Ticker

6/recent/ticker-posts

HUKUNCIN SANYA HAKORIN MAKKA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya. Allah gafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum'a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taɓa ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam'a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori ɗaya ba zai yi tasiri ba.

Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.

Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi ﷺ ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al'umata, amma an halatta ga matayansu)

Allah ne mafi sani. 

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments