Yadda Ake Toshe (Blocking) Na Haramtattun Websites Na Batsa A Waya

    Lallai yana da kyau mu haɗu mu yaƙi kallace-kallacen finafinan batsa a tsakaninmu, domin Allah subhanahu wata'ala ya haramta, kuma yin hakan na jazawa ƙasa fitina da bala'i.

    A addinance dai kowa ya san kallon video na batsa haramun ne, haka kuma kallonsu yana cutar da lafiyar idanu da kuma gurɓata zuciya tare da saka raunin imani da tsoron Allah a zukatan al'umma.

    Muna cikin wani zamani wanda yahudawa suke amfani da cigaban da aka samu na amfani da yanar gizo suna gurɓata mana tarbiyar ƙanne da yara dama mu kanmu ɗin baki ɗaya, ta hanyar buɗe website masu ɗauke da bidiyoyi na batsa wanda mu addininmu ya haramta mana kallansu, su kuma suna samun maƙudan ƙuɗaɗe ta haka.

    Ba a iya maza kallon bidiyoyin batsa ya tsaya ba, harda mata kuma hakan yana 'daya daga cikin abubuwan da suke bada gudunmuwa sosai wajen lalata mana tarbiya. Wa'iya-zubillah, Allah ka ƙara tsare mu, Amin.

    Ni Salisu Magaji Fandalla'fih, Zan faÉ—a muku hanyar da za ku bi domin ku toshe hanyar da dan uwan ka, ko yar uwar ka, da wayar ka, shiga shafukan finafinan da basu dace ba ta kafar Internet.

    Shin Kana da Æ™ani ko Æ™anwa da ke hawa kafafen Sada Zumunta, ? 

    Kuma kana tsoron kada su rinƙa zuwa shafukan Batsa na kafar Internet suna kallon Fina-Finan Banza ba tare da kai ka sani ba, ga hanyar da zaka hana su ko hana wayar ka shiga waɗancan lalatattun shafukan.

    Hanyar da zaka iya bi domin haramta ma wayarka ko wayar ƙaninka kota ƙanwarka, kota yaranka samun damar kamo wa'dannan website ɗin shine.

    1. Da farko zaka shiga cikin (Settings) na wayar ka.

    2. A cikin settings É—in akwai wajan Searching (Bincike) a sama saika shiga.

    3. Idan ka shiga saika rubuta wannan kalma (Private DNS) Zaka ga ya fito a ƙasa saika shiga.

    4. Idan ka shiga zai nuna maka wasu rubutu guda uku a jere

    Na farko an rubuta

    ✅ Off

    🔘 Automatic

    🔘 Private DNS provider hostname

    Idan kaga haka saika cire waccan alamar ✅ dake kan Off saika  kamayar dashi kan, ma'ana ka danna kan wannan kalma 👇

    ✅ Private DNS provider hostname

    Saika duba Æ™asa waje mai alamar wajan rubutu, a wajan zaka ga an rubuta,  enter hostname of DNS provider

    4. Saika shiga wajan ka rubuta wannan kalamar kamar haka 👉 adult-filter-dns.cleanbrowsing.org👈

    Idan ka rubuta haka a ciki, saika duba Æ™asa zaka ga an rubuta             

                                       ðŸ‘‡

                                   SAVE

    Ka danna wajan kana dannawa insha Allahu ka rigada ka gama rufe, duk wani website dake sanya Videon Batsa a internet, insha Ko kaje kayi searching ka shiga zaka ga bazai buÉ—e ba.

    Kuma koda a Facebook ka rubuta kalmar da take nufi da batsa a harshen turanci, to saidai kaga Facebook É—in ka sunce ka koma baya.

    Sannan ina bamu shawara wannan saitin mu saita shi a wayar duk wanda muka san wayar sa zata iya zuwa hannun mu, hakan ba laifi bane illa ma ka taimaki wanda kaiwa hakan.

    Dan Allah ku tayamu da sharing, domin duk wanda ya sanar da wani shima yana da lada.

    Zamu kulle wayoyin mu daga buɗe Fina-Finan Batsa a kafar Internet, kuma zamu kulle wa ƙannen mu, da duk wanda wayar sa tazo hannun mu, ba tare da ya sani ba, domin tsira daga azabar uban giji.

    Allah ya ƙara tsare mu da mu da ƴan uwan mu, tare da dukkanin musulmi daga faɗawa tarkon sheɗan da she'danun mutane, Allah ka tsare mana imaninmu aduk inda muke, ka nesanta mu daga aikata dukkan wani aiki wanda baka so. Amin.

    Gudummawar
    Salisu Magaji Fandalla'fih
    27-08-2022

    Finafinan batsa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.