Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Allah Na Gafarta Zunubai Duk Yadda Suke?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamou aleikoum, malam, ina cikin matsanantcin tashin hankali, ALLAH ya jarabche ni ina gani kamar saɓon da nake Ciki ne ALLAH ya jarabche ni da hakan, na bi hanyoyi da yawa dan neman mafita har da malaman tsibbu amma abun se kara chittira yake, shin malam idan na koma ga ALLAH, ALLAH zai karɓa min? Dan Na ji wani malami na cewa matukar bawa be yi hankuri ya meda al-amarinsa ga ALLAH tun da farko, idan se da ya yi iya iyawarshi ya kasa samun biyan bukata, to wai ALLAH ba ya karɓar irin wannan adou'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa Allah mai gafarta wa bawansa dukkan zunubansa ne matuƙar ya nemi tubar, duk yadda zunuban mutum suka kai wurin yawa, idan bawa ya nemi gafarar Allah, to Allah zai gafarta masa waɗannan zunubai, ko da shirka bawa yake yi, idan har ya daina kuma ya tuba cikakkiyar tuba kafin ya mutu, to lallai ana fatan Allah zai gafarta masa wannan shirka ɗin, matsalar ita ce idan har mutuwa ta riski mutum yana shirka kafin ya tuba, Allah Ta'ala a wurare mabambanta a Alƙur'ani ya ce:

"Ka faɗa masu (ya Manzon Allah) Ya ku bayina waɗanda suka aikata wa kawunansu zunubai, kada ku ɗebe tsammani da rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya, lallai shi Mai gafara ne mai jin-ƙai". Suratuz Zumar: 53.

A wani wurin kuma ya ce:

"Shi ne Mai karɓar tuba daga bayin sa, kuma yana share munana, ya kuma san abin da kuke aikatawa". Suratus Shúra: 25.

Sannan kuma shi ne ya ce: "Shin ba za su tuba zuwa ga Allah su nemi gafararsa ba, Allah mai gafara ne mai jin-ƙai". Suratul Má'ida: 74.

‘Yar uwa dukkan waɗannan ayoyi suna nuna cewa idan bawa ya tuba zuwa ga Allah, lallai Allah zai gafarta masa waɗannan zunubai nasa, duk yadda ko zunuban nasa suke wurin yawa da muni, babban abin da ya dace ki yi shi ne ki tuba zuwa ga Allah bisa bin hanyar ‘yan tsibbu da kika ce kin yi domin neman biyan buƙatunki, saboda harka da ‘yan tsibbu hanya ce ta zuwa Jahannama kai tsaye.

Kuma ki yi dauwamammiyar nadama a kan wannan babban laifi, ki ɗaura niyar ba za ki sake aikata wani laifi makamancin wannan ba, tare da yawaita yin istigfári, lallai idan kika yi hakan in Allah ya so duk Allah zai share maki waɗannan laifuka, saboda Allah ya kasance mai share munana da tabbatar da kyawawa ne, kuma ya kasance mai tsananin tausayi da jin-ƙan bayin sa ne, mai karɓar tubarsu ne a duk lokacin da suka nemi tubar. Hakan ya sa na fi tunanin wata ƙila ke ce ba ki fahimci abin da wancan malami yake nufi ba.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments