Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsattsafin Haliya: Wani Digo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Citation: Sani, A-U. & Suleiman, M. (2022). Tsattsafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA). In South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, Vol. 4, Issue 2, Pp 77-77. ISSN 2664-8067 (Print) & ISSN 2706-5782 (Online). DOI:  www.doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.005.

Haliyya

Tsattsafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Abu-Ubaida Sani1
Musa Suleiman2

1Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Nigeria
2Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria

Tsakure

Manufar wannan bincike ita ce zaƙulowa tare da faɗaɗa nazari a kan salon tsattsafi a cikin waƙa. Binciken ya mayar da hankali kan salon tsattsafin haliya. An ɗora nazarin bisa ra’ayin Yahya na “Salon Tsattsafi.” An keɓance nazarin kan zaɓaɓɓun waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) guda bakwai (7) waɗanda suke mazaunin samfurin binciken. An ɗauki waɗannan waƙoƙi a matsayin tushen bayani na farko. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi, shi ne rubuce-rubucen masana da suka gabaci wannan. Binciken ya tabbatar da cewa, lallai mawaƙi na tsattsafin haliya ko haliyoyi a cikin waƙa. Haka kuma, yana iya tsattsafin haliya guda a cikin waƙoƙi daban-daban da ya shirya yayin da yake cikin yanayi iri guda. A bisa haka, binciken na ganin za a iya amfani da wannan salon nazari a matsayin matakin bincike kan halaye da ɗabi’u.

Fitilun Kalmomin: Tsattsafi, Haliya, Waƙa, Salo

Gabatarwa

 Salo a fagen adabi ba al’amari ne da ya shafi waƙa kawai ba. Wani makeken kandami ne wanda da wuya a iya kai ga ƙarshensa. A fage na nazarin salo kullum ido na kaiwa ga wasu sababbin salailai da ba a nazarce su ba a baya (Yahya, 2013). Salon tsattsafi ya fito ne daga nazarin Yahya (2013).[1] Aikin nasa ne ya zama tubalin gina wannan bincike.

Takardar ta mayar da hankali wajen faɗaɗa nazari kan salon tsattafin haliya a cikin wasu waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa). Ta haka ne za a iya kallon matakan da ya bi domin barbaɗa haliyoyin zuciyarsa a cikin wasu waƙoƙinsa. Kai tsaye, binciken ya mayar da hankali kan muhimman abubuwa da suka haɗa da:

a. fito da yadda Aminu ALA ya yi tsattsafin haliya a cikin wasu waƙoƙinsa,

b. gano nau’ikan tsattsafin haliya da ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa,

Dabarun Gudanar Da Bincike

Wannan takarda ta tattara bayanan da aka nazarta kai tsaye daga tushen farko (primary source). Wannan tushe ya kasance zaɓaɓɓun waƙoƙin ALA da ke cikin samfurin binciken. An saurari waƙoƙin sannan aka rubuta su kamar yadda aka ji mawaƙin na rerawa. A ɓangare guda kuwa, bayanan da aka samu daga rubuce-rubucen masana sun yi ƙarin haske da jagoranci ga wannan bincike.

An ɗora wannan bincike kan ra’ayin Yahya, (2013) na Salon Tsattsafi. A bisa wannan fahimta, a cikin waƙoƙin ALA ana iya samun tsattsafin tunani da ra’ayoyinsa, ciki har da na haliya. Idan kuwa haka ne, za a iya tsintar ɗangwaye a cikin baituka da ba sa jere da juna waɗanda ke ɗauke da tsattsafin haliyar da ake magana kanta. Tattara tsattsafin haliyar mawaƙi wuri guda na iya samar da madubin da za a iya kallon hoton zuciyarsa, ra’ayoyinsa, halayensa da ɗabi’unsa, da ma al’adarsa a kammale.

Malam Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa) ya yi waƙoƙi da dama waɗanda suka shafi fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.  Wannan bincike ya taƙaita ga bakwai (7) daga cikin waƙoƙin a matsayin samfarun binciken. Kadadar binciken ta taƙaita kan wannan samfuri. Waƙoƙin da ke cikin samfurin binciken su ne:

i.          Waƙar Zuciya

ii.         Waƙar Ɗan Birni

iii.        Waƙar Wayyo Kaico

iv.        Waƙar Garin Gumel

v.         Waƙar Marainiya

vi.        Waƙar Komai Ya Yi Kyau

vii.       Waƙar Miftahul-Futahati

Waiwayen Tarihin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa)

Tarihin ALA ba ɓoyayye ba ne a ƙasar Hausa. Wannan ya samo asali daga ficen da ya yi bayan watsuwar waƙoƙinsa da suka karaɗe ƙasar Hausa. Akwai rubuce-rubuce da dama da aka gudanar a matakan ilimi daban-daban game da shi da kuma waƙoƙinsa. Daga cikinsu akwai Faragai, (2008) da Imran, (2008) da Malami, (2010) da Hamza, (2011)A da Hamza, (2011)B da Lawan, (2011) da Umar, (2011) da Mohammed, (2014) da Lawal, (2015) da Ahmad, (2017) da Sulaiman, (2017) da Yakasai & Sani, (2021). A bisa wannan, kawo tarihinsa tiryan-tiryan zai zama maimaici ne kawai kan abin da aka riga aka kundace a rubuce-rubuce da suka gabaci wannan. Sakamakon haka, wannan takarda za ta mayar da hankali kan kawo waɗansu muhimman al’amura da suka shafi rayuwarsa kawai.

Malam Aminu Ladan Abubakar da kansa ya yi tsokaci game da haihuwarsa a inda yake cewa:

 Shekararrun haihuwata,

            Ƙirgar shari’ar Nabina.

 

Hijira ta alif dubu ɗai,

Da ɗari uku da ɗugunna.

 

Ma’anar manufar ɗugunna,

Casa’in da uku nufina.

 

A Municipal Kanawa,

Yakasai ta garina.

 

Nan ne aka haihuwata,

            Labarin assalina.

 (ALA: Waƙar Shahara Ta 1, 19-23)[2]

Dangane da karatunsa na boko da na Islamiya kuwa, yana cewa:

Nai ilmin Islama,

            Matayassara gwargwadona.

 

 Nai ilmi zamanina,

            Boko dan zamanina.

 

 Gwargwado dai diploma,

            Nai domin kare kaina.

 

 Nai kan Art and design,

            Ƙirƙirar zane fununa.

 (ALA: Waƙar Shahara Ta Ɗaya, 24- 27)

Wani babban tagomashi da ALA ya samu a rayuwarsa shi ne sarautun gargajiya daban-daban. Wannan ya ƙara masa fice tare da ɗaukaka sama da mawaƙan Hausa da dama. Sarautun da yake riƙe da su sun haɗa da:

a.         Sarkin Waƙar Dutse (Sahibul-Hikima), a masarautar Dutse da ke jahar Jigawa

b.         Ɗan Amanar Bichi, a masarautar Bichi da ke jahar Kano

c.          Dujimin Ƙaraye, a masarautar Ƙaraye da ke jahar Kano

d.         Ɗanburan Gobir, a masarautar Gobir/Sabon birni da ke jahar Sakkwato

e.         Sarkin Ɗiyan Gobir, a masarautar Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar

f.          Fasihin Hausawan Duniya[3]

Salon Tsattsafi

Kamar yadda Yahya, (2013) ya bayyana, salon tsattsafi salo ne da ke nufin kawo ƙunshiyar tunani ko cusa wata haliya a wurare daban-daban cikin waƙa. Ya kuma shafi amfani da wani salo akai-akai (wato a yayyafa ko barbaɗa shi) cikin waƙa ko kuma mafi yawan waƙoƙin marubuci idan gaba ɗayansu ne ake nazari. Tsattsafi a waƙa haka yake kamar ƙyallin taurari cikin sararin samaniya ko ɗiyan rana (kawalwalniya) cikin yashi ko kuma ƙyallin kwalli wanda ya barbaɗa a kan daɓe.

A bisa wannan, za a yi cewa salon tsattsafi salo ne da mawaƙi ko marubuci ke yin yayyafi ko barbaɗen haliyoyin zuciyarsa ko harshensa ko al'adunsa a cikin waƙa ko rubutunsa. Ta la’akari da wannan ma’anarza a fahimci cewa salon tsattsafi yana da rassa da dama waɗanda suka haɗa da:

a. tsattsafin haliya,

b. tsattsafin harshe,

c. tsattsafin al’ada, da dai sauransu (Yahya, 2013).

Haka kuma, ana iya karkasa waɗannan salailai da aka lissafo a sama zuwa ƙananan rukunoni. A taƙaice za su iya kasancewa kamar haka:

 A. Tsattsafin Haliya: A nan ana iya samun (i) tsattsafin raha da (ii) tsattsafin ɓacin rai da (iii) tsattsafin fushi da (iv) tsattsafin murna da (v) tsattsafin bege da (vi) tsattsafin tausayi, da makamantansu.

B. Tsattsafin Harshe: A nan ana iya samun (i) tsattsafin Ingilishi da (ii) tsattsafin Fillanci da (iii) tsattsafin Larabci da (iv) tsattsafin Kanuri da (v) tsattsafi Yarbanci da (vi) tsattsafin Inyamiranci, da sauran makamantan harsuna.

C. Tsattsafin Al’ada: A ƙarƙashin wannan rukuni, ana iya samun ƙananan rukunoni da suka haɗa da (i) tsattsafi fada da (ii) tsattsafin noma da (iii) tsattsafin dambe da (iv) tsattsafin wasanni da (v) tsattsafin sutura da (vi) tsattsafin abinci da (vii) tsattsafin biki, da sauransu.

Tsattsafi Haliya a Cikin Waƙoƙin ALA

Yanayin da zuciya take ciki, ko kamar yadda Hausawa kan ce: “Labarin zuciya...” shi ne ake kira haliya. Haliyoyin zuciya kuwa suna da yawa. Daga ciki akwai fara’a, ɓacin rai, fushi, baƙin ciki, murna, nadama, da-na-sani, bege, ƙauna, ƙiyayya, da dai sauransu. A bisa haka, idan aka ce salon tsattsafin haliya ana nufin barbaɗɗaya ko fiye daga cikin waɗannan haliyoyi cikin waƙa. A misali, ana iya samun ‘salon tsattsafin raha’ ko ‘salon tsattsafin bege’ ko ‘salon tsattsafin soyayya’ ko wani makamancin wannan.

A mafi yawan lokuta, salon tsattsafin haliya ya dogara ne kan alaƙar zuciya da kalmomin waƙa. Zuciyar mawaƙi ko ta manazarci ita ce za ta ji ko ta ɗanɗani ko ta gani tare da jinjina kalma ko kalmomi masu ƙunshiyar haliya. A wani lokaci kuma mawaƙi kan yi amfani da salailai domin ya cusa haliyar cikin waƙoƙinsa. Misali, yana iya amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana domin yin hakan. Bisa ga haka, za a iya cewa salon tsattsafi salo ne da waƙa kan bayyana wani abu da yake cikin zuciyarsu, wanda yakan iya kasancewa farin cikin ne ko ɓacin rai ko murna ko wanin hakan.

Idan aka kalli waƙar zuciya ta Aminu Ladan Abubakar, za a tarar inda ya bayyana haliyar zuciya a cikin baiti na (1) zuwa na (3). A cikin waɗannan baituka, ya bayyana haliyoyin da zuciyarsa take ƙullawa. Yana cewa:

1. In na shirya zan je Brigade sai ta mai da ni Tarauni,

            In na durƙusa nai zaune yanzu ka ga ta tada ni.

 

2. In na yunƙura na miƙe take ka ga ta zaune ni,

            Nai gabas ana madalla baya za ta zo maida ni.

 

3. Na yunƙura hannun dama sai dawayar ni hauni,

            Bari zuciya bar ja na kar ki mai da ni majanuni.

 (Aminu Ala: Waƙar Zuciya, 1-3)

Idan aka kalli waɗannan baituka za a ga cewa ALA ya bayyana irin haliyoyin da zuciyarsa ke ƙulla masa, wanda idan ya yi niyyar shuka abin alkhairi sai ta so ta cusa masa akasin haka.

 Tsattsafin Raha

Salo ne da mawaƙi ke nuna farin cikinsa da nishaɗi a cikin waƙoƙinsa. A nan mawaƙi yakan bayyana haliyoyin raha ta amfani da kalmomin da ke nuna raha. Akan yi hakan ta hanyar yin tsattsafinsu a cikin baitukan waƙa. ALA ya yi amfani da wannan salo a cikin waƙarsa ta “Ɗan Birni” a baiti na 7 zuwa na 9. A ciki ya yi tsattsafin raha inda yake cewa:

 7. Ni ma da lafiya naka waƙa,

 Har nay yi ‘yar rawa nai tsalle.

 

 8. Kuma ku rausaya fa ku risa,

            In kun ga sarari kui tsalle.

 

 9. Mata a rausaya fa a risa,

            In an ga sarari ai tsalle.

 (ALA: Waƙar Ɗan Birni, 7- 9).

Idan aka dubi waɗannan baituka za a ga mawaƙin ya rubuta waƙar a lokacin da yake cikin nishaɗi da fara'a. Za a iya lura da hakan musamman idan aka mayar da hankali kan ire-iren kalmomin da ya yi amfani da su. Kalmomin sun haɗa da rawa, tsalle, rausaya, risa... dukkanninsu kalmomi ne da ke nuna raha da nishaniɗi a zuciyar mawaƙi.

Tsattsafin Ɓacin Rai

Salo ne da mawaƙi ke amfani da shi domin nuna irin haliyar da zuciyarsa ta shiga a yayin da yake cikin ɓacin rai. Wannan ne ya sa idan mawaƙi ya yi waƙa a irin wannan yanayi, ya zama dole sai ya yi tsattsafi na haliyoyin ɓacin rai a cikin baitukan waƙarsa. ALA ya nuna irin wannan haliyoyi a cikin waƙarsa ta ‘’Wayyo Kaico’’ a baiti na 6. Ya nuna ɓacin ransa ta hanyar yin zambo a cikin baitin waƙar. Yake cewa:

6. Wai gyartai ka bai wa ƙirar mota,

 Mai ƙira ka ba shi saƙar mata,

 Ya zama ‘yar burum-burum ɗan wauta,

 An yi fagabniya ya mai tatata, wayyo kaico!

 (ALA: Waƙar Wayyo Kaico, 6).

A nan mawaƙin ya nuna ɓacin ransa ta hanyar yin zambo, da kuma amfani da kalmomi irinsu wayyo kaico. Ya nuna takaicinsa game da yadda aka kasa ajiye komai a hulallin da ya dace.

Ba a iya wannan waƙar kaɗai ya nuna haliyar ɓacin rai ba. Idan aka dubi waƙar “Garin Gumel” a baiti na 13, za a ga yadda ya nuna mutuƙar ɓacin ransa. Yana cewa:

13. Bana an yi gumi nai sharkaf ya jiƙa ni,

 Na taho nai murna gun sarkinmu sani,

 Mahara mafasa ƙwauri kawai suka hana ni,

 Sai na dawo gida ɓacin rai ya ƙume ni.

 (ALA: Waƙar Garin Gumel, 13).

A nan ma an ga yadda ya nuna cewa ya taho domin ya yi murna ga sarki amma mahara mafasa ƙwauri (‘yan daba) suka hana shi. Haka ya dawo gida cikiɓacin rai. Ya yi amfani da kalmomi irinsu; wayyo, kaico, ɓacin rai, da ƙumewa domin nuna haliyarsa.

 Tsattsafin Tausayi

Salo ne da mawaƙi ke amfani da shi domin ya nuna haliyar tausayi, wanda zuciyarsa ta tsinci kanta a ciki. Irin wannan haliyoyi su ne makaman da za su nuna wa mai sauraro ko mai nazari irin tausayawar da mawaƙi ya yi da kuma yanayin da zuciyarsa ta shiga ciki. ALA ya yi amfani da irin wannan salon a cikin waƙarsa ta “Marainiya. A cikin waƙar yana cewa:

 Abin ban tausai gidan marayun yara,

 Abin ai kaico hawaye sui ta darara,

 Abin su marayu dagwai-dagwai ‘yan yara,

 Wasu haɗarin mota a kai suka zam maraya,

 Wasu ko tsinto ake a cikin shara,

 Wasu masu taɓin hankali ka haifa yara,

 Sababi na haɗakarsu ba shi ƙirgo yara,

 Wasu ‘yan jarira a kan gadonsu na yara,

 Wasu na tatata da rarrafe ‘yan yara,

 Wasu na makarantar karatun ta mora,

 Wasu an kakkai su sakandare da kara,

 Ba uwa babu uba haɗin gamayyar yara,

 Gida ɗaya amma kamarsu bamban yara,

 Wani na zaluntar na ƙas da shi dan ƙwara,

 Wani jarumta wani shagwaɓa ‘yan yara,

 Wani ba ƙoshin lafiya cikin ‘yan yara,

 Wasu ko ƙoshin lafiya kamar tantabara,

 Abinci idan za a ba su tamkar fara,

 Jerin gwano suke kamar masu bara,

 Gidansu matsattse sai ka ce tantabara,

 Gidansu guda ɗaya jal ku je kui duba.

 (ALA: Waƙar Marainiya)

 Mawaƙin ya nuna tsantsar tausayinsa ga yaran da ya tarar a gidan marayu saboda irin halin da ya tsince su a cikiYa gan su yan dagwai-dagwai ba uwa ba uba. Wasu na tafiya, wasu a kan gadonsu na yara, wani na tatata, wani jarunta, wani shagwaɓa. Haka kuma, idan za a ba su abinci tamkar fara. Wannan ne ya sa bai ankara ba sai ya ga hawaye yana zubo masa saboda tsananin tausayi da ya kama shi.

Tsattsafin Fushi

A nan, mawaƙi na amfani da haliyoyin fushi ko wasu mizanai da ke iya nuna fushi a yayin gudanar da waƙa. Aminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salon a cikin waƙarsa ta “Garin Gumel” a baiti na (1) da na (2), inda yake cewa:

1. Bana na ga daren kure na ba da baya,

Sukuwa da makahon doki na ƙidaya,

A bikin sallar gani na hangi shirinya,

Bana ga abin al’ajabi ya suƙe ni.

 

2. Taro irin na gani tushensa maulidi ne,

Taro irin na gani tushensa al’ada ne,

Taro irin na gani tushensa zumunci ne,

Mahara mafasa ƙwauri kawai suka hana ni.

 (ALA: Waƙar Garin Gumel)

Idan a ka kalli waɗannan baitukan, za a ga cewa mawaƙin ya nuna fushinsa ta hanyar amfani da mizanin fushi domin ya nuna irin fusatar da ya yi. Ire-iren waɗannan kalmomi da ya yi amfani da su sun haɗa da; daren-kure, sukewa, makahon doki, hanawa, da sauransu. Ya yi hakan ba don komai ba sai saboda ya je ne garin Gumel domin ya taya sarkin Gumel murnar sallar Gani, amma ‘yan daba da mahara suka kawo farmaki suka tarwatsa taron nasa. Wannan ne abin da ya yi mutuƙar ɓata wa Aminu ALA rai har ya bayyana fusatarsa a cikin wannan waƙa.

Tsattsafin Murna

 Shi ma yana ɗaya daga cikin rassan tsattsafin haliyya, inda akan samu mawaƙɗauke da murna da farin ciki, wanda hakan ne zai sa ya gudanar da waƙarsa a cikin wannan yanayi na annashuwa. To a nan dole za a samu ya yi yayyafi ko barbaɗa tsattsafin haliya na murna da farin ciki ta hanyar amfani da wasu mizanai da za su nuna irin yanayin sakewa da yake ciki.

Aminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salo a cikin waƙarsa ta “Komai Ya Yi Kyau, wadda ya yi wa mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero. A baiti na 8 da na 10 yana cewa:

8. Lale-lale duk jama’ar Kano suna ma lale da alfahharo,

Yaran sauka ‘yan tahafizu na oyoyo ga ɗan Bayero,

Gatan kumbo ka dawo gare mu sai madalla mui ayyiraro,

Matan birni sai guɗa suke suna yin nishi suna ta asayyaro,

Tamkar baba in na rufe idona na buɗe Ado Bayero.”

Ba a iya nan ya tsaya baYa ƙara bayyana farin cikinsa a cikin baiti na goma (10) inda yake cewa:

10. Birni ƙauye sai guɗa ake ana ga Ado sak ɗan Bayero,

 Har kaikawon nan fa da kas sani ga fararen kaya jikan Bayero,

 Na tsinkaya na aza mai Kano ne ashe mai Bichi ne ɗan Bayero,

 Sai na ga ƙwalla na ta ciko ido tunani na can baya ya warwaro,

 Kan takawa marigayi mai Kano madubin mulki ba siddadaro”.

 (ALA: Waƙar Komai Ya Yi Kyau, 8-10)

 A cikin waɗannan baitukan ALA ya nuna mutuƙar murnarsa, inda ya yi amfani da kalmomi irinsu: lale-lale da ayyiraro da assayyaro. Haka kuma, ya nuna yadda mutanen birni da na ƙauye suke murna da dawowar Aminu Ado Bayero, da yadda ‘yan sauka suke murna. Wannan ne har ya sa shi tunowa da sarki Kano marigayi Ado Bayero.

Tsattsafin Bege

Bege na ɗaya daga cikin rassan tsattsafin haliya. Akan samu mawaƙi na begen abin da yake so yake kuma ƙauna. A nan mawaƙi kan yi amfani da haliyoyin ƙauna domin ya bayyana irin son abin da yake begeAminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salo a cikin waƙarsa ta “Miftahul-Futuhati ta 1. Za a ga hakan a baituka na 36 zuwa na 45. A ciki ya kira Ma’aiki (S.A.W) da “linzamin rayawata.” Hakan ya nuna mana cewa shi ne ke juya duk wasu al’amura na rayuwarsa. Da jin ire-iren waɗannan kalamai na ALA za a iya fahimtar so da ƙauna ce ta sa shi ya yi haka. Yana cewa:

 36. Na yunƙura in yi yabon masoyi,

            Annabi ne babban masoyi.

 

 37. Mai darajar da ta zarce shayi,

            Mai hali na yabo da koyi.

 

 38. Mai nasaba ciki babu shayi,

            Rabbu hane ni ni da in yi sanyi.

 

 39. Kan lamarin da na tsara zan yi,

            In yabi Annabi babu shayi.

 

 40. Babu kure ciki ba bulayi,

            Sai madarar ƙaunar masoyi.

 

 41. In faɗi tarihin masoyi,

            Kuj ji busharorin masoyi.

 

 42. Babu kasala babu sanyi,

 Ba nukusani babu shayi.

 

 43. Ku ji abin da yahudu kan yi,

            Daga busharorin masoyi.

 

 44. Duk a cikin waƙar da zan yi,

            Nutso a cikin bahari fa zan yi.

 

 45. Hujjoji na zuwan masoyi,

            Har ahlil kitabi sun yi.

 (ALA: Waƙar Miftahul-Futuhati ta 1, 32-45)

A nanmawaƙin ya nuna irin ƙauna da tsantsar soyayyar Ma'aiki da suka saka shi begensa. Ma’aunan haliyyar bege da ya yi amfani da su sun haɗa da; masoyi, zarce, babu kamar shi, ba nukusa ni, madarar ƙauna, babu kasala, da sauransu.

Sakamakon Bincike

Lallai akan samu tsattsafin haliya a cikin waƙoƙi. An ga misalan kalamai da ke mazaunin mizanan haliyar tausayi a cikin Waƙar Marainiya. An kuma ga na fushi a cikin Waƙar Garin Gumel, duk na Aminu Ladan Abubakar. A taƙaice ke nan, haliyoyi da mawaƙi ke iya tsattsafawa cikin waƙa suna da yawa. Za a iya kallon hakan cikin waƙoƙin ALA inda aka samu tsattsafin haliyoyi da suka haɗa da na fushi da bege da raha da sauransu.

A ɓangare guda kuwa, binciken ya fahimci cewa ana iya nazartar tsattsafin haliya ta fuskoki guda biyu. Fuska ta farko ita ce ganowa da ƙwanƙwance haliya ko haliyoyi daban-daban cikin waƙa guda. Ke nan wannan na nuna cewa, ana iya samun haliyoyi sama da guda a cikin waƙa ɗaya. An ga irin haka a cikin Waƙar Komai Ya Yi Kyau. A cikin waƙar, an ga yadda tsattsafin tausayi ko jimami ya keta cikin na murna. An kawo hakan cikin baiti na 10 yayin da jimamin rashin sarki ya kai ga mawaƙin zubar da ƙwalla alhali yana tsakiyar murna.

A ɗaya fuskar kuwa, ana iya nazartar tsattsafin haliya guda cikin waƙoƙi daban-daban. Ana iya ɗaukar ɗaukacin waƙoƙin mawaƙi ko waɗansu daga cikinsu domin nazartar wata haliya ko waɗansu haliyoyi. A irin wannan yanayi, za a riƙa bin waƙoƙin ɗaya bayan ɗaya domin zaƙulo wuraren da haliyar ko haliyoyin da ake nazari suka bayyana domin ƙwanƙwance su.

Naɗewa

Ko bayan kasancewar adabi wani madubin hango rayuwar al’umma, nazarin tsattsafin haliya madubi ne ko hoto da za a iya kallon mawaƙi a cikinsa kai tsaye. Salon nazari ne da ka iya taimakawa wajen gano abin da ke ƙunshe cikin zuciyar mawaƙi yayin da yake barbaɗa wannan ƙunshi cikin baitukan waƙa ko waƙoƙinsa. Har ila yau, hanya ce da ka iya taimakawa wajen gano asalin yanayin mawaƙi ta fuskar sauƙin kai ko zafin kai, jarumta ko ragwanci, soyayya ko ƙiyayya, lalama ko saurin fushi, da dai sauransu. Salo ne da ke buƙatar ƙarin nazari domin ƙwanƙancewa sala-sala ta yadda za a ci cikakkiyar gajiyar hikimomi da ke ƙunshe ciki.

 Manazarta

Adewale, E. O.(1984). An Introduction to Social Anthropology. Ibadan: Agbo Areo Publishers.

Ahmad, S. B. (2017). Tasirin Waƙa A Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar da aka gabatar a wajen taron Masoya Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a ɗakin taro na Makrantar Ado Gwaram da ke kan titin Gidan Namun Daji, Kano.

Aliyu, S. B. (1986). Alhaji Isah Mai Kukuma Mina Da Waƙoƙinsa.” Kundin digiri na farko jami’ar Sakkwato.

Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Center Limited.

Ɗangambo, A. (2007)Ɗaurayar Gadon Feɗe WaƙaKano: Amana publishers.

Faragai, N. A. (2008). Nazarin Salo Da Sarrafa Harshe A Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Gobir, Y. A. da Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Amal Printing and Publishing, Nigeria.

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i Da Tarke A Adabi Da Al’adu Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing

Gwammaja, K. D. (2018). Jagoran Nazarin Karin Magana. Kano: Kdg publishing limited.

Hamza, M. K. (2011)A. “Nazarin Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminuddeed Ladan Abubakar (ALA). Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Hamza, M. K. (2011)B. Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Imran, A. L. (2008). Jigo da Salo a Waƙoƙin Aminu ALA. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya

Lawal, M. (2015). “Yabon Sarakuna A Waƙoƙin ALA: Nazari Daga Waƙar Bakan Dabo Da Waƙar Farar Aniya Farar Atafa.” Kundin digiri na biyu da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jahar Kaduna.

Lawan, M. B. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALAn Waƙa, Littafi na Ɗaya. Kano: Iya Ruwa Publishers.

Magaji, B. (2009)Nazarin Aron Kalmomi a Waƙoƙin Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa. Kundin digiri na farkoJami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Malami, U. (2010). “Jami’a Gidan Ban Kashi: Nazarin Matsayi Da Kimar Jami’a Ga Cigaba da Bunƙasa Al’ummar Hausawa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Mohammed, Y. (2014). “Kwatanta Salon Wasu Waƙoƙin Aminu ALA Da Na Fati Nijar.” Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Muhammad, D. (1980). “Waƙa Bahaushiya” Cikin studies in Hausa Language, Literature and culture. Kano: Bayero University.

Muhammad, D. (1980)Zumunta Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Hausa da MakaɗaCikin Harsunan Nijeriya na 4. Kano: Bayero University.

Omar, S. (2013). Fasahar Mazan Jiya Nazarin A kan Rayuwa Da Waƙoƙin Malam Malam Mu’azu Hadeja. Kaduna: Garkuwa Media Service Limited.

Sulaiman, I. M. (2017). Salon Hoton Zuci: Nazari A Waƙar Ta’aziyar Yahaya Mahmud Da Ta Ado Bayero na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar da aka gabatar a wajen taron Masoya Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a ɗakin taro na Makrantar Ado Gwaram da ke kan titin Gidan Namun Daji, Kano.

Umar, R. A. (2011). “Matsayin Uwa a Bahaushiyar Al’ada: Nazarin Waƙar ‘Ummina’ ta Aminu Ladan Abubakar.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Yahya, A. B. (2004). “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Haliru Wurno”Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yahya, A.B. (1999). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yahya, A.B. (2013). “TSATTSAFI: Wani Ɗigo Cikin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa.” Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriaya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Nigeria: Amal Printing Press. ISBN: 978-978-57624-9-0.

 



[1] A duba takardarsa mai taken “TSATTSAFI: Wani Ɗigo Cikin Gulbin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa.”

[2] A baitocin da ke sama, za a ga cewa ALA ya bayyana ranar haihuwarsa da wurin da aka haife shi.

[3] An yi masa wannan naɗi ne a taron ranar Hausa ta duniya a jahar Gwambe.

Post a Comment

0 Comments