Bismillahi
Allah madawwami
Shi mahallicin mu Rahimi
Mai yawaita alheri magami
wanda ya yi ɗari ya yi gumi
Wanda ya yi rani da damina.
Komai yanayi
mai ma'ana
Dan hikimominsa Rabbana
Masu yawa ko a ko'ina
Tabaraka Sarkin sarakuna
Ya sa ni'imomi ga damina.
Nomau manomi
mai dariya
Tsaya inai maka tambaya
Shin me yake saka dariya
Ko kana da jikkar zinariya
Koko ka ci riba da damina.
Sai ya kada
baki da hanzari
Ya ce da ni kai albishiri
Yau zuciya ta ta yi fari
Zaƙin ta ya zarce sukari
Na ga alama ta damina.
Daga kai ka
dubo samaniya.
Ka ga gajimarai na tafiya
Kafin na bushe da dariya
Sai na ji tsawa da walkiya
Suna bushara da damina.
....................................
....................................
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.