𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum warahmatullahi wabarakatuhu. Malam dafatar antashi lafiya, kuma irin taimakon da kake da kar6a fatawowin jama'a, Allah ya saka maka da gidan aljanna, iyalan ka Allah ya ƙara sanya musu albarka ya kiyaye maka su.
Malam tambaya
ta anan ita ce, nine nake aikata aiki maras kyau. Na yi tuba na yi tuba, har alƙawari na
yiwa Allah cewar ba zan sake ba bayan na yi sallah na yi addu'a, Amma saida na
sake aikata wannan abin bama sau 1 kuma bakomai ba ne illa kallon fina-finan
batsa. Tau malam don Allah yanzu mene ne hukunci na a wurin Allah. Kuma ka taimaka
min da shawara da Allah.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Aikin Zunubi
yana daga cikin abin da Ubangiji yake jarabtar bawansa da shi. Kuma ya buɗe mana hanyar tuba da kuma istighfari domin
samar mana da mafita daga Ƙangin zunubi.
To amma ita
tuba ba ta zama cikakkiya kuma mai amfani ga bawa har sai mai yinta ya cika
sharudan nan guda uku:
1- Yin nadama
bisa laifukan baya.
2- Rabuwa da
aikin saɓon nan take
ba tare da jinkiri ba.
3- Ɗaukar
niyyar ba zaka sake aikatawa ba, har abada.
- To idan kuma
akwai hakkin wani, wajibi ne ka mayar masa, ko kuma ka nemi yafewarsa.
To duk tuban
da ta cika waɗannan
sharudan ita ce cikakkiyar tuba. Kuma ko da Allah ya jarrabi mutum da komawa
cikin zunubin ba za a kirashi Mayaudari ba. Kuma idan ya sake tuba Allah zai
gafarta masa. ko da zai yi haka fiye da sau dubu.
Shi ne wanda
Manzon Allah ﷺ yake
cewa: "MAI TUBA DAGA ZUNUBI KAMAR WANDA BASHI DA ZUNUBI NE".
Amma ya
zamanto lokacin da mutum yake tuba a kan harshensa ne, amma a cikin zuciyarsa
yana jin zai koma cikin zunubin, to wannan shi ne Mayaudari. Tubansa ba
Karbabbiya bace. Kuma Allah yakan yi azaba ga masu yin haka.
Hanyar da zaka
bi domin kange kanka daga wannan shi ne:
- Kodai ka
rabu da waya mai shiga internet, Ko kuma ka dena shiga Shafukan batsa.
- Ka kori shaiɗan daga kusanci dakai ta hanyar
yawaita Karatun Alƙur'ani da zikirin Allah ako yaushe.
- In da hali
kaje kayi aure. In babu hali ka yawaita azumi. Idan kuma kana da auren, to duk abin
da ke jikin wadancan Shaiɗanun
da kake kallo, to akwaishi jikin Matarka.
- Ka rika yin
sallar nafila raka'a biyu ko huɗu
kana Ƙara
tuba duk lokacin da shaiɗan
ya rinjayeka ka aikata zunubi.
- Babban
al'amari shi ne Kaji tsoron Allah ka rika tuna gamuwarka dashi. Kuma ka, sani yana
tare dakai aduk inda kake.
Allah ya
shiryeka tare damu da zuriyarmu baki ɗaya.
Ya kiyayemu daga Sharrin Shaiɗanun
fili da ɓoye da kuma
sharrin Miyagun laifukanmu.
WALLAHU
A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
ƘARIN BAYANI
HUKUNCIN MAI MAIMAITA ZUNUBI DA KUMA
MAIMAITA TUBA A MUSULUNCI
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Mene ne matsayar shari’ar
Musulunci game da mutumin da ya fada cikin babban zunubi, sannan ya ji tsoron
Allah ya yi tuba ta gaskiya tare da kudurin ba zai sake komawa ba, sai dai
bayan wani lokaci sai ransa ya sake rinjayarsa ya koma ga wannan zunubin,
sannan ya sake tuba? Wannan lamari ya kasance yana maimaituwa a gare shi; bai
daina zunubin ba, kuma bai fasa tuba ba. Shin ana daukar wannan mutumin a
matsayin mayaudari, kuma shin Allah yana karbar irin wannan tuban?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Tsira da
amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW). Hakika,
rahamar Allah tana da fadi, kuma Shi Ubangiji ne Mai yawan gafara ga bayinsa
muddin ba su yanke kauna daga rahamarsa ba. Shi zunubi yana daya daga cikin
abubuwan da Allah Yake jarrabar bawansa da su domin ya ga kankan da kansa da
komawarsa zuwa ga Mahaliccinsa.
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana cewa kofarsa a bude take ga
kowa, komai girman laifin mutum. Allah Yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki:
۞ قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا
عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ
يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
"Ka ce: Ya ku bayina waɗanda suka yi wa kansu ƙetaren
haddi (da zunubai)! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah yana
gafarar zunubai gaba ɗaya. Lalle Shi, Shi ne Mai yawan gafarar, Mai yawan jin
ƙai." (Suratuz Zumar: 53)
Wannan aya tana nuna mana cewa babu wani zunubi da ya fi
karfin gafarar Allah. Babban abin lura a nan shi ne, muddin bawa ya san cewa
yana da Ubangiji wanda yake gafarta zunubi kuma yake kama mutum da zunubi, to
muddin ya tuba, Allah zai yafe masa.
Ma’anar Tuba ta Gaskiya da Sharrudanta
Tuba ba kawai furucin harshe ba ne; tana da wasu muhimman
shika-shikai da malamai suka fitar daga nassoshi, wadanda idan babu su, tuba ba
ta zama karbabbiya. Wadannan sharruda su ne:
1. Yin nadama (An-Nadam): Mutum ya ji radadi a zuciyarsa na
sabon da ya yi wa Allah.
2. Barin zunubin nan take (Al-Iqla’): Ba za a yi tuba ana ci
gaba da laifin ba.
3. Kudurin rashin komawa (Al-Azm): Mutum ya kudurce a
zuciyarsa cewa ba zai sake komawa ba har abada.
4. Maida hakkin mutane: Idan laifin ya shafi mutunci, dukiya,
ko ran wani, dole ne a nemi yafiya ko a maida masa hakkinsa.
Idan bawa ya cika wadannan sharruda, Allah yana karbar
tubansa ko da kuwa daga baya rauninsa ya sanya ya sake fada wa. Ba a kiran sa
mayaudari muddin a lokacin da yake tuban, ya kudurce ba zai koma ba. Amma wanda
yake tuba da harshe yana nufin zai sake aikatawa nan gaba, to wannan shi ne mai
wasa da tubansa.
Maimaita Zunubi da Maimaita Tuba
Musulunci ya fahimci raunin dan Adam. Annabi (SAW) ya kawo
mana labarin wani bawa wanda ya yi zunubi sau da yawa, kuma duk lokacin da ya
yi ya ce: "Ya Ubangiji na yi zunubi Ka yafe mini." Sai Allah Ya ce:
"Bawana ya sani cewa yana da Ubangiji Mai gafara, na gafarta masa."
Manzon Allah (SAW) ya fada a cikin wani Hadisi na Kudusi:
إِنَّ عَبْدًا أَذْنَبَ ذَنْبًا،
فَقَالَ: رَبِّ أَذْنَبْتُ ذَنْبًا فَاغْفِرْ لِي، فَقَالَ رَبُّهُ: أَعَلِمَ
عَبْدِي أَنَّ لَهُ رَبًّا يَغْفِرُ الذَّنْبَ وَيَأْخُذُ بِهِ؟ غَفَرْتُ
لِعَبْدِي، ثُمَّ مَكَثَ مَا شَاءَ اللَّهُ ثُمَّ أَذْنَبَ ذَنْبًا... (إلى أن قال
في الثالثة أو الرابعة): فَلْيَعْمَلْ مَا شَاءَ
"Lalle wani bawa ya aikata zunubi, sai ya ce: 'Ya
Ubangijina, na aikata zunubi, Ka gafarta mini.' Sai Ubangijinsa Ya ce: 'Shin
bawana ya sani cewa yana da Ubangijin da yake gafarar zunubi kuma yake kama
mutum da shi? Na gafarta wa bawana.' Sannan ya zauna tsawon lokacin da Allah ya
so, sai ya sake aikata wani zunubin... (har zuwa karshe inda Allah Yake cewa):
'Ya aikata duk abin da ya ga dama (muddin zai kasance yana tuba bayan kowane
zunubi, Zan rika gafarta masa).'" (Sahihul Bukhari da Muslim)
Wannan hadisi yana nuna cewa idan bawa ya sake komawa zunubi
bayan ya tuba, hakan ba ya bata tubansa na farko. Abin da ake bukata shi ne ya
sake yin wata sabuwar tubar.
Kwadaitarwa kan Yawan Istigfari
Duk yadda zunubi ya yawaita, kada bawa ya karaya. Allah
Madaukakin Sarki ya siffanta kansa da "Al-Ghaffar", ma'ana Mai yawan
gafarar da ba ta karewa. Annabi (SAW) ya ce:
كُلُّ بَنِي آدَمَ خَطَّاءٌ، وَخَيْرُ
الْخَطَّائِينَ التَّوَّابُونَ
"Dukkan 'yan Adam masu kuskure ne, kuma mafi alherin
masu kuskure su ne masu yawan tuba." (Sunan al-Tirmidhi)
Wannan yana nuna mana cewa dabi'ar dan Adam ce yin kuskure,
amma dabi'ar daukaka ita ce komawa ga Allah. Kar ka taba barin shaidan ya
yaudare ka da cewa "ai tubarka ba za ta karbu ba tunda ka saba
alkawari". Wannan ita ce babbar yaudarar shaidan domin ya sa ka ci gaba da
zunubin har mutuwa ta zo maka ba ka tuba ba.
Hattara: Kada a Dogara da Tuba a Ci Gaba da Zunubi
Duk da cewa kofar tuba a bude take, hakan ba yana nufin mutum
ya raina zunubi ba. Yin gangancin aikata zunubi da nufin "zan tuba daga
baya" hatsari ne babba, domin mutum ba shi da tabbacin zai rayu har
lokacin da zai yi tubar. Allah yana cewa:
وَلَيْسَتِ التَّوْبَةُ لِلَّذِينَ
يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ حَتَّىٰ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ
إِنِّي تُبْتُ الْآنَ
"Tuba ba ta zama ga wadanda suke aikata miyagun ayyuka
har lokacin da mutuwa ta halarci dayansu sai ya ce: 'Lalle ni yanzu na
tuba.'" (Suratun Nisa'i: 18)
Kammalawa
Hukuncin wannan mutumi da yake komawa zunubi sannan ya sake
tuba shi ne: Tubansa karbabbiya ce muddin ya cika sharrudan tuba a lokacin da
yake yin ta. Ba a kiransa mayaudari matukar zuciyarsa tana yin nadama. Abin da
ya kamata ya yi shi ne:
1. Ya yawaita ayyukan kwarai domin kyawawan ayyuka suna
tafiyar da munana.
2. Ya nisanci wuraren da suke tunatar da shi zunubin ko
abokan da suke tura shi zuwa ga laifin.
3. Ya kasance mai yawan tsoron Allah da kankan da kai.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu ikon yin tuba ta
gaskiya (Tawbatan Nasuha), kuma Ya sa mu cika da imani.
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.