Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Sake Ni Bayan Na Haihu, Shin Zan Yi Idda?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, idan mace mijinta ya sake ta lokacin da ta haihu ta dawo gida wanka za ta yi idda ne ko babu idda?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, duk matar da mijinta ya sake ta bayan ta haihu za ta yi idda na wata uku, kuma ba za ta lissafa jinin haihuwa cikin iddarta ba, za ta bari ne idan jinin haihuwar ya ƙare, sai ta fara ƙirgen iddarta da jinin hailar da ta fara yi bayan na haihuwar can, da zarar ta yi jini uku shi kenan iddarta ta ƙare. Amma in da a ce kafin ta haihu ne ya sake ta, to shi ne da zarar ta haihu iddarta ta ƙare kenan, saboda duk mai cikin da aka sake ta kafin ta haihu, to da zarar ta haife wannan ciki, ba wata idda da za ta yi, haihuwar ita ce ƙarshen iddarta, kamar yadda bayanin ya zo a suratuɗ 'Dalaƙ, aya ta: 4.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments