Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Layya Wajibi Ne A Kan Mai Aikin Hajji?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Shin layya wajibice a kan mai aikin hajji?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Layya A Kan Mai Aikin Hajji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

shin layya wajibi ce akan mai aikin hajji?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai Sunyi saɓani akan hukuncin layya akan mai aikin hajji, wasu sukace mustahabbi ce akan mai aikin hajji, wasu sukace babu layya akan mai aikin hajji.

Waɗanda sukace babu layya akan mai aikin hajji sunyi saɓani akan saɓanin rashin shar'antuwarta akansa abisa magan-ganu guda biyu:

1. Sukace mai hajji babu Sallar idi akansa, yankansa kuma shi ne hadayar tamattu'i, ko Qirani.

2. Mai hajji matafiyine, layya kuma an shar'antawa mazaunin gidane, wannan shi ne maganar Abu hanifa, awajansa mai aikin hajji, idan dan cikin makkah ne shi ba matafiyi bane, layya ta wajaba akansa.

Hanafiyyah sukace: Wajibice akan matafiyi da Mazaunin gida,  kamar yanda yazo  acikin Al-Mabsuud (6/171).

Yazo acikin "Jauhara (5/285-286)" Layya ba wajibi bace akan mai hajji matafiyi, amma wanda yake mazaunin makkah wajibice akansa koda zaiyi hajji.

Malikiyyah sukace: Babu layya akan mai hajji, saboda kasancewarsa mai hajji, ba saboda kasancewar sa matafiyi ba. Kamar yanda yazo acikin Mudawwanah ( 4/101).

Shafi'iyyah sukace: Layya Mustahabbi ce akan mai hajji.

Imamu Shafi'i ya ce: Layya Mustahabbi ce akan mai hajji mazaunin makkah, da wanda ke kai kawo tsakanin gari zuwa gari, da Mazaunin gida,  da wajibice akan wasu banda wasu, da akan mai hajji zatafi zama dole, domin yankane, mai hajji kuma akwai yanka akansa, saidai bai halatta a wajabtawa mutane abuba saida hujja, babu ban-banci tsakaninsu. Al'Ummu (2/348).

Ibnu hazam ya ce: Layya ga Mai hajji mustahabbi ce kamar yanda take akan wanda baije hajji ba.

Wasu sunce babu layya akan mai hajji, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Kwaɗaitar akan yin layyah, bai halatta a hana mai hajji falala da samun kusanci ga Allah ba, ba tare da wani nassi akan hakan ba. Al-Muhalla ta Ibnu hazam (5/314-315).

Hanabila sukace: Layya ta halatta gamai aikin hajji. Kamar yanda ibnu qudama acikin Al-mugny (7/180) Ya faɗa.

Hadisi yazo daka Aisha Allah yaqara mata yarda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yiwa matansa layya a mina ahajjin bankwana. Bukhari (5239) da Muslim (1211) suka ruqaito.

Wasu malamai sunyi raddin hujja da wannan hadisin kamar ibnul qayyeem sukace: Abunda ake nufi da layya a hadisin shi ne hadaya. Duba zhadul Ma'adi (2/262-267).

Shaikul Islam da ibnul qayyeem sun zaɓi maganar masu cewa babu layya akan mai aikin hajji. Duba Al'iqna'a (1/409) da Al-Insaaf (4/110) Shaik Usaimeen ya rinjyar da wannan zancen.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments