𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Don Allah ya halatta a gina gida a ba wa Kiristan haya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum
assalam.
Ya halatta
mana, tun da Annabi S.A.W. ya yi mu'amala da Yahudawa kuma ya mutu silkensa na
yaki yana wajan Bayahude saboda Sha'ir din da ya amsa kamar yadda ya zo a
hadisi ingantacce
Akwai gonakin
Annabi S.A.W. da na sahabbai a wajan Yahudawan Khaibar inda suke aiki a cikinsu
suke bawa musulmai rabin abin da ya fito na amfani kamar yadda ya tabbata a
Sahihu Al-bukhari
In har an san
zai yi ɓarna ko saɓon Allah a cikin gidan bai
halatta a ba shi hayarsa ba, Allah maɗaukakin
sarki yana cewa: "Kada ku rika taimakekeniya wajan aikata saɓo" Suratu Al'ma'idah
aya ta: 2.
A cikin Suratu
Al-mumtahanah Allah ya yi bayani cewa: Ana iya kyautatawa kafirai a kuma yi
musu adalci mutukar ba sa yakar musulmai, hakan sai ya nuna halaccin ba su haya
Allah ne mafi
sani
Dr, Jamilu
Zarewa
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.