𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahamatullah, malam dan Allah ana bin mutum azumi sai ta fara rama wanda ake bin sa dagaba ya Sai ta dau sittu Shwwal ba ta gama ba sai al'ada ta zo mata har watan Shawwal ya kare ba ta gama ba, Malam to mutum zai iya rage wanda ya rama guda biyu ya cikashe sittu Shwwal dagaba ya sai ya rama biyun a matsayin na ramuwa? Allah ya ba da ikon amsawa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu Wa Rahmatullah, ‘yar uwa bai inganta mutum ya canja ninyar azumin nafila ta
koma matsayin azumin ramako na Ramaḍāna da ake bin sa ba, haka nan ko ya ce
zai canja ninyar azumin farillah ta koma ta nafila, duka wannan bai inganta ba,
saboda ba makawa azumin ramako sai an kwana da ninya da daddare, domin azumin
ramako yana ɗaukar
hukuncin azumin Ramaḍānan da ake yi ne, saboda hadisin Annabi ﷺ da Ibn Umar ya ruwaito
cewa:
"Duk
wanda bai ɗauki ninyar
azumi kafin ketowar Alfijir ba, to ba shi da azumi". Abu Dáwud (2454), Tirmizhiy
(730), Ibn Majah (1700).
Wannan hadisin
wasu malaman Musulunci sun bayyana cewa ana nufin azumin farillah da na kaffara
da kuma na bakance ake nufi, wato ban da azumin taɗawwu'i kenan, domin shi ko ba a kwana da
ninyarsa ba za a iya ɗaukarsa
bayan wayewar gari matuƙar mutum bai riga ya ci abinci ba.
Imamun Nawawiy
ya ce:
"Azumin
Ramadana ba ya inganta da ɗaukar
ninya da rana, haka nan na ramako, da na kaffara, da na fansa a aikin Hajji, da
sauran duk azumin da suke wajibai ne, babu saɓani
a wannan".
Dubi Almajmu'u
(6/286).
Imamus Siyuɗiy cewa ya yi:
"Lallai
canja ninya bayan kammala ibada ba ya tasiri a kan wannan ibada".
Dubi Al'ashbaáhu
Wan Nazwaá'ir shafi na (38).
Bisa dalilan
da ke sama sai ya zama kenan, canja ninya ko ɗauƙar
azumin farillah a mayar da shi matsayin sittu Shauwal hakan bai inganta ba,
haka nan mutum ya mayar da sittu Shauwal ko wani azumin nafila a matsayin na
ramakon Ramadana, duk hakan bai inganta ba tun da canja niyya ba ya aiki a kan
ibada bayan an kammala ibadar.
MATSAYIN SITTU
SHAUWAL ƊIN
DA BA A KAMMALA SHI BA
Duk wanda ya
fara yin azumin sittu Shauwal bai sami damar kammalawa ba sai rashin lafiya ko
wani uzuri ya same shi har watan ya fita, malamai sun ce zai sami ladar waɗanda ya azumta, wasu
malaman kuma suka ce zai sami ladar duka azumi shidan matuƙar
uzuri ne mai ƙarfi ya hana shi kammalawa.
Amma kuma wasu
malaman suna da fahimtar cewa zai iya ƙarisa cikon sauran da rashin lafiya ko
uzuri ya hana shi cikasawa ko da a watan Zhulƙi'ida ne, sai dai ladarsa ba zai yi dai-dai
da yin ta a Shauwal ba.
Ibn Hajar
Alhaitamiy ya ce:
"Wanda ya
azumci sittu Shuwal tare da Ramaḍāna a kowace shekara, to za su zamo
tamkar azumin shekara ɗaya
na farillah ne ba tare da ninkawa ba, wanda kuma ya azumnci kwanaki shida ba na
Shauwal ba, to za ta zamo tamkar sauran azuminsa na nafila ne ba tare da
ninkawa ba.
Tuhfatul
Muhtaj (3/456).
Wasu malaman
kuma suka ce ko mutum ya yi azumi shida da nufin sittu Shauwal matuƙar ba
a Shauwal ba ne ba zai sami falalar da ake samu na sittu Shauwal ba saboda zahirin
yadda nassoshi suka nuna.
Ibn Baáz shi
ko cewa ya yi:
"Ba a
shar'anta rama azumin sittu Shauwal ba bayan ficewar watan, saboda ita Sunnah
ce da mahallinta ya shuɗe,
dai-dai ne saboda uzuri ne ba a yi ba ko ba da uzuri ba".
Majmu'u
Fataáwa na Ibn Baáz (15/389).
Da kuma aka
tambayi Allama Ibn Baáz ɗin
game da wata mata da ta yi azumin sittu Shauwal guda huɗu, amma saboda uzuri ba ta sami cikaso biyun
ba sai Allama ya ce:
"Azumin
kwanaki shida na Shauwal ibada ce mustahabbiya ba wajiba ba ce, kina da ladar
abin da kika azumta, kuma ana maki fatan samun ladar sittu Shauwal ɗin baki ɗaya idan ya kasance abin da
ya hana ki cikasa azumin uzuri ne na Shari'a, saboda faɗin Annabi ﷺ
cewa:
"Idan
bawa ya yi rashin lafiya ko ya yi tafiya, Allah zai rubuta masa abin da ya
kasance yake aikatawa a lokacin zaman gida, kuma yake lafiyayye. Bukhariy
(2996). Don haka babu ramuwa a kanki na azumin (Shauwal) da ba ki yi ba.
Dubi Majmu'u
Fataáwa Ibn Baáz (15/395).
Bisa shawara
abin da ya fi zama daidai ga wanda ya fara azumin Sittu Shauwal bai sami ikon
kammalawa ba har watan ya ƙare saboda wani uzuri shi ne; ya bar abin da bai azumta ɗin ba, ba sai ya rama ba,
ana fatan Allah zai cikasa masa sauran sakamakon, saboda Sittu Shauwal ba
wajibi ba ne, mustahabbi ne, balle mutum ya ce dole sai ya rama.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.