Ticker

6/recent/ticker-posts

Jarumar Mata - Ta Hafiz Koza

Sha'iri Hafiz Koza ya rubuta wannan waƙa ranar 03/06/2014.


Hafiz Koza

Ko da ba ta san ina yi ba,
Sai na yabi Gimbiyar Mata!

Ta sassarƙe tunani na,
Begenta kaɗai ya zam mafita.

Ke ce ni, ni kwa ni ne ke,
Jininmu guda cikin hanta.

In har zan kalli fuskarki,
Ni tawa nake gani kwata.

Kai mai son rarrabewar mu,
Zo nan in ba ka 'yar bita.

Tamkar gishirin cikin teku,
Muke ni da Sarauniyar Mata!

Ko dai sukarin da ke a ruwa,
Mun narke tsaf da ni da ita.

Ko numfashi ga rayayye,
Ƙauna ce ɗai ta zuzuta.

Mai kyan fuska da annuri,
Gaishe ki Sarauniyar Mata.

Ga murya sai ka ce Kanari,
Tsuntsun nan walla mai gata.

Mai kyawu ba misaltawa,
Kallonki ya sa na ɗimauta.

Mai kyan nasaba da kyan siffa,
Ƙaunarki nake fa 'yan mata!

Ki ji ƙai na mai dubun hairi,
A gare ki nake biɗar gata.

Na yo nisa na kiwo can,
A cikin gona ta begenta.

Zuciyata na ta ninƙaya,
A cikin kogi na ƙaunarta.

Wayyo! Ni rayuwar wannan,
In ba ke ya nake yin ta!

A misali dai kamar riga,
Kuma babu wuyan da zan sa ta.

Ko mota ba ruwan fetur,
Wa zai hau don ya tuƙa ta.

Tamkar saƙar da babu zare,
Sususu ɗai yake sa ta!

Ko alƙalamin da ba inki,
Wai to me za shi kukkurta?!

Kash! Wai duk ma abin da nake,
Ku matso ku ji tawa ni wauta!

Na san ba ta san ina yi ba,
Ya ya zan yo; ina mafita?!

Ga dai raina yana tihu,
Da bulayi har da ragaita.

Dangi ku taya ni roƙonta,
Ta amince sad da naf furta!

Ki ji ƙai na Gimbiyar Mata,
In na furta ki sassauta!

Ina Mafita?!

Post a Comment

0 Comments