, wasu sun bi tsarin kayan kiɗan da ake amfani da su, wasu kuma sun lura da rukunonin mutanen da makaɗan suke yi wa waƙoƙi ne, wasu kuma sun yi tsokaci ne a kan saƙonni da waƙoƙin baka suke ɗauke da su da sauran abubuwan da nazari yake ba da dama a lura da su. Alal misali, kashe-kashen makaɗan baka na Hausa ta la’akari da kayan kiɗansu ya haɗa da; kiɗan sarauta da kiɗan sana’a da kiɗan biki da kiɗan datsa da kiɗan tankiya da kiɗan bori da kiɗan ban dariya da kiɗan bariki da kiɗan yaƙi da kiɗan busar iska da kuma kaɗe-kaɗen mata Zarruƙ da wasu 1998.

Hausawa suna daga cikin mutanen da suka dogara rayuwar su ga noma tun fil-azal. Wannan ya sa a rayuwar yau da kullum, al’ummar Hausawa suna tinƙaho da noma, wannan ya sa ake samun makaɗa na Hausa masu yi wa wannan sana’a kiɗa da waƙa. Daga cikin irin kiɗan da makaɗa suke yi wa manoma ya haɗa da na zaburar da su domin su yi aiki a samu abinci mai yawa. Haka kuma akwai kiɗan da suke yi masu na zuga, wato a fifita wani a kan wani da sauransu. Irin waƙoƙin da makaɗa suke yi domin zaburar da manoma da sauran mutane su yi noma a wadata ƙasa da abinci, suna yi ne domin a kuɓuta daga matsalar yunwa. Wannan matsala ta yunwa saboda muhimmancinta tasa ake samun makaɗa suna yin kiɗa a kan yunwa ta yadda manoma za su zabura a samu abinci ya wadata a cikin ƙasa.

Maƙasudin wannan maƙala shi ne, ƙoƙarin fitowa da hangen da makaɗan noma na Hausa suka yi wa yunwa. Sun yi ƙoƙarin bayyana yunwa a kan mizani na amfani da rashin amfani. Daga cikin irin rashin amfanin yunwa da suka hango ya haɗa da; Ƙaurar mutane da samuwar mutuwar aure da takaici da rowa. Haka kuma amfanin da suka hango tare da yunwa ya haɗa da; bayyana raggon mutum da kuma samun maganin yunwa. Waɗannan batutuwa su ne abin da wannan maƙala za ta mayar da hankali a kansu.

2.0 YUNWA

An bayyana yunwa da cewa, motsewar hanji da galabaita a sabili da rashin cin abinci ko ƙarancin amfanin gona a ƙasa, a sabili da faruwar fari da kuma ƙarancin abubuwan buƙata, misali yunwar tufafi, yunwar gishiri. Ƙamusun Hausa (2006). Watts (1983:1) ya bayyana yunwa da cewa, wani bala’i ne da kan shafi al’umma wanda ke haddasa ƙarancin abinci ta yadda jama’a masu dama za su tagayyara.

Yunwa tana nufin matsanancin ƙarancin abinci. Watau mutane su rasa abincin da zai wadace su. Umar (1992:5). Ta la’akari da ma’anonin yunwa da aka bayyana a sama, za a iya cewa ba komai ne yunwa ba, sai rashin wadatar abinci da ababen more wa rayuwa da sakamakonsa yake haifar da matsala a zamantakewa.

Ba kamar fahimtar da mafiya rinjayen mutane suka tafi a kanta ba, na cewa yunwa ta tsaya ne a ƙarancin cimaka. Yunwa ta wuce fahimtar mutane (ta cewa rashin cimaka ne). Yunwa ta haɗa da duk wani rashin yalwa na abubuwan buƙata na rayuwa da kuma abubuwan more wa rayuwa. A taƙaice duk wani abu a tsarin rayuwa da ake da ƙarancinsa to yunwa ne. (Malumfashi 2000)

Idan aka dubi tasirin yunwa a zamantakewa, za a fahimci cewa, ba ta tsaya a kan irin yanayin da mutum yake shiga a sakamakon rashin samun abinci kawai ba. Har ma da yadda ƙasa take samun kanta a cikin tsaka mai wuya dangane da kasa wadatar da mutanenta da muhimman buƙatu na rayuwa da suka haɗa da abinci da sutura. A taƙaice, duk inda ake da yalwa, to ba a samun yunwa, kamar dai yadda Illon Kalgo yake cewa a cikin waƙarsa ta gonar Sardauna:

“Shehu Kalgo taho rakka ni,

Mu zo waƙar gona,

Ni kan gona can nika wasa,

In kwana can,

In yini kuma can in koma hantsi,

Raina Ƙwal,

Gonar Sardauna,

Ba ka jin yunwar komi,

Kowas shiga gonar Amadu,

Has shi wuce duniyag ga,

Bai yunwa ko ɗai,

Ko guda.”

 (Usman 2011:13-14)

 

Al’adar yin awo a mafiya yawan wurare, ƙarancin abinci da rashinsa ne yake kawo ta. Don haka, yin awo (wato sayen abinci) abin kunya ne ko a kasuwa ne a idon Bahaushe. Duk wanda ba ya yin noma, to awo ya wajaba a kansa. Sakamakon haka, sai matansa su raina shi, saboda gidansa ba zai rabu da yunwa ba, domin babu wadataccen abinci.

A ƙoƙarin samun sauƙin bala’in yunwa, akan samu makaɗan noma na Hausa da suke yin waƙa domin zaburar da manoma su himmatu wajen yin sana’ar noma domin a wadata ƙasa da abinci don a kuɓuta daga bala’in yunwa.

An fahimta cewa waƙoƙin suna ƙoƙarin fitowa fili da irin illar da yunwa take haddasawa a zamantakewa duk da cewa, akwai yanayi da za a iya cewa a dalilin yunwa ne aka sami warakar matsalar. Daga cikin irin bala’o’in da yunwa take haddasawa waɗanda aka yi ƙoƙarin fahimtar su a sakamakon gudummawar makaɗan Hausa musamman na noma sun haɗa da ƙaura da mutuwar aure da takaici da kuma rowa. Haka kuma abubuwan da ake ganin an sami warakar su ta hanyar makaɗan Hausa a noma musamman a cikin waƙoƙi masu ɗauke da jigon yunwa sun haɗa da samun maganin yunwa da kuma bayyana raggon mutum ta yadda hakan zai sa ya sauya halinsa na ragganta.

Ga dai abin da Amali Sububu yake cewa a waƙarsa ta gwarzayen noma:

                 

 “Sarki ya yi doka a bar waƙar manoma,

In ba mu gurza su ba ba aiki suke ba,

Dan nan am mafarin hatsi su katse magwarza.”

 

Yunwa ba ta tsaya ga mai hankali, har maras hankali ba ta bari ba. Illar yunwa uku adabin Bahaushe ya ruwaito. Na farko, takan tanƙware dogo ya jicce, ya yi ɗan doro. Na biyu, takan sa gajeren mutum ƙaton kai, fuska ta tamuƙe, ta matse kamar an tatse rawani. Na uku, takan taɓi hankalin mai hankali. Hausawa na cewa, ko hauka ta san da yunwa. Da yawa akan tarar da mahaukaci yana kuka a kasuwa idan yunwa ta ƙwaƙwale shi, a ƙarshe in ba a sa kula ba, ya ce ga garinku. Yunwa na sa mai hankali ya yi aiki irin na marasa hankali, ya furta magana irin ta marasa hankali, duk ba cikin ya san abin da ya yi ba. Idan yunwa ta ci mutum ko ta koro shi, a wajen Bahaushe, mahaukaci ne a jaye masa a yi masa uzuri. (Bunza 2006:119)

An bayyana yunwa da cewa, motsewar hanji da galabaita a sabili da rashin cin abinci ko ƙarancin amfanin gona a ƙasa, a sabili da faruwar fari da kuma ƙarancin abubuwan baƙata, misali yunwar tufafi, yunwar gishiri. Ƙamusun Hausa (2006).

Watts (1983:1) ya bayyana yunwa da cewa, wani bala’i ne da kan shafi al’umma wadda ke haddasa ƙarancin abinci ta yadda jama’a masu dama za su tagayyara.

Yunwa tana nufin matsanancin ƙarancin abinci. Watau mutane su rasa abincin da zai wadace su. Umar (1992:5).

3.0 MIZANIN AWON YUNWA A HANGEN MAKAƊAN NOMA

Yaƙi da yunwa yana ɗaya daga cikin manyan jigogin waƙoƙin noma. Makaɗan sukan zuga manoma su noma abinci, a yaƙi yunwa a kuma zaburar da manoma su ƙara ƙwazon aiki. Haka kuma waɗannan waƙoƙi cike suke da ambaton labarin yunwa da illolinta da kuma irin amfanin da ake ganin yunwa tana kawowa, musamman wajen farkar da manoma su ƙara ƙwazon aiki a sami maganin yunwa. Ta la’akari da irin waɗannan illoli da alfanu da yunwa take haifarwa, tasa makaɗan yin waƙoƙi masu ɗauke da turken yunwa, domin ƙoƙarin fito wa da yunwa a tsarin zamantakewa da kuma a ƙasa baki ɗaya.

Daga cikin ire-iren abubuwan da yunwa take kawo wa sun haɗa da:

3.1 ƘAURA

Ƙaura aba ce da ke aukuwa ko faruwa a kai a kai lokacin yunwa. Mutane kan ƙaura zuwa waɗansu wurare musamman inda suka san za su sami abincin da za su ci. Sakamakon yunwa kan sa mutane tashi daga yankinsu zuwa wani yankin da suke ganin akwai yalwar abinci. Zaman iyali ba tare da mazajensu ba, ba ƙaramar takurawa ba ce a gare su. Iyali babu maigida tamkar garken dabbobi ne da ba makiyayi. Kowa zai iya yin abin da ya ga dama. Bayanin ƙaura ya zo a cikin waƙoƙin noma, kamar inda Amali Sububu yake cewa:

“Yunwa ta taho da gorori,

Ta iske maza,

Duk ƙaton da ta ƙuma ga wuya,

Sai a shantala,

Sai ya hurce Kwantagora,

Sannan ta waiwayo,

In taƙ ƙwumi bugu,

Wajjen yamma za ya sauka.”

(Amali Sububu: waƙar Yari Ɗanbangi)

 

A nan makaɗa Amali ya bayyana yadda yunwa ta ciyo mutane har ta sa suka yi ƙaura daga wurarensu zuwa waɗansu wurare da suke ganin akwai yalwar abinci. Kamar yadda ya bayyana, bala’in yunwa ya sa mutane suka yi ƙaura har zuwa yamma. Zuwa kudancin wannan ƙasar.

 “Rani wanga ya yi rani,

Ya sa maza lage,

Tafiya wagga ta yi nisa,

Ta sa maza gaba,

Yunwa wagga ta yi yunwa,

Ta ba mu arkane

Ga mata da ‘yan ɗiya,

Ka ji ƙatonta ya yi lalata,

Ya ba ta wuri,

Ya tceere yana ta kai nai.”

(Amali Sububu: Waƙar Noma ba ya Saka Rama)

 

A nan makaɗin yana bayani ne a kan masibar yunwa da take sa mutum ya gudu ya bar iyalinsa. A sakamakon wahala, maigida yana ji yana gani ya gudu ya bar matarsa tare da yara. A tsari na zamantakewa, da jin haka an sami matsala. Maigida shi aka sani da ya samo wa iyalinsa abin da za su ci. Sai gashi an sami akasin haka, an bar matar gida da ɗawainiyar iyali. Makaɗin yana cewa:

“Yunwa ta ci Adarawa,

Sun yo ga Gobirawa,

An iske Zamhwarawa,

Mun zan mutum guda,

 Kowa ba ka jin raha tai,

Sanda ina raha take,

Ƙato bai ci yar raga ba,

Garba ina batun raha,

Ƙato bai ci yar raga ba.”

(Amali Sububu: Waƙar Noma ba ya Saka Rama)

 

A wannan ɗiyan waƙar, makaɗin ya kawo dalilin da ya sa ya dage wajen zuga manoma su noma abinci domin a kori yunwa da take haddasa ƙaura. Amali ya nuna cewa, da zarar hatsi ya ƙare wa gwarzayen manoma, to yunwa ta yi sallama ke nan. Da zarar yunwa ta auka wa gari sai maganar ƙaura, kamar yadda ya nuna Adarawa sun yo ƙaura zuwa ga Gobirawa, aka kuma ɗunguma gaba ɗaya aka nufi wajen Zamfarawa.

3.2 MUTUWAR AURE

Aure abu ne da ya zama al’ada ga al’ummar Hausawa tun kafin su sami cuɗanya ko hulɗa da wasu mutane ko wata al’da ta ƙetere. Dalili kuwa shi ne Bahaushe a al’adance bai yarda da bin wata hanya ta ɗebe sha’awa ba (tsakanin mace da namiji) face ta hanyar aure. A al’adance idan aka ƙulla aure ba a warware shi sai da wasu ƙwararan dalilai. Duk irin wannan matsayi da aure yake da shi a al’adar Bahaushe, sakamakon yunwa, sai a wayi gari ana samun matsalolin da ba a tsammani, kamar dai yadda makaɗan noma suke nunawa:

Kaya ba ganin la’arin ganwo,

Zama da mace ba tsabac ci,

Akwai wuya akwai ban haushi,

Tana yi ma abin ganganci,

Ka hanƙure ka maisai banza,

Ka hanƙure takaici,

In ba ka tanka ba ka yi tsoro,

In ka tanka ta ɗora ce maka tcinannan maza.”

(Amali Sububu: Waƙar da Hanzarin Noma na Sanka)

 

Zama na aure ba abinci abu ne mai wahalar gaske. Kamar yadda makaɗin yake faɗa, a cikin wannan yanayi, za a ga matar mutum tana yi masa abubuwan da ba su kamata ba. Da zarar mutum ya yi magana a ce ya yi ganganci. Idan ya yi shiru a ce ya ji tsoro. Idan kuma ka matsa da yin magana sai rikici ya tashi wanda akasari shi ke sanadin rabuwa.

 

“Shekarun dandi ne,

Ba gudun kunya akai ba,

Yanzu karuwa tai yawa,

Ga su nan hab ba iyaka,

Karuwa ke baro iyaye ke zaɓi dandi,

Wagga ɗiya uwayenki na da baƙin cikinki.”

 

A wasu lokuta yunwa takan haifar da mutuwar aure ko kuma kasa yin aure. Wannan kuma sai ya haifar da yawon dandi. Amali Sububu ya kawo bayanin illar yunwa ta yadda har takan haifar da gurɓacewar zuciya. Haka shi ke sa wasu suna suna gudu daga gidajensu suna tafiya yawon dandi da karuwanci.

3.3 Takaici

An bayyana takaici da cewa, jin haushi ne wanda ɓacin rai yakan kawo (Ƙamusun Hausa 2006). Ta la’akari da wannan ma’ana akwai alamun da ya yi kama da haka a cikin waƙoƙin noma. Dubi dai abin da aka samu makaɗa Umar yana cewa:

 To kowa damuna ta kama,

Ya ƙi zuwa daji noma,

Danginshi su bar horar ƙato,

Su bari yunwa tai mai tuyar masa,

Sai ka ji hanji na ƙugi.”

(Umaru ya fi sha’awa: Waƙar musa mai lahiya)

 

Duk wani mutumin da ya ƙi yin noma, makaɗin yana kira ga dangin shi da su daina wahalar banza wajen ci da shi. A maimakon haka su bar shi ya shiga cikin halin ɓacin rai na yunwa ta yadda zai lalace kamar masar da aka toya.

A wata ‘yar waƙa da aka bayyana halin takaici, makaɗa Amali Sububu yana cewa:

Kun gani yunwag ga na sa,

Mutum ya yi zaune jangwam,

Yana magana cikin zuciya tai ba a sani ba,

Sai ka ji zuciya tai tana mai ebe-ebe.”

(Amali Sububu: waƙar mai shirin yaƙi da sabra)

 

A sakamakon shiga halin takaici da yunwa take haddasawa, Amali Sububu a cikin waƙar mai shirin yaƙi da sabra, yana cewa, akan sami mutum yana zance a cikin zuciyarsa ba tare da ya san abin da ya ke faɗa ba. Sai ya ƙulla wannan zance ya warware wannan. Haka zai yi ta yi saboda halin da yunwa ta jefa shi ciki.

A game da abin da ya shafi takaicin da yunwa take haddasawa makaɗa Bawa Sakkarawa yana cewa:

 

“Mai kiɗin mata tare da yunwa yake,

Ya kwanta ya rasa kwanci da kyau,

Ya zauna ya rasa zaunawa da kyau,

Yunwa tai mashi ɗarmen dame.”

 (Bawa Sakkarawa: Waƙar Noma)

 

Bawa Sakkarawa ya bayyana cewa, yunwa ba ta bar kowa ba, har makaɗa ba ta bari ba. Kamar yadda yake faɗa halin da yunwa take sa mutane, bai tsaya ga mutanen da suke da dangantaka da gona ko noma ba. Abin ya wuce nan domin har ya haɗa da makaɗa.

3.4 Rowa

Ana iya cewa rowa kishiar kauta ce. Idan muka dubi wannan ma’ana ta rowa za mu ga abin da ya yi kama da haka a gangumman noma na makaɗa. Amali Sububu yana cewa:

“Ashe yunwag ga na sa,

Mutum ya gaza da mata,

Ya sa a yi mai jiƙo,

Ba ya ce mata tashi gashi.”

(Amali Sububu: Waƙar mai Shirin Yaƙi da Sabra)

Amali Sububu yana cewa yunwa tana sa mutum ya sami abinci amma ya hana abokin zamansa, kamar dai yadda ya bayyana cewa, ga miji ya sami abinci amma ya hana wa matarsa saboda masifar yunwa.

3.5 Maganin Yunwa

Waƙoƙin yunwa da makaɗan noma sukan shirya, suna yin su ne domin zaburar da manoma da sauran jama’a da su koma gona domin duk wani tsanani da aka shiga na matsalar yunwa, in dai ana noma to za a samu sauƙin matsalar. Abubuwan da aka bayyana a baya idan aka dube su da idon basira za a tarar cewa, hanyoyi ne da yunwa take yin tasiri na abin ƙi a tsarin rayuwa. To amma ta wata fuskar idan aka duba sai a gane cewa, akwai abubuwan da yunwa ta sa suka zama hannunka mai sanda a tsarin zamantakewa. Ga dai abin da aka samu makaɗan suna faɗa:

“Maganin yunwa noma,

 Maganin yunwa noma,

Yara maganin yunwa noma,

Na faɗa sau uku ke nan,

Maganin mai yin shakku,

Na faɗa sau uku ke nan,

Ko mutum na yin shakku.”

(Abdu Wazirin Danduna: Waƙar Noma)

 

Duk da cewa Abdu Wazirin Ɗanduna ba makaɗin noma ba ne, amma ya yi wata waƙa da ya ba ta suna waƙar noma. A cikin wannan waƙa ya yi bayanin abin da yake gani a matsayin maganin yunwa. A tasa fahimtar babu maganin yunwa da ya wuce noma.

A gaba kuma an samu inda Muhammadu Yaro hore yake cewa:

“Wanda duk ya faso dajin ga,

In ya jiyo yunwa,

In ka jiyo yunwa,

In ka zo gidan goje,

Kana samun hurar gero.”

(Muhammadu Yaro Hore: Waƙar Gojen Noma)

 

Idan aka duba za a lura cewa, dalilin da ya sa wannan makaɗi ya ce maganin yunwa hurar gero, ya faɗa da niyyar zaburar da mutane da a tashi a yi noma, domin kamar yadda ya nuna an sami hura a gidan Goje, Goje yana ɗaya daga cikin zaruman manoma don haka ba a tsammanin gero ya yanke a gidansa. A taƙaice duk wanda ya dage wa aikin noma to ba shakka abinci ba zai yanke masa ba.

Da aka matsa gaba, an ci karo da abin da makaɗa Maidaji Sabon Birni yake faɗa kamar haka;

 “Maganin yunwa,

Kudaku ko rogo da ƙuli-ƙuli,

In anka haɗa su kuma ga dawo da hwarau-hwarau.”

 (Maidaji Sabon-birni: Waƙar Manoma Allah ya Taimaka Mana a Gurin Hatci)

 

A tasa fahimtar, ya tunatar da mutane cewa ko da noman kudaku ko rogo da ƙuli-ƙuli ana iya tsira daga masibar yunwa.

 

 Bakura gonar Amadu Sardauna,

Zaman shi ya sa wani kudaku,

Wanda ban ga kowa da irinai ba,

Kudakun ga na Sardauna,

Ya ƙwale zaƙi ag gare shi,

Ban ga iyaka ba,

Ashe kudaku na gonar Sardauna,

An bar yunwa ƙasag ga,

Ga saya ya girma,

Kudaku na gonar Sardauna.”

(Illon Kalgo: Waƙar Gonar Sardauna)

 

A wannan ɗiyan waƙa, makaɗa Illon Kalgo yana bayyana wani ingantaccen iri na kudaku da ya gani a gonar Sardauna. A ganinsa wannan kudakun mai kyau ne ta yadda idan aka sa himma wajen nomansa, ana iya wadata ƙasar nan da abinci a kori yunwa.

3.6 BAYYANA RAGGO

Awde (1996) ya bayyana raggo a matsayin malalaci.

Raggo shi ne, malalacin mutum marar kuzari. Haka kuma ana iya ɗaukar matsoraci ko marar dabara a matsayin raggo. Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ta Kano. Bergery (1934:832) ya bayyana ma’anar raggo da cewa, shi ne mutumin da yake santolaɓi ko malalaci ko soloɓiyo ko sahorami ko salloto ko kuma zawaliƙi.

A taƙaice abin da aka fahimta da raggon mutum shi ne, mutumin da ba ya son dagewa wajen yin wani aiki. Ya zama marar dabara ta neman abin da zai taimaki rayuwarsa. Watau mutum ya zama kumama.

 

A game da bayyana raggon mutum a cikin waƙoƙin noma, ga abin da aka samu makaɗa suna ambatawa:

 

Zamanin ana yunwa,

Shi ta da turbe ni a riƙa mai,

Shi ta da sassanya a riƙa mai,

In anka kai kaka,

Ran nan fa mai hatsi,

Sai ya biɗi jinga,

Kowa ya kai ga na kai nai,

Ran nan raggo ya butulce.”

(Bawa Ɗanance: Waƙar Garba Nagoɗi)

A nan makaɗa Ɗananace ya kawo abin da ya faru lokacin da aka yi wata yunwa, ta yadda ba kowa ne ke iya yin noma ba. Garba Nagoɗi yana yin noma, kuma ana taya shi, amma sai kaka ta yi yake biyan kuɗin aikin da aka yi masa. Amma raggo da yake bai yi tayin aikin sai ya rasa alamar tabbata cikin yunwa.

4.0 SAKAMAKON BINCIKE

A bayane yake cewa sana’ar noma tana daga cikin fitacciya kuma daɗaɗɗiya a ƙasar Hausa, kuma duk mai yenta yakan hushe haushi a zamantakewa. wanda bai iya yenta yana cikin takaici kuma shi ne wanda yuwa take aura. Daga cikin ire-iren abubuwan da wannan takarda ta gano waɗanda yunwa take kawo wa ko ta jefa mutum a ciki sun haɗa da:

 

a.       Ƙaura

b.       Mutuwar aure

c.        Takaici

d.       Rowa

e.       Maganin Yunwa

f.        Bayyana Raggon mutum

4.1 Kammalawa

Wannan maƙala mai taken “Mizanin Awon Yunwa a Mahangar Makaɗan Hausa na Noma” yunƙuri ne, na nazari a kan yunwa musamman kamar yadda makaɗan noma na Hausa suka gwada ire-iren abubuwan da take haifarwa, wanda ake so da wanda ba abin so ba ne. Yunwa ta daɗe tana addabar mutane. Kamar yadda aka ambata tun da farko, hali ne na rashin abinci ga mafi rinjayen al’umma na wata ƙasa ko yanki. Abubuwan da suke haddasa yunwa sun haɗa da, fari da bala’in ƙwari masu ɓata amfanin gona kamar tsutsa da kuma tsuntsaye. Haka kuma talauci ba kanwar lasa ba ne wajen kawo yunwa a ƙasa. Kamar yadda makaɗa waƙoƙin noma suka dubi yunwa a bisa mizani, an fahimci cewa, akwai matsaloli da take haifarwa da suka haɗa da ƙaurar mutane daga wani wuri zuwa wani, da yawaitar mutuwar aure da yawon karuwanci da rowa da halin takaici da kuma bayyana yadda ragon mutum ya ke. Haka kuma ta ɓangare guda idan aka dubi yunwa sai a tarar tana saka mutane su zama masu ƙwazon aiki wajen samar da abinci da za a yi maganinta da shi.

 

Manazarta

 

1.       Awde, N. (1996). Ƙamusun Hausa da Turanci da Turanci da Hausa. Hippocrene Books, INC 17 Madison Avenue New York, NY10061

2.       Bergery, G. P. (1934). A Hausa -English and English-Hausa Vocabulary.Second edition. Ahmadu Bello University Press Ltd. 1993

3.       Bunza, A. M (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Ltd, Surulere Lagos.

4.       Gummi, M. F. (2008). Tsumangiyar Kan Hanya: Nazarin Wasu Waƙoƙin Yunwa na Baka A Sakkwato da Kabi da Zamfara. Kundin Kammala Karatun Digiri Na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

5.       Gusau, L. G. (2001). Tarihin Yunwa Yar Gusau. Unpublished B. A. Prroject. D. N. L. UDU Sokoto

6.       Gusau, S. M. (1983).Waƙoƙin Noma Na Baka: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu Musamman a Sakkwato. Juzu’i Na Ɗaya, Kundin Neman Shedar Kammala Karatun Digiri Na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya B. U. K. Kano.

7.       Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazain Waƙar Baka. Benchmark Publishers, Ltd, Kano, Nigeria.

8.       Ƙamusun Hausa (2006). Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano. Ahmadu Bello University Press, Zaria.

9.       Usman, B. (2011). Yunwa a Mahangar Waɗansu Waƙoƙin Noma. Unpulished B. A. Hausa Project. D.N. L. UDU Sokoto.

10.    Malumfashi, I (2000). Minene Yunwa? A Cikin Mujallar Garkuwa. Garkuwa Publishers.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.024

Post a Comment

0 Comments