𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum warahmatullah. Malam ya qoqari Allah ya saka muku da mafificin alkhairi . Tambayata ita ce wani bawan Allah ne ya auri wata kafin su yi aure sai bai san tana da tabban quraje a bayanta ba, bayan sun yi aure sai ya ce ta tafi gidansu wai ai ko Manzan Allah S A W ma ya auri wata mata bayan sun yi aure sai ya tarar tana da wani ciwo a fatarta wanda bai sani ba , sai ya ce ta tafi gidansu, to malam ya abin yake! Shin gaskiya ne ko qarya ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám, Tabbas Malaman addinin Musulunci sun yi maganganu masu yawa akan auren da sai bayan da aka yi shi sai mijin ya sami matar da wata illa da yake da zaɓin ci gaba da zama da ita a haka ko kuma akasin haka. Ko kuma matar ta sami mijin da wata cuta da take da zaɓin ci gaba da zama da shi a haka, ko akasin hakan.
Daga cikin irin waɗannan cututtukan sun haɗa da taɓin hankali, da cutar kuturta, da shanyewar gaban namiji, da cutar da mace take da shi da ke hana saduwa da ita, da sauransu. Idan ɗaya daga cikin waɗannan ya bayyana ga mace ko na miji bayan sun yi aure, ba tare da an sanar da shi ko ita kafin auren ba, to a nan yana da zaɓin cigaba da zama da ita a haka, kuma yana da zaɓin rabuwa da ita, idan har bai sadu da ita ba, kuma ba su kaɗaita inganccen kaɗaita daga shi sai ita ba, to za a dawo masa da sadaqinsa da ya bayar, idan kuma ɗayan waɗannan abubuwa biyu ya tabbata, to ba za a dawo masa da sadakinsa ba, sai dai ya rabu da ita kawai, ko ya haqura a haka. Haka idan shi ke da wannan cutar ita ma tana da irin wannan zaɓi.
Akwai cututtukan da suka keɓanci maza kaɗai, akwai kuma cututtukan da suka keɓanci mata kaɗai, sannan akwai cututtuqan da suka yi tarayya a ciki. Ba kowane ɗan qaramin ciwo ne ake yi ma irin wannan hukuncin ba, akwai qananan cutuka da ba a hukunta su da wannan hukuncin, saboda idan aka jira kaɗan aka yi magani sukan zama kamar ba a yi su ba, kuma ba za su cutar da miji ko zamantakewar aurensu ba, to ba irin wannan ciwon ake magana ba.
Dubi ATTAAJU WAL'IKLEEL (5/144 - 151) domin qarin bayani.
Sannan game da maganar Auren Manzon Allah ﷺ. Tabbas akwai ruwayar da ke cewa: "Annabi ﷺ ya auri wata mata ƴar qabilar Gifaar, sai bayan da ya aure ta sai ya ga wani hasken tabo a qungurunta, sai ya ce mata: Ki sanya tufafinki, ki koma wurin iyalinki". Ahmad ya ruwaito wannan hadisin, amma hadisi ne mai rauni matuqa.
Daga cikin maruwaita hadisin akwai Jamilu bn Zaid.
Ibn Ma'een ya ce ba thiqa ba ne.
Imamun Nasá'i ya ce hadisinsa ba shi da qarfi.
Bukhariy ya ce hadisinsa ba shi da inganci.
Duba Irwaa'ul Galeel, Fiy Takhreeji Ahaadeethi Manaaris Sabeel (6/327).
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.