Nasabar Dan Zina

    NASABAR ƊAN ZINA

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

    Mace ce mai aure ta yi zina dawani alokacin sai ciki ya shiga kuma tasani saita haife yaron shin yaron na mijin aure ne kona zinar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Babu makawa abunda ta aikata na zina tana matar aure yana cikin manyan laifuka, koda zina zunubi ce maigirma ita kaɗai to girman zunubin nakaruwa idan akace mai aure ta yi zina, shiyasa ma hukuncin mazinacin da bai taɓa aure ba shine bulala 100, wanda kuma yake da aure ko yataɓa aure shine ajefeshi harsai ya mutu.

    Tare da girman laifin data aikata da muninsa a al'ada da kuma hankali, babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa Allah yana farin ciki da tuban bawa kuma yana karbar tuban, Allah madaukakin sarki ya ce:


    ﻗﻞ ﻳﺂ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﺳﺮﺍﻓﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻻ ﺗﻘﻨﻄﻮﺍ ﻣﻦ ﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺟﻤﻴﻌﺎ

    Kagaya musu ya Annabi sallallahu Alaihi wasallam yaku bayina wadanda kuka wuce gona da iri wajan aikata saɓo kada ku debe tsammani daka rahmar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba ɗayansu, komai girmansu

    Ibnu kasir rahimahullah ya ce: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah, tana kuma bada labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daka aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu koda sunkai yawan kumfar kogi, matuƙar anyi tuba nagaskiya Allah yana gafarta su.

    Amma nasabar ɗan za'a jingina shi ga mijinki na aure ne, matuƙar yasadu dake, saboda faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam daya ce: ,( Ɗa na me aurene,) ma'ana ɗan na mijin dakike aure da shine koda ba'a saduwa da shi cikin ɗan ya shiga ba, indai kin kwanta da mijin bayan zinar ɗan nasane.

    An tambayi shaik bin baaz dangane da matar datake da aure kuma tanada 'ya'ya uku, ɗa na huɗun saita samu cikinsa ta hanyar zina, shin ya halatta ta zubda cikin ɗan? ko zata kyaleshi idan ta kyale cikin shin zata baiwa mijinta labari ko bazata bashi ba? sannan menene yake wajibi akan mijin a wannan halin?.

    Sai ya amsa dacewa: Bai halatta agareta ta zubda wannan cikin ba, abunda yake wajibi akanta shine tuba zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, da kuma kin bayyana al'amarin, ɗan data haifa kuma za'a jinginawa mijinta ma'ana ɗansane, saboda faɗin Annabi sallahu Alaihi wasallam ( Ɗa na mai aure ne mazinaci kuma uquba ce kawai tasa) Ma'ana wanda yai zina baida hakkin ajingina ɗan gareshi, shi kawai uqubar zinarce akansa.

    Fatawa bin bãaz (21/205).

    Da wannan majalisar fatawa ta kasar saudiyyah tai fatawa, Allah yagyara halayen mu gaba ɗaya.

    Wallahu A'alamu.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.