Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Azumtar Sittu Shawwaal

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm malam. Dan Allah Ina so na ji falalar sitta shwwal. Wannan shi ne tambaya ta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Azumin shittu shawwaal Mustahabbine Sunnah ne da'akeson mutum ya daure ya aikata, saboda akwai falala mai girma a cikin azumtar kwanaki shida na watan shawwal, da kuma lada Babba, wanda ya azumta za a rubuta masa ladan azumin shekara guda, kamar yanda ya tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam kamar yanda yazo a cikin hadisi Abu Ayyubar Ansary Allah yaƙara yarda da shi ya ce: (Wanda ya Azumci watan ramazhaan sannan yabi bayansa da Azumin kwanaki shida na watan shawwal kamar ya azumci zamani guda ne.

Muslim, Abu Dauda, Turmuzy, Nisa'i, Ibnu Majah

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya fassara wancan hadisin da fadinsa ya ce: { Wanda ya Azumci kwana shida na watan Shawwal bayan ƙaramar Sallah, ya kasance cikwan shekara (Wanda ya aikata kyakkyawan aiki yanada lada goma na kwatan-kwacinsa) Awata ruwayar Allah yana maida ladan kyakkyawan aiki da goma irinsa, watan Ramaān yana amatsayin watanni Goma, Azumin kwanaki shida na watan Shawwaal sune cikwan shekara.

"Nisa'i da Ibnu majah, hadisin yana cikin #Saheehu Targeeb wattarheeb, (1/421) ibnu kuzaima ya ruwaitoshi da lafazin [ Azumin watan Ramaān yana dai-dai da goma irinsa,

Azumin sittu shawaal yana dai-dai da wata biyu, inka haɗa yazama azumin shekara guda.

Daga cikin fa'idojin masu muhimmanci na Azumtar Sittu shawwaal shi ne cike gibin tawayar data faru a cikin Azumin farillah na Ramaān, saboda mutumba ya kubuta daka gajiyawa ko aikata zunubi wanda zai tasiri a azuminsa, ranar ƙiyama za a dauka daka ayyukansa na nafila acike masa gibin daya bari na tawayar ayyukansa na wajibi.

Kamar yanda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Farkon Abun da za a fara yiwa ɗan Adam hisabi a kansa ranar Alƙiyama daka cikin Aikinsa shi ne Sallah, Allah zai cewa mala'ikunsa kuduba kuga bawana yana da wani aikin na nafila, idan yanada nafila sai ya ce: kucikewa bawana gibin daya samu a aikinsa na farillah da aikinsa na nafila, sannan sai aci gaba da karbar sauran ayyuka a kan hakan.

Abu dauda.

Ataƙaice azumin Sittu shawwal akwai hikimar Allah wajan shar'antashi, Sannan yanada fa'idoji masu tarin yawa.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments