Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Akwai Zunubin Da Allah Bai Yafewa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm mlm anwuni lpia mlm inada tanbaya mlm akwai zunubin da Allah baiyafewa aduniya ko ka tuba???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Laifin Shirka babba shi ne wanda Allah () ba Ya yafewa. Saboda fadin Sa:

إِنَّ اللَّهَ لَا يَغفِرُ أَن يُشرَكَ بِهِۦ وَيَغفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ وَمَن يُشرِك بِاللَّهِ فَقَدِ افتَرَىٰٓ إِثمًا عَظِيمًا" [ النساء: ٤٨]

MA'ANA: “Lalle ne Allah ba ya gafarta a yi shirka gami da shi, kuma amma Yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda Ya so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne ya kirkiri zunubi mai girma.” (Suratun Nisa’i: 48).

Wannan ayar na nuna duk wanda ya haɗu da Allah alhali ya mutu yana Shirka, to Allah ba zai gafarta masa ba, kuma wuta ita ce makoma a gare shi.

Amma idan mutum ya yi tuba, tuba keɓantacciya tun a duniya kafin ajalinsa, to Allah Mai yawan gafara ne, Zai iya yafe masa idan Ya so.

Babu wani laifin da ya tabbata cewa idan mutum ya tuba tun a duniya Allah ba zai amshi tubar shi ba. Ni dai ban san wannan laifin ba.

WALLAHU A'ALAM.

🏿Ayyoub Mouser Giwa.

08166650256.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments