𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam alaika warahamatullah wabrakatuhu Dr don Allah mene hukuncin dalibai masu zuwa wata kasa karatu shin zasu iya kasaru a can ?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wassslam
alaika warahamatullah wabrakatuhu.
Mu rike akida a musulunci hakika asalin kasaru
mutum yana yin tane a garin da bazai jima cikinsa ba kokuma bazai ɗauki kwanaki
a cikinsa ba misali Wanda yaje daurin aure ko kasuwanci da sauransu
Amma duk garin
da yake mutum idan yaje zai dade cikinsa ma’ana
abin da ya kaisa zai dauki lokaci mai tsawo misali dalibin da yaje
karatu zaiyi degree a wata kasa zai dauki shekara huɗu to anan bai halatta ya
yi kasaru ba ya kamata dalibai masu karatu a wata kasa su kiyaye wannan ka’ida
lokacin da yake karatu kasar domin shari’a ta ware adadin kwanakin da mutum zai
iya yin kasaru idan ya tsinci kansa a wani gari
Amma idan ya yaje garinsu hutu ko kasarsu babu laifi zai iya yin tunda bazai dade ba zai koma karatunsa wannan shi ne zance mafi inganci daga malamai.
Allah shi ne sani
Amsawa:
DR ABDALLAH GADON ƘAYA.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.