Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (2)

    Ga waɗanda suke biye da ni daga rubutun kashi na farko, na tsaya ne a cikin wancan rubutun a daidai gaɓar da na jefo wata tambaya dake cewa shin yaya rayuwar al'ummar Karai-Karai ta kasance ta fuskar addini da can a zamanin baya kafin shigowar addinin Musulunci da kuma addinin Kiristanci Najeriya? Domin an sani cewa duk wata daɗaɗɗiyar al'umma a cikin wannan ƙasa tana da wani lokaci a shekarun baya da tayi rayuwa ta gabannin zuwan waɗannan manyan addinan guda biyu wanda wasu al'ummun suke kiran shi irin wannan nau'i na imanin da suna Addinin Gargajiya.  Shi ne kuma tambayar da zamu amsa a yanzu.

    Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (2)

    Musaddam Idriss Musa
    Marubuci kuma Mai Binciken Tarihi
    07067132948
    realmusaddam@gmail.com
    Karai-Karai

    Mene ne Addinin Gargajiya?

    A sassauƙan harshe, idan aka ce addinin gargajiya a na nufin tafarkin imani da wata al'umma ko wani mutum ya ginu akai kafin bayyana ko kuma shigowar addinin musulunci izuwa yankin da yake. Shakka babu, duba da tarihin zuwa da bayyanar addinin Musulunci ga al'ummar Najeriya wanda bayan kafuwarsa ne aka kuma sake samun zuwan addinin Kiristanci ta hanyar Turawan mulkin mallaka, kowace al'umma da muka sani ko muke gani a yanzu suna da irin nasu hanyar da suke bi a matsayin tafarkinsu na imani. Kama daga masu bautar rana, bautar gumaka, bautar shuri, da kuma tsaunuka, da masu bautar aljanu ko iskokai har da ma waɗanda ke rayuwa hakanan ba tare da dogaro da wani abin imani ba dukkaninsu al'ummu ne da anyi su a cikin Najeriya kuma har yanzu akwai burbushin hakan a wasu sassa na arewaci da kuma kudancin Najeriya inda ake cigaba da samun masu gudanar da ire-iren wannan bautar duk da kuwa karfin tasirin da addinin Musulunci yayi a arewacin Najeriya da kuma tasirin da addinin Kiristanci yayi a shiyyar kudanci.

    Tunda kuwa Karai-Karai na daga jerin tsofin al'ummun cikin Najeriya, shin to mene ne addinin Bakarkarai na gargajiya kafin ƙarfafuwar musulunci?

    Domin amsa wannan tambayar wajibi ne mu yi duba ga wasu keɓaɓɓun siffofi wanda Karai-Karai na da suka ginu akai kuma suka kasance alamomi da ake danganta daɗewar al'umma da ma tsagin da ake kira ƙasarsu ɗin da su. Waɗannan siffofin su ne zasu bayyana mana asalin addinin Bakarkarai kafin zuwan musulunci da kuma yadda yake gabatar da rayuwarsa kai har ma da dalilai da kuma tarihin samuwar wasu abubuwa na siffofin Bakarkarai wanda har izuwa yanzu aka ganin Bakakarai ɗin da su amma ba tare da yawancin mutane wanda daga cikin su harda kaso mai yawa na wasu Karai-Karai ɗin sun san cewa ga ta yadda suka samo asali ga Bakarkarai ba wanda kuma hakan ya faru ne ba don komai ba sai don daɗewar zamani da kuma taƙaita bincike ba tare da faɗaɗa shi ba wanda ni kuma shi ne abinda na fi bada ƙarfi na akai kenan. Waɗannan siffofi da nake maganar cewa zasu zame mana jagora wajen sanin mene ne haƙiƙanin addinin Bakarkarai zan kasa su ne izuwa azuzuwa guda uku domin sauƙaƙa bayanin yadda za a fahimta, su ne kuma kamar haka:

    1. Duban Bakarkarai ta fuskar harshensa

    2. Duban Bakarkarai ta fuskar al'adarsa

    3. Duban Bakarkarai ta fuskar muhallinsa

    Bakarkarai Ta fuskar Harshensa

    Samuwar furucin; "Yahweh Ndagai nau!" da kuma alaƙar hakan ga wanzuwar addinin Bakarkarai a zamanin da.

    Kowa yayi imanin cewa, duk duniya da zaran ka faɗi kalmar "Yahweh Ndagai nau!" amsar da ɗan wata ƙabilar zai ba ka shi ne, "in ji Karai-Karai" saboda an san furuci ne da babu wata al'umma da take yinsa kuma babu wani guri da za ka ji shi sai ka shiga ƙasar Karai-Karai ko kuma ka ji hakan daga bakin wani Bakarkarai da ka haɗu da shi a wani wurin. Shin mutane nawa ne suke da masaniyar cewa wannan furucin yana da alaƙa da tafarkin addinin da Bakarkarai yake bi na kafin zuwan Musulunci a Najeriya? Na san dayawan izuwa yanzu sun fara cika da mamaki. To ga bayanin yadda abin yake.

    Yawancin Karai-Karai na wannan zamanin sun san cewa kalmar "Ndagai" tana nufin Allah ne amma idan kace musu ita kuma kalmar "Yahweh" ɗin fa sai ka ga sun yi shiru ko kuma su fara kame-kame na nuna kar a ce musu ba su iya yaren su ba. Wasun kuma kan yi ƙoƙarin fassara su ne a tare ta hanyar satar kwaramniyar nuna fushi ko damuwa da Hausawa ke yi da cewa ai "Yahweh Ndagai nau" abinda yake nufi shi ne, "Wayyo Allah na" kuma an samu nasarar ɗora matasan Karai-Karai na yanzu da dama akan ita wannan fassarar wadda a zahiri ba shi ne haƙiƙanin abinda jimlar take nufi ba ga kuma bayanin komai nan daki-daki.

    Duniyar masana ilimin tarihi sun yi imanin cewa saɓanin wasu harsunan Najeriya da aka tsamo su daga jikin wasu harsunan misali kamar yadda tarihi ya bayyana ƙabilar Pyem na jihar Filato da cewa asalin su Gobirawa ne, da kuma yadda tarihi ya nuna samuwar harshen Hausa a matsayin wanda ya fito daga jikin Haɓe da kuma Buzaye, da kuma Ngizimanci da shi ma aka tsamo shi daga Badanci, Bolanci kuma daga Tangale, Ngamanci daga Karai-Karai da dai sauransu, masanan sun nuna gamsuwar su ga tabbatuwar harshen  Karai-Karai a matsayin tsoho kuma daɗaɗɗen harshen da ya kwashi dubban shekaru a duniya. Ba kuma komai ne ya janyo haka ba illa samun tsofin kalmomi da aka yi a cikinsa kamar dai ita wannan kalmar ta "Yahweh" da nake batu yanzu akanta wanda kamar yadda na ambata, su kansu Karai-Karai ɗin da dama ba su san haƙiƙanin ma'anarta ba.

    Shakka babu, bayyanar kalmar Yahweh a cikin harshen Karai-Karai wata alama ce da za ta iya zama manuniya ga irin tafarkin addini da kuma turbar bauta ta al'ummar Karai-Karai a zamanin da domin gurare da bangarorin da al'ummar Karai-Karai suke amfani da kalmar a fili yake a bayyane kuma ƙarara cewa tana nuni ne da dangana, sallamawa, saduda, miƙa wuya a wani sa'in ma harda nuna buƙatar neman taimako na wanda ake ambato ɗin. Misali, idan Bakarkarai yayi aiki ya gaji lilis ko kuma saboda zama yayin da yake shirin zama ko miƙewa tsaye, ko kuma ya ga wani yana neman faɗuwa, ko aka ba shi wani labari na faruwar abu marar daɗi ko na al'ajabi, ko idan farin ciki yayi masa yawa da dai sauransu za ka ji yace, "Yahweh" ko kuma "Yahweh Ndagai nau" wadda ita wannan kalmar "Yahweh" ɗin ita kaɗai ɗinta abinda take nufi shi ne, "Ubangiji na" kamar yadda yake a cikin tsohon harshen Hibraniyawa wato harshen annabawa da kuma manzannin farko (ƙarin bayani yana gaba). Idan kuma aka haɗa kalmomin nan biyu, "Yahweh (Ubangiji na)" da kuma "Ndagai nau (Allah na)" abin ya fito a fili ƙarara cewa, "Yahweh, Ndagai nau" ɗin da ake ji Karai-Karai suna cewa, haƙiƙanin ma'anarsa shi ne, "Ubangiji na, Allah na"

    To kuma daga nan ne hankalin mu kuma zai koma ga tambayar shin wane irin Ubangiji ne "Yahweh" ɗin, shin shi ma shuri ne? Rana ce? Gunki ne kamar yadda wasu ƙabilun suke bautawa ko kuma dai wani abin ne na daban? Domin samun wannan amsar a biyo ni a rubutu na gaba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.