Ticker

6/recent/ticker-posts

Bai Wa Shata Digirin Girmamawa, Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya

Aliyu Ibrahim Kankara
Mawallafin Littafin Shata

Ina tunawa, ranar wata Juma'a, 15/1/1988 aka yi taron tunawa da rasuwar Sardauna a Kongo Conference Hotel, Zariya. Na halarci taron, lokacin ina ajin zangon karatu na farko a Kwalejin share fagen shiga Jami'a ta Zariya. Amma da dare sai Musa Dankwairo ya yi wasa a wurin. Kudin shiga kallo naira daya. Ni da wasu abokai mu ka dawo da dare mu ka biya, mu ka sha kallo. To, a nan wani abokina ya shaida ma ni cewa za a ba Shata digirin girmamawa a Jami'ar Ahmadu Bello, sati mai kamawa.  Na yi ta al'ajabi. Sai kuma ga shi, aka ce, gobe  Asabar, shi dai Shatan za ya yi wasa a nan dai KCH, a kan dai bukukuwa na tunawa da Gamji dan kwarai.

Wanshekare, da dare, wuri ya cika. Amma kudin shiga naira uku. Sai na makale kudina cikin aljihu na ki biya in shiga, na ce sai na ga zuwan Shatan tukun. Karshe har karfe biyu na dare Shata bai zo ba. Wasu su ka zanzare su ka tafi. Amma, ni, ni da wani abokina mu ka zauna a bisa wata kwalbati a daidai shiga cikin wurin, har asuba. Da gari ya fara wayewa, muka tabbatar Dodo dai ba za ya zo ba, sai mu ka koma Kwaleji.

Ran Juma'a mai zuwa, ya kama 22/1/1988 sai ni da abokina Abbas Mohammed Dutsinma (yanzu ma'aikacin INEC Kano) mu ka tafi kofar gidan Sani Gadagau (Bakatoshi) da ke nan cikin unguwar Magume inda dakunan kwananmu su ke, don mu tabbatar, da gaske ne ABU za ta ba masoyinmu digiri? Kafin ma mu isa wurin, sai mu ka ga wata mota fijo ta Jami'ar ta dauki Shatan da shi Bakatoshi ta fita da su. Na ce ma Abbas, 'ka ga maganar nan da gaske ne, ina ma tammanin can ABU din za su tafi.

Amma, sai muka isa kofar gidan Bktshi. Sai ga yaran Shata. Su ka tabbatar ma na da haka. Mu ka tafi mu na farin cikin cewa masoyinmu ya kara samun girma a Duniyar mawaka.

Ran Asabar, 23/1/1988 na yi sammako na tafi Samaru. A gabana aka yi komi, don ban bari aka ba ni labari ba. Mu na ma tsaitsaye a hanyar shiga cikin wurin taro manyan baki su ka yi jerin gwano su ka shiga ciki. Na ga Shata cikin tawagar baki, ya na sanye da farar shadda da kube mai ruwan goro.

Lokacin taro, Farfesa Dalhatu ya karanta tarihin Shata da ingilishi, sannan ya gabatar ma mataimakin shugaban Jami'a, Farfesa Adamu Nayaya Mohammed Shata don a ba shi digiri. Ga kuma shugaban Jami'a, Aliyu Mustafa, Lamidon Adamawa a tsaye. Su biyu su ka yafa ma Dodona wannan alkyabba, su ka ba shi wani zagayayyen abu. Duk akan idona aka yi komi. Su hudu aka ba digiri a lokacin. Amma, cikar da aka yi a wurin, kusan, saboda ganin Shata ne. Ga kuma gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, sun zo da motar nan ta tafi-da-gidanka domin watsa shirin a kai tsaye.

Sai aka ce Shata ya yi waka don nuna godiya. Sai na ga ya fara da wakar Sarkin bori Sule, ya yi ta kamar baiti uku, sai ya goce ya fara 'Mu je gidan ilimi ABU'. To, su dai na ke iya tunawa.

Da aka watse, sai kuma a nan din dai, na samu labarin wai za kuma a tafi gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN) don yin taron dare, watau Gala Night. Ina fitowa bakin get sai na afka motar Kaduna. A lokacin naira daya ne kacal kudin mota, har Kawo.

A Kaduna, na tafi Fanteka na samu abokina Hamza Dan'azumi Kankara. Ya tambaye ni, lafiya? Na ce ma sa 'ka ji ka ji'.  Nan na zauna har almuru. A wurin, akwai 'yan Kankara da yawa. To sai na ga labarina ya fi karjata ga wani, Sama'ila. Ya ma ce tare za mu je FRCN. Wuf, kafin mangariba sai munka shafa kasa, sai Tudunwada. Mu ka ci abin kusa da baki, mu ka yi sallah. Isha'i na gotawa sai munka shafa kasa, mu ka bi ta Oriyafata, mu ka rabi titin Katsina, sai Metro, sai titin indafenda, sai ga mu gidan Rediyo.

Sa'adda mu ka isa mu ka tarar wuri ya cika tsangam da mutane, an ma fara wasa. Mun tarar Magajiya Danbatta na waka. Mun kuma tarar wata mata ta gama. Ga Shata zaune, sanye da kayan digiri.

Amma, babban abin da ya bata ma ni rai da hukumar gidan Rediyon ba su dauki matakin rage yawan masu shiga kallon ba. A wurin, daga baya, inda ake yin wasannin Kashe Ahu ne, akwai wasu dogwayen itatuwa. To nan wasu tsagera, marasa kunya, samarin Rigasa da Tudunwada su ka haye sama su ka yi ta aiko da rashin kunya da iya ahege. Ko lokacin da aka kira Adamu Danmaraya Jos ya yi waka, sai da su ka yi masa rashin kumya. Kowa na jin su amma aka kyale su.

Ina matsawa a hankali, har na matsa kusa da Shatan. Ina kusa da kafafuwansa ne ma na ga an kawo ma sa bangaji na zuma, aka ce kyauta ce daga wani. Na kuma lura da lokacin da aka kawo ma sa kyautar kwalebanin turare. Har ya yi barkwanci, ya ce ba ya so, kada gobe idan ya shafa ya tafi dawa yawon halbi zuma ta biyo shi. A like da Shata, na ga wani, Dokta Mijinyawa, wanda hukumar ABU ta turo ya zama mai kare lafiyar Shatan. Kadan-kadan sai in ga ya gyara ma Shatan wannan alkyabba. Na kuma ga wasu matan Shatan a wurin, Hajiya Hurera Yamai da Hajiya Dijen Falgore. Amma, a gaskiya, a cikin 'ya'yansa, idan ma su na a wurin, ba wanda Allah Ya gwada ma ni in ban da Jamila. Hakika na gan ta a kusa da Hurera.

Da ya tashi za ya yi waka, na tuna, ya yi wakokin ABU da ya fara dazu a Zariya da ta Allah Ka taimaki Mamman Koguna, sai kuma na ji ya fara ta Nagode wa Dankabo Mamman. Su dai na ke iya tunawa.

Da kimanin karfe 1:45 am ya ce ya gaji, barci ya ke ji. Ya na mikewa sai taro ya fara watsewa. Mun bi shi ke nan, sai ga Barmani Coge ta dawo, sai ya tsaya. Sai na ji ya ce ma ta 'Kanwata, ba ki tafi ki ka kwanta ba? Sai na ji ta ce ma sa 'ai ranka ya dade, na tafi ban zo na yi bankwana ba wurinka? Ina daga gefen hannun damar Shatan a tsaye, ina rike da hannunsa. Har wani saurayi ta taka ma ta takalmi ya katse. Sai na ga ta dauke shi ta rike a hannu. Na ji Shatan ya ce ma ta 'ashsha'. Saboda runtsin mutane ma su son su ma taba Shatan, don su na ma ta taba shi, sai na saki hannunsa na fita daga wannan runtsin. Na nemi Sama'ila ban gan shi ba. Saidai na bi ayarin matasa mu ka koma Tudunwada.

Da safe, ran Lahadi, na koma Zariya.

Har ila yau, wanshekare, ran Litinin, mun gama darasin rana, mun dawo daki mun yi sallah, mun ci abinci, ina ahirin tafiya darasin marece, watau mu, daliban Kimiyya, mu na zuwa dakunan gwaji (laboratories) don yin darasi. To a duk litinin, mu na halartar gwajin darasin kimiyyar rayuwar dan Adam da tsirrai (Biology) Kawai sai ga Abbas ya shigo dakina, ya ce 'yau kai Adoke, ashe Shata bai tafi ba, ya na nan gidan Bakatoshi.

Haba, sai na jefar da practical book, mu ka kuma ruga kofar gidan Bktshi.

Na rantse da Allah, lokacin da mu ka isa mu ka tarar an kulle falo, an koro kowa waje, Shatan ne kadai a ciki, shi da Adamusawa. Mun isa da kimanin karfe uku, mun kuma tarar Shatan na waka. Mu na nan tsugunne a bakin falo mu na saurarensa. Ya yi waka kala hudu kacal. Mun dai tarar ya na wakar Dankabo da ya fara a FRCN, da ya gama sai ya yi ta ta Mu je gidan ilimi ABU', sai ya yi wata mai amshin Gaisheku malaman ABU. Da ya gama sai ya yi ta Allah Ka taimaki Mamman Koguna. Kowace ya dauka sai ya yi kamar awa daya da mintoci ya na yin ta. Ni dai, karfe uku na isa wurin, amma na rantse da Allah, a gabana Shata ke waka bai tsaya ba (non-stop) har karfe tara na dare, wallahi summa tallahi. Ba mu kuma gusa mu ka bar wurin ba. Wuri fa ya cika makil da dan mutum .

Ashe ashe, hukumar ABU ce ta aiko da katuwar rikoda ta ce ya yi ma Jami'ar waka, wai su na zaton idan aka bari aka dauki kwanaki to ana iya nemansa ba za ma a gan shi ba. Gara, tunda zafi-zafi a tursasa ma sa ya yi wakar ya ba su.

Kimanin tara da mintoci ya fito. Sai na ga wannan dai kaya na digiri a wuyansa.

Sai na ga wasu malamai sun amshi rikoda da kaset din (special cassette ne) su yi godiya. Na ga sun afka cikin wata farar fijo ta ABU sun tafi. Shi kuma Shata, sai na ga sun yi bankwana da Bakatoshi, shi da Adamusawa sun ahiga wata mota. Suna dagawa, sai na tambayi Bakatoshi, 'ina za su tafi'. Sai ya ce ma ni 'Funtuwa'. Cikin minti kadan sai kowa ya watse.

Wannan, duk akan idona aka yi su.

Daga baya, bayan na shiga Jami'ar Ahmadu Bello sai Dr. Adamu Abubakar Kafin Hausa, shugaban sashen nazarin harshen Hausa ya ce wadannan wakokin su na nan an ajiye su a ODU (Oral Documentation Unit) na Jami'ar.

Dakta Mamman Shata Katsina

Post a Comment

0 Comments