Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Alhali Tana Azumin Sittu Shawwal?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Alhali Tana Azumin Sittu Shawwal?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Mai Azumin nafila shi ne sarkin kansa, yanada damar yakai azuminsa koya karyashi, sai dai yakai azumin shi ne yafi.

Imamu Ahmad ya Ruwaito hadisi (26353) daka Ummu Hani Allah yaƙara musu yarda Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yashiga dakinta, ya buƙaci takawo masa Abun sha yasha, Sannan Sai ya ba ta tasha, saita ce: Ya Manzan Allah na kasance ina Azumi sai Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Mai Azumin Nafila shi ne sarkin kansa, inyaga dama ya yi Azumin ingaya dama ya karya Azumin)

Albani ya ingantashi a cikin Sahihul jami'i (3854).

Wanda yadau azumin sittu shawwal, sai yaso yaci Abunci yana da wannan damar, da cin abunci zai karya ko da jima'i ko da wanin haka.

Idan mace ta ɗauki Azumin Sittu shawwal Batare da Izinin mijinta ba, mijin yana da damar ya kira ta zuwa jima'i, kuma dole ne ta Amsa masa.

Idan Kuma ta dauki Azumi da izinin mijinne bashi da damar ya lalata mata Azuminta, dole ya haƙura ya barta takai azuminta.

Amma idan ya Matsa a kan dole sai ya yi jima'i da ita, Abun da yafi shi ne ta Amsa masa.

Amma Bai dace ba yatursasa mata ɓata Azuminta.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments