𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As Salamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh. Please, ina da tambaya: ‘Daughter-in-law’ na tana ‘300 level’, yanzu ga takaba ta same ta. Shin za ta iya zuwa ‘lectures?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
W alkm slm w rhmt laah wa barakaatuh.
Al-Imaam
Muslim ya fitar da hadisi (Lamba: 1483) da isnadinsa sahihi har zuwa ga Sahabi
Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce: An saki innata, sai ta yi
nufin ta je ta yanke 'ya'yan ita cen dabinonta, sai wani mutum ya hana ta. Don
haka, sai ta tafi ta gaya wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),
sai ya ce:
بَلَى فَجُدِّي
نَخْلَكِ ، فَإِنَّكِ عَسَى أَنْ تَصَّدَّقِي ، أَوْ تَفْعَلِي مَعْرُوفاً
A'a! Ki je ki yanko 'ya'yan dabinonki, domin za ki iya yin sadaka, ko kuma ki yi wani aikin alkhairi.
Watau kamar ta yi kyauta, ko sada-zumunci, da sauransu.
Dukkan Malaman Fiƙhu irinsu: Maalik da At-Thawriy da Al-Laith da As-Shaafi'iy da Ahmad, ban da Abu-Haneefah sun yarda cewa: Wannan hadisin dalili ne a kan cewa mace mai idda tana iya fita daga gidanta da rana, idan akwai larurar da ta janyo ta ga hakan, (kamar abin da hadisin ya nuna, na zuwa yin aiki a cikin gonarta, ko wani abin da ya yi kama da hakan).
Amma har Abu-Haneefah ya dace da su wurin amincewa cewa: Mai takaba tana iya fita, idan aka samu irin larurar da ta sanya mai idda ta fita.
Haka Al-Imaam An-Nawawiy ya kawo waɗannan maganganun a cikin sharhinsa ga wannan hadisin a cikin Sharhu Muslim.
A ƙarƙashin hasken wannan hadisin da waɗannan kalamai na manyan malamai za mu iya gane cewa: Mai takaba tana iya fita daga gidanta ko ɗakinta domin larurar zuwa ɗaukar lectures a jami'a, ko dai wata makaranta irinta, amma a ƙarƙashin kulawa da wasu manyan ƙa'idoji kamar haka:
1. Daga ta gama abin da ya fitar da ita, sai ta yi gaggawan komawa gida. Kar ta tsaya hira, ko yin duk wani abin da ba shikenan ba.
2. Kuma lallai ta tsare dokokin da aka ɗora wa mai takaba, tun daga lokacin da ta fito daga gida har zuwa ta koma. Watau:
(i) Ba za ta sa kayan kwalliya irinsu ɗan-kunne da sarƙa da warwaro da makamantansu ba.
(ii) Ba za ta sa tozali ko gazal ko eye-shadow da lalle ko dyes ba, balle su jan-baki da hoda da sauransu.
(iii) Ba za ta sanya tufafi masu launi na ado, kamar leshi da shadda da sauran nau'ukan atampa masu tsada da ake yin ado ko kwalliya da su ba.
(iv) Za ta dawwama a cikin hijibinta na shari’a.
(v) Ba za ta sanya turare da sauran kayan shafe-shafe masu ƙanshi a jikinta ko a kanta ko a tufafinta ba.
3. Haka za ta zauna har sai ta yi tsawon watanni huɗu da kwanaki goma, daga ranar da mijinta ya rasu.
Allaah ya ƙara mana shiriya da ƙoƙarin tabbata a kan bin dokokin Al-Ƙur'aan da Sunnah bisa fahimtar Magabatan wannan al'umma, domin samun tsira a duniya da barzahu da lahira.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.