Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Karya Azumin Nafila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Wanda Ya Ɗauki Azumin Sittu Shawwal Sai ya Karya shi, Shin Zai Rama Wannan Azumin Bayan Ya Kammala Sittu Shawwal Ɗin, Sai ya Zama Ya Azumci Kwana Bakwai Kenan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai Sun yi Saɓani a kan wanda ya Ɗauki Azumin nafila Shin dole ne sai ya kaishi ko ba tilas ba ne?

Wasu Sukace: Ba tilas ba ne kai Azumin nafila, kamar yanda yake a mazhabar Shafi'iyyah da Hanabila Sun kafa Hujja da Hadisin Aisha Allah yaƙara mata yarda wanda yazo a cikin Muslim (1154) da hadisin Abu juhaifa wanda Bukhari ya ruwaito (1968) da Hadisin Abu sa'idul khudry Wanda Dharul ƙudny yaruwaito (24) Alhafiz ibnu hajar ya kyautatashi a cikin fat-hul baary (4/210).

Wanda dukkansu suna Nuna Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yawayi gari yana azumin nafila, amma daya Samu Abunci sai ya karya azumin.

Haka Sahabi Abuldar-da'a yawayi gari yana azumin nafila sai Ɗan'uwansa salman Ya haɗa masa Abunci yaci, yakarya azumin kamar yanda yazo a cikin hadisin Abu juhaifa.

Wasu Malaman sukace: Wajibine kai Azumin nafila, idan kuma mutum yakarya wajibine ya ramashi, wannan shi ne yazo amazhabar Abu hanifa sunkafa hujja da: Hadisin Aisha Allah yaƙara mata yarda wanda Abu dauda ya ruwaito (2457) da Turmuzy (735), sai dai hadisine mai rauni Nawawi ya raunatashi a cikin Al-Maj-Mu'u (6/396) da Ibnul Ƙayyeem a cikin zhadul Ma'adi (2/84) da Albani.

Wanda ya nuna Aisha da Hafsa sun wayi gari Suna azumin nafila sai aka kawo musu abunci da sukayi sha'awarsa sai suka karya azumin, da Suka baiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam labari sai ya ce: Su rama wani amadadinsa.

Sai dai hadisine Mai rauni bai ingantaba.

Maganar farko ita ce mai ƙarfin dalili hadisan da suka kafa hujja dasu sun inganta..

Babu laifi idan kadauki azumin Sittu shawwal saika karyashi bazaka ramashi ba, domin mai azumin nafila shi ne sarkin kansa.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments