Ticker

6/recent/ticker-posts

Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (3)

 Waɗanda ba su karanta rubutu na farko da na biyu ba muddin ba su faro daga kansu ba to ba lallai ne su fahimci wannan kashi na ukun ba. A kashi na biyu na tsaya ne inda nake bayani akan furucin da al'ummar Karai-Karai suke yi na "Yahweh" da kuma "Yahweh, Ndagai nau" wanda bayan na bayyana ma'anar kalmar ta "Yahweh" na kuma faɗi abinda Bakarkarai yake nufi idan aka ji ya faɗi kalmar wanda duk mai karatu ya fahimta cewa akwai alakantuwa ta imani tsakanin Karai-Karai da kuma wannan kalma ta "Yahweh" ɗin wanda shi ne abinda zamu duba a yanzu.

Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (3)

Musaddam Idriss Musa
Marubuci kuma Mai Binciken Tarihi
07067132948

Karai-Karai

Asalin Kalmar "Yahweh" na harshen Karai-Karai

Bincike ya kai ni ga samo tabbataccen bayani akan ainihin inda kalmar Yahweh ta samo asali da kuma farkon ma'ana ko abinda take nufi kamar dai yadda tarihi ya nuna inda domin yin bayani cikin gamsassun hujjoji, zamu nazarci kalmar ta fuskar manyan addinai guda biyu da muke da su a yanzu haka a Najeriya kafin kuma mu ɗora da abinda ya zo daga rubutaccen tarihi domin abinda bincike ya nuna a game da daɗewar kalmar Yahweh shi ne cewa an fara amfani da ita ne tun a zamanin ƙarni na 6 Miladiyya wanda idan muka duba nisan daɗewar zamanin yayi tsufan da idan muna son yin batu akan sa to dole ne sai mun fara samar da bayanin wani abu da zai sa zukatan mu su samu nutsuwa akan abinda muke son yin bayani akai wanda domin yin hakan, dole ne mu yi duba ga neman sanin shin meye ne muka sani game da ƙarni na 6 ko kuma wane tarihi muke da shi game da wancan zamanin? Domin samun amsar wannan tambaya dole mu koma ga littattafan addinai domin su ne suke ɗauke da bayanai akan al'amuran da suka faru daga farkon wannan duniya har izuwa wanda zasu faru a ƙarshenta.

A duniyar mabiya tafarfin addinin Musulunci an yi imani da cewa Allah maɗaukaki, ya sauƙar da manzanni da kuma annabawa masu tarin yawa inda kuma a cikin Alqur'ani mai girma ya ambaci sunayen guda 25 daga cikin su tare da bada labaransu don al'ummar musulmi na yanzu su sansu kuma su yi imani da cewa sun wanzu a doran duniya a gabannin wanzuwar wannan al'ummar tamu ta yanzu. Daga cikin waɗannan annabawa 25, an kuma samu jerin sunayen 5 a matsayin annabawa mafi girman matsayi a wurin Ubangiji, inda guda daga cikin su shi ne Annabi Musa wanda wani abin ban sha'awa game da abinda muke son gabatarwa a nan shi ne, hatta a cikin littafin mabiya addinin Kiristanci sun yi imanin cewa Allah ya taɓa sauƙar da manzo daga manzanninsa masu girma da aka ambace shi da suna Prophet Moses wanda kuma shi manzon da su kuma Musulmi suke kiransa da suna Annabi Musa wanda shi suna Musa ɗin ya samo asali ne daga Larabci a matsayin harshen da aka sauƙar da Alqur'ani da shi. Ita kuma kalmar Moses ta samo tushe daga sabon alƙawari (New Testament) wanda aka samar da shi da harshen Turanci. To, ma shin me yasa nake kawo waɗannan bayanan? Saboda ƙoƙari muke mu koma ga ainihin lokacin da aka samo kalmar Yehweh da kuma ma'anarta tare da dubawa mu gani ko tana da bambanci da sanin da muka yi mata a cikin al'ummar Karai-Karai

 

Kundin da ake adana rubutaccen tarihin duniya na Encyclopedia Britannica ya bayyana cewa harshen da aka fara sanin kalmar Yahweh ta bayyana a cikinsa shi ne Hibraniyanci kuma daga nan ne asalin kalmar yake farowa wanda shi wannan yaren Hibraniyancin kamar yadda na bayyana a rubutu na biyu shi ne yare mafi daɗewa a duniya saboda shi ne yaren da annabawan farko da kuma manzanni suka yi amfani da shi wanda aka bayyana cewa bayan shuɗewarsa ne aka samui dandazon waɗannan harsunan da muke amfani da su a yau. Idan muka koma ga Britannica, bayanin ya ɗora da cewa kuma zamanin da aka fara amfani da kalmar "Yehweh" ɗin a cikin yaren Hibraniyancin shi ne zamanin ƙarni na 6 lokacin da aka sauƙar da ita ga Annabi Musa (Prophet Moses) a matsayin sunan Ubangijinsa da zai yana bautawa saɓanin sauran abubuwan bauta da al'ummarsa ta wancan zamanin suke bautawa wanda a littafin mabiya addinin Musulunci Surah ta 2 (Baqarah) da bayanin da ta ƙunsa ya kasanceu babban abin misali na daga ire-iren abubuwan da mutanen wancan lokacin suke bautawa kuma shi ne dalili na aika musu shi Annabi Musa tare da ita wannan kalma ta Yehweh kamar yadda bayanin ya zo a matsayin cewa shi ne yadda sunan Ubangiji wato Allah ya kasance a cikin harshensa na asali domin ita kalmar Allah asalinta na komawa ne ga harshen Larabci wanda kuma bayyanannen abu ne dama cewa Annabawa na da waɗanda aka fara aikowa sun fito ne daga wasu al'ummun waɗanda ba Larabawa ba.

Kenan ashe "Yehweh, Ndagai nau" ɗin da tsofaffi kuma dattawan Karai-Karai suke faɗa wanda na bayyana mana abinda yake nufi ma'ana "Ubangiji na, Allah na" abu ne da yake da asali na daɗewa tare da yin nuni ga irin tafarkin imanin da al'ummar suka ginu akai.

Sai dai kuma wace hujja ce ake da ita wadda za ta nuna cewa al'ummar Karai-Karai suna da wata dangantaka ta harshe da kuma tsohon harshen annabawa na farko ko kuma dai kawai bayanin duk ya ƙare a hasashe ne? Domin samun wannan amsar sai a biyo ni a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments