Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Azumtar Sittu Shawwal Kafin Rama Azumin Da Mutum Yasha Awatan Ramadan?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Ya Halatta Azumtar Sittu Shawwal Kafin Rama Azumin Da Mutum Yasha Awatan Ramaān?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai Sun yi Saɓani a kan Wannan Mas'alar.

Wasu sun tafi a kan Bai halatta yin Azumin nafila kafin yin na ramuwa ba, wanda ya aikata hakan zai Samu zunubi.

Sukace: Ba'ayin nafila kafin farillah.

Wasu Malaman kuma sukace: Ya Halatta yin Nafila kafin farillah matukar akwai yalwataccen lokaci, lokacin da zai iya yin nafilar Sannan yazo ya yi farillah din.

Kamar ya yi nafila kafin ya yi Sallar farillah, Misali Sallar Azahar lokacinta yana shiga da zarar rana ta yi zawali, yana ƙarewa idan inuwar kowanne abu ta yi biyunsa, zai iya jinkirtata izuwa ƙarshen lokacinta, A wannan lokacin ya halatta ya yi Nafila, domin lokacin yalwataccene.

Wannan Zancen shi ne zancen jamhur din malamai, shaik Usaimeen yazabi wannan zancen, domin shi ne yafi hujja mai ƙarfi yafi kusa da dai-dai.

Wanda ya yi azumin nafila kafin yarama na farillah Azuminsa ya yi, Bawani zunubi a kansa.

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

 ومن كان مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر. البقرة /185.

Wanda yake ahalin rashin lafiya, ko yake ahalin tafiya sai ya rama awasu kwanaki ƙididdigaggu.

Ma'ana yarama awadansu kwanakin, Allah bai ƙayyade kwanakin dacewa Dole sai sun kasance ajereba, da'ace ya ƙayyadesu da jerantawa daya zama dole a gaggauta ramuwa, wannan ya nuna al'amarine mai fadi.

 Duba Sharhin Mumti'i Mujalladi na (6/ shafi Na 448)

Ataƙaice ya halatta yin Sittu shawwal kafin ramuwar Ramadan

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments