Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Auren Kashe Wuta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam dafatan an tashi lafiya, malam mene ne hukuncin mutumin da ya saki matarsa saki uku dagaba ya shi da ita suka je suka nemi wani da yarjejeniyar auren sati 1, kuma shi tsohon mijin shi ya biya sadakin, bayan satin sai tsohon mijinta ya mayar da ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, Idan mutum ya saki matarsa saki uku, to ba ta halasta a gare shi har sai ta auri waninsa, aure na buƙata ba da nufin halastawa mijinta na farko ita ba, kuma dole sai ya zama mijin na biyu da ta aura ya yi kwanciyar aure da ita kamar yadda nassoshin Shari'a suka tabatar.

Sannan dole ne ya zama ba haɗa baki mijinta na farko da na biyu suka yi da nufin ya aure ta su yi zaman aure zuwa na wani lokaci sai ya sake ta, shi kuma mijinta na farko ya mayar da ita ba. Idan aka samu wannan sharaɗi a auren ta da miji na biyu, to kusan dukkan malamai sun ce wannan aure ɓatacce ne kuma haramun ne. Irin wannan aure shi ne malamai suke ce masa auren halastawa miji na farko, wato (Nikáhut Tahleel), irin wannan aure ɓatacce ne kuma haramtacce ne bisa fahimtar mafi yawan malamai.

Kuma irin wannan aure malamai sun ce ba ya halasta wa miji na farko matar, haka shi ma miji na biyun ba ta zama halas a gare shi ba ko da kuwa bayan an ƙulla auren ne, dukkan su biyun ba ta halasta ga ko ɗayansu ba, saboda aure ne ɓatacce kuma haramtacce. Har Manzon Allah ﷺ ma ya tsine wa mai yin auren halasta ma wani, da kuma wanda aka halasta mawa ɗin, wato miji na farko da na biyun, kamar yadda Abu Dáwud ya ruwaito a hadisi mai lamba: (2076).

Saboda haka ‘yar uwa ya zama lazimi a kan wannan mata da wannan miji su rabu, saboda su ba ma'aurata ba ne a Shar'ance, aurensu ɓatacce ne kuma haramtacce, su yi nadama da tuba zuwa ga Allah saboda yin wannan babban laifi.

Amma in da a ce ita matar da aka saka saki uku, ita ce ta nemi wani ya aure ta da nufin in ta yi auren ta kashe don ta koma wurin mijinta na farko, ba tare da sanin miji na farko ba, ba kuma tare da sanin miji na biyu ba, to wannan ko da ta yi sanadin mutuwar auren don ta koma wurin mijinta na farko babu laifi, matuƙar wannan mijin na biyu da ta aura ya yi kwanciyar aure da ita. Saboda a nan miji na farko ba shi ya nemi a halasta masa ba, shi ma miji na biyun bai yi hakan da nufin halasta wa mijin farkon can ba.

Duba Almugniy (7/180, 181) domin ƙarin bayani.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments