GARGAJIYA: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (I)

    Wannan gajeren taƙaitaccen tsakure ne daga abubuwan da nake kan cigaba da tattarowa gami da faɗaɗa bincike na a kai a kan rubuce-rubucen da nake na tarihin al'ummun arewacin Najeriya. Inda duk da cewa ba tarihin al'ummar Karai-Karai ne zan bayar kai tsaye ba, zan so na fara ne da bayar da wasu muhimman bayanai a matsayin matashiyar shi wannan rubutu. Zan fara da wannan tambayar:

    GARGAJIYA: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (I)

    Musaddam Idriss Musa 
    Marubuci kuma mai binciken tarihi
    07067132948
    realmusaddam@gmail.com

    Karai-karai

    Su waye Karai-Karai?

    Kafin na bayyana su waye al'ummar Karai-Karai, yana da kyau ƙwarai fara sanin me kalmar ta ƙunsa a matakin farko domin ita kalmar "Karai-Karai" ɗin tana da ma'anoni ne guda uku, kuma su ne kamar haka; na farko, Karai-Karai suna ne na wata al'umma daga al'ummu mazauna Najeriya. Har ila yau, kalmar tana nufin yaren ita wannan al'ummar ma'ana shi ma harshen da take magana da shi ɗin a na kiransa ne da kalmar "Karai-Karai". Ma'ana ta ukun kuma na komawa ne ga ƙasarsu ko lardinsu wato inda kowa ya sani da cewa yanki ne da ita wannan al'umma suka samar aka kuma wayi gari da sanin cewa su ne mutanen da suka samar da wajen daga daji izuwa gari. Wannan dalili yasa Hausawa fatake na da masu yawon kasuwanci suke amfani da ƙarin wasu kalmomin yayin da suke amfani da kalmar don nuna akan me suke magana domin bambace su ta hanyoyi guda uku:

    1. Al'ummar Karai-Karai: yayin da suke batu akan mutane 'yar ƙabilar Karai-Karai.

    2. Ƙasar Karai-Karai: yayin da suke magana akan lardin Karai-Karai.

    3. Harshen Karai-Karai: a lokacin da suke magana akan yaren al'ummar.

    Idan muka koma ga tambayar can dake sama, su waye Karai-Karai?

    Karai-Karai wata al'umma ce daga al'ummun Najeriya da a ƙidayar shekarar 1963 aka bayyanata a matsayin ƙabila ta 23 daga cikin ƙabilu sama da 300 da ake da su a faɗin Najeriya. Wannan ya bayyana mana a fili ƙarara matsayin al'ummar na zamowa ɗaya daga manyan al'ummun Najeriya. Kodayake, tun ma kafin wannan lokacin yaren al'ummar na daga jerin rukunin manyan harsunan Najeriya 10 daka zaɓa domin yin wallafe-wallafe da su a Najeriya a cikin shekarar 1953 ƙarƙashin hukumar NORLA.

    Al'umma ce da ta kafa ƙasarta tsakanin tsohuwar daular Borno da kuma Ƙasar Hausa ta kuma zamo mahaɗin wanzar da zaman lafiya a tsakanin manyan daulolin biyu saboda kyakkyawar alaƙar dake tsakanin ta da al'ummun waɗannan ƙasashen. Inda yankin da ya zamo gurbi na wannan ƙasar tata a yanzu ya haɗa da sassan jihohin Yobe, Gombe, Bauchi da kuma Jigawa. Babban kirarin da ake musu shi ne Karaidu Goyon Fata saboda fasahar su ta iya jima da sarrafa fatun dabbobi izuwa abubuwan amfani na yau da kullum kama daga na dangin kayan farauta izuwa na amfani a cikin gida ciki har da su takalma, kayan sakawa da ma rigar goyon jarirai don sauƙaƙawa matayensu a wajen yin raino da kuma goyo a yayin ayyukan gida, tafiye-tafiye da kuma wurin aikin gona. A takaice mutane ne, masu baiwa ta iya maida baƙi ya koma fari a fagen ilimin kimiyya da fasaha.

    Shin to yaya rayuwar wannan al'umma ta kasance ta fuskar addini? Wannan ita ce manufa kuma abinda wannan rubutun zai karkata akai kenan sai ku biyo ni a rubutu na gaba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.