Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yaya Zan Tattali Mijina?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, tambayata a nan ita ce malam a yi min karin bayani a kan yadda ake tattalin miji?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, ‘yar uwa mace za ta iya tattalin mijinta cikin sauƙi idan ta cire girman kai da ganin isa, sannan kuma ta sa haƙuri tare da yawaita addu'a. Sai dai kamar yadda maza suke da haƙƙi a kan matansu, to haka su ma matan suna da haƙƙi a kan mazajensu, kamar yadda aya ta 227 ta cikin suratul Baƙara ta bayyana.

Sai dai a nan za a dubi yadda mace za ta yi tattalin mijinta ne kamar yadda mai tambaya ta nema. Daga cikin dabarun da mace za ta bi don ta tattali mijinta sun haɗa da:

1. Nuna masa soyayya a zahiri da ɓoye, da bin umurnin da duk ya yi mata wanda bai saɓa wa shari'a ba, da yin haƙuri da talaucinsa idan ya kasance talaka ne, da riƙe masa sirrinsa musamman a kan wani aibi da yake da shi, da yin shiru a lokacin da ya fusata har sai ya sauko, da yi masa magana cikin tausasawa da rarrashi.

2. Yi wa miji kwalliya, da yawan yin tsafta ba tare da zama da ƙazanta ba, da yi wa miji murmushi da sakin fuska, da yin tarayya da shi a lokacin da yake cikin farin ciki ko baƙin ciki, da amsa masa kira a duk lokacin da ya kiraki, da rashin aikata abin da zai fusata shi.

3. Ki guje wa rashin godiya a kan abun da yake maki na kyautatawa komai ƙanƙantarsa, da gujewa yawan kai masa ƙara ko na wane ne, da gujewa kai shi ƙara a wajen iyayenki har sai in abin ya zama dole sai an yi hakan, kada ki riƙa yi masa alfahari da tinƙaho da kyawonki ko dukiyarki idan kin zama kin fi shi kuɗi.

4. Ki riƙa ganin girman mijinki, saboda miji yana da haƙƙi mai girma a kan matarsa, saboda girman haƙƙin miji a kan matarsa, Annabi ﷺ ya ce: "Matar mutum ba ta taɓa cutar da shi a nan duniya, face sai matarsa daga cikin matan Aljannah ta ce: "Ki daina cutar da shi, Allah ya tsine maki, shi fa baƙo ne a wurinki, ya kusa ya rabu da ke zuwa wurinmu"". Ibn Majah 1857.

5. Ki riƙa neman yardar mijinki, ki taimaka masa wajen neman halal, kada ki zama marowaciya ga ‘yan uwan miji, da sauran mutanen gida, ki zamo mai taimaka masa wajen yi wa Allah ɗa'a a duk abin da ya umurce shi da abin da Allah ya hane shi, kada ki riƙa tuna masa kirkin mijinki na farko idan ke bazawara ce a wurinsa, kada ki fita gida sai da izininsa, kada ki tambaye shi zuwa unguwa ki haɗa da zuwa inda ba ki tambaye shi ba, kuma ki daina yawan fita unguwa in bai zama dole ba.

6. Kada wani ya shigo gidan mijinki sai da izininsa, ki yi ƙoƙari wajen neman ilimi da aiki da shi, ki riƙa damuwa da kula da mijinki da ‘ya’yansa har wanda ba ke kika haifa ba, kada ki riƙa bijiro da saɓani a gaban yara. Ina kashedinki da yawan tsaftace gidanki.

7. Ki riƙa girmama iyayen mijinki, musamman mahaifiyarsa ko da tana cutar da ke, da sauran ‘yan uwnsa da abokanninsa, da sauran duk masu alaƙa da shi. Da kuma kawar da kai ga saɓanin da bai taka kara ya karya ba. Ki guje wa duk ƙawar da take ba ki shawarar ɗaukar fansa a kan saɓa maki da aka yi.

8. Ki riƙa amsa kiransa a duk lokacin da ya buƙace ki zuwa shimfiɗa, ki guji yaɗa labarin yadda kuke jima'i ga ƙawayenki. Ki guji kaɗaita da namijin da ba muharraminki ba.

 Waɗannan kaɗan ne daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata mace ta kiyaye su don ta tattali mijinta, kuma in Allah ya so duk matar da ta kiyaye waɗannan abubuwa za ta zauna lafiya da mijinta.

Domin neman ƙarin bayani sai a duba littafin Muhammad Siddeeƙ Alminsháwiy mai suna: FANNUT TA'ÁMULI BAINAZ ZAUJAIN shafi na 59 zuwa na 125.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments