Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Haɗa Sittu Shawwal Da Ramuwar Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam idan ana binka ramuwar azumi za ka iya niyya biyu: wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadana a guda ɗaya? don Allah mlm taimaka min da bayani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalamu, To 'yar'uwa kowanne daban ake yin sa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za a haɗa su da niyya ɗaya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma'a, za mu fahimci haka, a cikin faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Duk wanda ya azumci Ramadana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara" Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban.

Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal" ya sa wasu malaman sun tafi a kan cewa: bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a: sharhurmumti'i 6\443.

Allah ne ma fi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi


Post a Comment

0 Comments