𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum. Don Allah ina da tambaya. ko mutun zai iya fara azumin sitta shauwal
kwana ɗaya bayan
sallah?
Nagode Allah ya saka da Alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaykumussalam.
Jamhurun malamai daga mazhabobi uku wato Hanafiyya, Shafi'iyya da Hanabala duk sun
ce anso mutun ya gaggauta yin sitta Shawwal, domin hadisin da manzon Allah yce:
Duk wanda ya azumci ramadan sannan yabi bayan sa da azumi shida daga (watan)
shawwal...
Sai suka ce
anan an kwadaitar da abi bayan ramadan da yin azumin shawwal wato alal akalli a
samu kwana ɗaya ko
biyu tsakani...
Amma mazhab na
Malikiyya sun ce makaruhi ne azumtar sitta shawwal 'mubasharatan' wato kai
tsaye bayan ramadan don gudun kada a kirga waɗannan
kwanakin a matsayin ramadan....
Babu laifi dai
idan an samu kwana ɗaya
a tsakani, amma inso samu ne a samu tazara sama da kwana ɗaya.
WALLAHU
A'ALAM.
Malam
Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.