𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikm mal. inada tambaya mace ce mijnta ya rasu kuma takasance tana aikin gomnati shin zata iya fita a lokacin da take takaba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaiku
mussalam warahmatullah, a zahirin maganar malamai, mai takaba ba za ta je aikin
gwamnati ba, tun da bai halatta mai takaba ta fita ba sai lokacin tsananin
lalura, aikin gwamnati ba ko yaushe zai zama lalura ba, tun za’a iya ba ta hutu,
in har ta nema, in tana da yadda zata cı abinci ya wajaba ta amshi hutu, ko da
babu albashi. Saboda bin sharia shi ne zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah,
to shi ma zai kiyaye shi, duk wanda ya yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.
Amma idan ta rasa yadda za ta yi ta cı abinci sai ta hanyar aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi ﷺ ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a gidan ɗaya dağa cikinsu domin hira da debe kewa da rana, lokacin da suka takuru da zaman kaɗaici, duk da ya wajabta musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai takaba fita da rana, kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata a littafinsa na Mugni 8/130.
Duk da cewa wasu malaman Hadisin sun raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan Mas’ud da Abdullahi dan Umar, Allah ya kara musu yarda, maganar Sahabi hujja ce, in har ba’a samu wani sahabin ya saɓa maşa ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fiƙh.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.