𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne
Hukuncin Azumin Kwanaki Shida Na Watan Shawwal.?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Azumin kwanaki
shida na watan shawwal bayan gama azumin farillah na Ramadan sunnah ne kuma
mustahabbine amma bawajibi ba ne, An shar'antawa mutum azumtar kwanaki shida na
watan shawwal, a cikin hakan akwai falala maigirma da kuma lada mai yawa, duk
wanda ya azumce su kamar ya yi azumin
shekara gudane, kamar yanda ya inganta daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam, a
cikin hadisin Abu ayyubal Ansari yardar Allah takara tabbata agareshi, Manzan
Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: " Duk wanda ya azumci watan Ramaḍān
sannan yabishi da azumin kwana shida a cikin watan shawwala kamar ya azumci
zamani ne.
Muslim da Abu
dauda da turmuzi da ibnu majah da Nisa'i sun ruwaici wannan hadisin.
Annabi
sallallahu Alaihi wasallam yafassara wancan hadisin da fadinsa(Wanda ya azumci
kwana shida bayan karamar sallah ya kasance cikwan shekara guda ne.
"ibnu
majah da Nisa'i, hakama yazo a cikin sahihul targeeb wattarheeb, (1/421).
Ibnu kuzaimah
ya ruwaito shi da lafazin (Azumin
watan Ramaḍān
yana dai-dai da kwatan kwacinsa sau goma, azumin sitta shawwal kuma yana
amadadin azumin wata biyu, sai ya zamto azumin shekara guda kenan.
Hakika malaman
fiƙhun
hanabila da shafi'iyyah sun bayyana karara cewa " azumin watan Ramaḍān
yana dai-dai da azumin shekara guda na wajibi, idan bahakaba ninka ladan aiki hukunci
ne daya game komai, har azumin nafila, domin duk wani kyakkyawan aiki yana
dai-dai da kamarsa guda goma.
Yana daka
cikin fa'idoji masu muhimmanci dangane da azumi shida a cikin watan shawwal
cike gurbin tawaya da mutum yasamu a cikin azumin farillah na Ramaḍān,
saboda mai azumi bazai kubuta daka wata tawaya ko zunubi maitasiri a cikin
azuminsa daya aikata a cikin watan Ramadan ba, ranar alkiyama sai adauka daka
nafilolinsa acike masa wancan gurbi na tawaya daya samu a cikin ayyukansa na
wajibai, saboda haka Annabi sallallahu Alaihi wasall ya ce: " Farkon abun
da za a fara yiwa mutane hisabi a kansa ranar alkiyama daka cikin ayyukansu shi
ne sallah, Allah madaukakin sarki zai cewa mala'iku, Alhalin yasani kuduba
sallar bawana yacikata koya tauyeta, idan tacika kurubuta masa ita cikakkiya,
idan kuma kunsamu wata tawaya toku duba shin bawana yanada nafiloli, sai ya ce:
kucikawa bawana farillarsa da nafilarsa, sannan saiku dauki sauran ayyukansa a
kan haka.
Ma'ana duk
wata ibada idan aka samu ranar alkiyama bawa yanada wataya a cikin wacce aka
wajabta masa to za a duba yanada nafila ta irin wannan ibada sai adauka daka
nafilarsa acike masa gibin ɗaya
samu afarillarsa.
WALLAHU
A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...w
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.